Saturday 25 May 2024

Halaye 5 Masu Sauya Rayuwa Nan Take

Tura Wannan Zuwa Ga

Da bulo ɗaya-bayan-ɗaya ake kammala gini, haka zalika rayuwarka, kana buƙatar ɗabi’u daban-daban waɗanda za su ginaka, kuma su ba ka makaman da kake buƙata domin yin nasara a fagen yaƙin rayuwa.


Dabi'un Samun Sauyi A Rayuwa
Hoto: Leading Great LearningMarubuciBello Galadanchi


Zan lissafo ɗabi’un da za su agaza maka wajen ƙara arziki, basira da nasara wajen gudanar da abubuwa a rayuwarka. 


1. IBADA: Babu shakka jama’a masu yawa suna ibada kullum, amma a wannan zamani, sau da yawa ibada ya zama da baki kawai ake yi, ba ya kai wa har zuci. Ka tashi kullum kafin wayewar gari, bayan sallar Asuba, ka yi karatun Al-Qur’ani, ka yi adduo’i. Ka cire tunaninka da zuciyar ka daga hayaniyar duniya zuwa wani waje wanda daga kai sai Ubangijinka. Daga wannan ɓangare, ka yi tunanin daga inda rayuwar ka ta zo, da kuma inda za ta koma. Wannan zai ba ka nutsuwa, tunani mai zurfi, hangen nesa, hikima da kwanciyar hankali. Idan kana haka, to Allah (S.W.T) zai ba ka damar mayar da hankali akan burin ka, kuma ko wani bil-adama ya ce maka ba za ka iya ba, to ba za ka saurare shi ba. 


2. KA BAI WA KANKA MAMAKI: Idan kai matashi ne ko dattijo, ga wani abu da zai amfane ka yadda ba ka zato. Mene kake fargabar yi? Mene ne babban burinka wanda kake kunyar bayyanawa jama’a? Ɗauki tsintsiya ka share gidan ku baki ɗaya kafin kowa ya tashi. Idan lokacin sanyi ne, to ka yi wanka da ruwan sanyi.  Kai marubuci ne amma babu wanda ya sanka, buga a shafin ka na facebook, sannan ka aika wa wani edita kullum, koda ba ya amsawa. Neman aure kake yi amma ba ka samu haɗin kai ba, ka gaida iyayen ta kullum, kuma ita ma ka aika mata saƙo mai ma’ana. Mene ne yake firgita ka? To wannan abun za ka yi. Kar ka ɓoye a cikin kogon fargaba da sanyin gwiwa. Duniyar nan filin daga ne, saboda haka ka fito a yi da kai. 


3. KA MOTSA JIKI: Babu shakka. Ko ke matar aure ce, motsa jiki na da matuƙar muhimmanci ga lafiyar ki da kuma ƙwaƙwalwar ki. Idan kuwa ba ka yi, to akwai wahalar farawa. Za ka iya farawa da takawa a ƙasa na mintuna biyar zuwa goma kullum. Wata rana sai ka ƙara. Idan kana motsa jiki, to za ka rage jin gajiya da kasala, sannan cikin ka zai samu ƙarin lafiya, kuma za ka samu kwanciyar hankali da ma wasu fa’idoji masu yawa kamar ɗaukar hutu daga amfani da wayar hannu. 


4. AIKI  A TSANAKE: Wannan yana nufin cire kanka daga duk wani abu dake ɗauke maka hankali, domin mayar da hankali sosai wajen aikin da ya fi maka muhimmanci. Ya zamanto kullum ka ware wasu lokuta kamar mintuna 20 zuwa sa’o’i biyu kana aiki akan abu daya. Misali shi ne wannan rubutu da kake karantawa, kullum ina share sa’o’i biyu wajen shiryawa da rubutawa. To idan kana haka kullum, wata rana za ka yi mamakin abin da ka cimma. 


A halin yanzu wannan littafin da nake rubutawa yana da shafuka 55 da kalmomi dubu ashirin da shida da ɗari huɗu da ‘yan kai. Wannan ɗabi’a na ƙara nutsuwa da ƙwarewa wajen mayar da hankali a duk wani abu da ka saka a gaba.


5. KA BAYYANA WA JAMA’A: Babu shakka. Duk abin da kake yi, akwai wanda ya fi ka sani da ilimi. Saboda haka kana buƙatar malamai, da tsokacin jama’a, da kuma shaidar jama’a. Mutane da yawa na yin kuskure wajen ɓoye tunanin su ko shawarwarin su daga jama’a gudun kar a kwafa ko a ce ba zai yi tasiri ba. Idan har ka ɗauki shawarwarin jama’a, to wannan aiki da kake yi zai samu rayuwar shi ta kanshi, sannan zai canza daga tunanin ka.


Babu komai, duk mutanen da suka yi nasara a rayuwa sun yi shi ne ta hanyar ɗaukar shawarwarin jama’a. Allah Ya ɗaukaka mana ƙasar mu ta gado. 

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user