Wednesday 20 March 2024

Hanyoyi 8 Masu Sauki Na Inganta Kasuwanci

Tura Wannan Zuwa

Duk lokacin da ake maganar ƙara adadin ciniki a sana’a, abubuwa guda uku ne ya kamata ka yi la’akari da su.


1. Ƙara adadin kwastomominka.


2. Ƙara adadin cinikin da kowane kwastoma yake maka.


3. Ganin cewa kwastoma yana ƙara yawan dawowa domin yi maka ciniki.


Hanyoyin bunƙasa cinikin ku
Hoto: Pens

MarubuciBello Galadanchi


Yau za mu mayar da hankali akan na farko, wato “Ƙara adadin kwastomominka”. Zan bada shawarwari da yawa, kai kuma sai ka duba waɗanda kake gani za su dace da sana’arka ka gwada. Wannan rubutu ya shafi maza da mata. 


1. KA YI WA KWASTOMOMINKA TAMBAYOYI: Ka mayar da hankali wajen sauraron shawarwarin kwastomominka. Ka tambaye su, banda cinikin da kuke yi tare, me kuma za ka iya kawo musu? Wani irin biyan buƙata suke so? Manyansu waɗanda ke ƙaunarka za su gaya maka tsakaninsu da Allah abubuwan da suke buƙata. Idan har bakin su ya zo ɗaya dangane da abu ɗaya, to ka tabbatar ka samar da wannan abu yadda suke so. Hakan ne zai dawo da su, kuma ya jawo maka hankalin sababbin kwastomomi. 


2. KOWACE WATA, KA YANKE SHAWARAR NAWA KAKE SO KA SAMU: Duk abin da ba shi da alƙibla, to babu ci-gaba. Idan ka yanke shawarar nawa kake so ka samu a wata, to sai ka raba waɗannan kuɗaɗen zuwa makonni huɗu. Hakan zai nuna maka irin aikin da ya kamata ka yi. Idan har ka cimma, kuma ka samu ci-gaba, to za ka iya ƙara adadin cinikin da kake da burin yi. 


3. KA SALLAMI MA’AIKACIN DA YA FI RASHIN TAƁUKA ABUN ARZIKI: Babu shakka!!! Wato kwastomomi suna da matukar daraja. Idan har kana da ma’aikacin da ake yawan kawo ƙararshi, ko aikinshi ba ya gamsarwa, ko yake da taurin kai wajen koyon sababbin abubuwa, to ka sallame shi gobe-goben nan. Tabbatarwa babu wake ɗaya da ke ƙoƙarin ɓata maka gari na da matukar muhimmanci a kasuwanci, saboda mutum ɗaya zai iya sakawa kwastomomi su guji sana’arka. Ka tabbatar ka san kowane ne, kuma ka tunkuɗa ƙeyarshi. 


4. KA LAƘANCI BAYYANA SANA’ARKA CIKIN KALMOMI ƘALILAN: Za ka haɗu da mutane da yawa, kuma ba za ka san wanda zai yi maka babban ciniki ba, ko ma ya yi sanadin samun dukiya mai yawa. Idan yau wani ya fito ya tambaye ka ya ce “Mece ce sana’arka?” To wannan babbar dama ce ta yin amfani da furuci wajen jawo hankalin jama’a. KAR KA YARDA KA CE “Ɗinki muke yi, ɗinkin mata da yara”. Ire-iren waɗannan bayanan sun yi kwantai. Ga samfurin amsa “Muna farantawa mata da yara rai, ta hanyar ɗinka musu kaya a cikin hanzari da rahusa”. To duk wanda ka gayawa wannan, zai yi murmushi ya fara yi maka tambayoyi kamar “hanzari kuma? Kamar kwanaki nawa? Nawa ne kuɗin ɗinkinku?” Idan har ka yi haka, to ka tabbatar ka karɓi lambar waya da WhatsApp kuna gaisawa. Ko ba su da ɗinki, za su nunawa ‘yan uwansu da jama’a kasuwancinka. 


5. KA RIƘE ZUMUNCI: Ka tabbatar kana da littafin da kake rubuta lambobi da duk wasu bayanai na kwastomominka. Kar ka dogara akan wayar hannu, za ta iya faɗuwa ko ta samu matsala. Ka tabbatar ka rubuta da biro a cikin littafi. Ka nemi sanin abubuwan dake da muhimmanci a rayuwar kwastomominka. Ka rubuta, kar ka mance. Wasu ‘ya’yansu ne, to ka rubuta sunayensu. Wasu aikin su ne, wasu iyayensu ne, wani amaryarshi ce, wani motarshi ce, abubuwa iri-iri. Ka yi ƙoƙarin sanin wani abu na rayuwarsu, kai ma ka bayyana musu abin da keda muhimmanci a rayuwarka. Duk kwanaki biyu zuwa huɗu, ko mako-mako musamman Juma’a, ka buga ku gaisa. Kar ka yi maganar sana’a, idan ba su ne suka fara ba. 


6. KA BINCIKI IRE-IREN TALLACE-TALLACEN DA KISHIYOYINKA SUKE YI: Akwai waɗanda ke sana’a irin taka dake kashe maƙudan kuɗaɗe wajen tallace-tallace. Ka nazarce su domin fahimtar abin da suke yi. Wannan zai ba ka makamai wajen bambanta kanka daga saura ta yadda za ka fi jawo hankali. 


7. KA KAMA ƘAFA A WAJEN SHUWAGABBANNIN AL-UMMA: Shuwagabannin al-umma sun san jama’a sosai. Kama ƙafa a wajensu zai iya buɗe maka wata sabuwar taskar kwastomomi. 


8. KA ZAMA MAI TAIMAKO: Ka ɗauki kanka a matsayin likita, kuma ka ɗauki duk kwastomomi a matsayin marasa lafiya masu neman likita. Ka taimake su, ka yi musu murmushi, ka amsa duk tambayoyinsu. Idan ba ka san amsa ba, ka tambaya. Ka kula da komai nasu yayin da suke tare da kai. Lokacin Sallah ka yi musu tanadin buta da tabarma, lokacin cin abinci a sayo musu kaza, wajen zama ka ba su mai laushi, ɗakin otel idan daga wajen gari suke, da mota ko adai-daita sahu ya kai su gida ba. Ka zama mai kula sosai. N500 ɗin da za ka kashe domin kula da kwastoma zai iya haifar da N500,000 saboda kulawa da taimako. 

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user