Monday 27 May 2024

Muhimmancin Aikawa Da Saƙonnin Soyayya Ga Masoya

Tura Wannan Zuwa Ga

Yawan tura saƙonnin soyayya zuwa ga masoyan ku cikin dare ko rana babban abu ne da zai taimaka muku wajen samun soyayyar wanda kuka nufa da hakan cikin gaggawa.


AMFANIN AIKAWA DA JUNA SAƘONNIN SOYAYYA A TSAKANIN MASOYA
Hoto: Love To Know 

MarubuciAbba Muhammad Dan Hausa


Saƙon soyayya wani sinadari ne da yake ƙarawa soyayya zaƙi da kuma armashi.


Matuƙar zai kasance ka iya turawa da masoyiyarka daɗaɗan kalaman soyayya, ka kuma iya furta mata su a lokacin da kuke tare a zahiri ko kuma ta wayar salula to hakan zai mayar da kai masoyi na musamman a wajen ta.


Akwai buƙatar ka nemo wasu keɓaɓɓun kalmomi masu daɗi da jan hankali da za ka yi amfani da su cikin kowace jumla wajen rubutawa masoyiyarka ko masoyinki saƙon soyayya.


Kamar yadda wani masani yake cewa " Kalaman da ake yin amfani da su wurin rubuta wasiƙar soyayya sun kasance kalamai ne musamman masu ɗauke da saƙonnin;


1 Soyayya.

2 Ƙauna.

3 Bege.

4 Yabo.

5 Ƙarfafa zuciya." (S.I. Fatimiyya 2008). 


Misali:


"Samuwar ki a cikin rayuwata ya samar da gagarumin canji ga ƙaruwar farin ciki na ta hanyar sauraren muryarki da kuma kasantuwata a tare da ke cikin rayuwarki mai tsari. Ke ce tauraruwar da hasken ta yake haskaka birnin zuciyata, kina ɗaya daga cikin mutanen da ba zan taɓa mantawa da su ba har abada a cikin rayuwata. ki huta lafiya."


Sannan kuma da yawan masana suna ganin "Bai dace ku saba da wani ta wajen aika saƙon soyayya ba tare da niyar aure ba. Idan soyayya ta shiga, hakan zai jawo baƙin ciki da tashin hankali."

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user