Monday 17 June 2024

Karanta Kayatacciyar Hikayar Birnin Tagulla (5)

Tura Wannan Zuwa Ga

Ya kai mai karatu, ko kasan mai yi maka wannan gargadi? Ba kowa ba ne face ni dake cikin wannan kabari. Sunana Sarki Kush ɗan Sahaddadu ɗan Adi Babba."


 HIKAYAR BIRNIN TAGULLA
Hoto: Story


Bayan wannan saƙo sai kuma aka rubuta wannan saƙon cikin baitocin waƙa:


"Za ku tuna sunana can da daɗewa, yayin shuɗewar ranaku da darare. Ni ne ɗan Shaddadu mai ƙarfin mulki, wanda mulkina ya ratsa kowace ƙasa a duniya. Na biyar da masu girman kai na lankwasa masu ƙarfin zuciya, tun daga Ƙasar Sham da Misira har zuwa Adinanu. Na mulki dukkan sarakuna na mallaki dukiyarsu, sarakuna kan razana su tsorata idan suka ji ambaton sunana. A gabana ga tarin askarawa da sadaukai, ina ji kamar na fi kowa ƙarfi a duniya. Idan na hau doki ina zagaya sadaukai, ga su nan dubu zambar dubu a kan dawakansu. Na mallaki dukiya mai yawa mara adadi, daga zinariya azurfa da har zuwa tagulla. Da a ce dukiya na amfani yayin mutuwa, da na dawwama har abada ba tare da na mace ba. Amma ƙaddarar Allah ba ta kankaruwa, na wayi gari yau ga ni kwance cikin ramin kabarina."


Yayin da Sarki Musa ya ji saƙon da ke rubuce cikin wannan Allo sai ya ɗimauce don tsoro, ya yi ta kuka yana kwararar da hawaye, saboda ganin irin yadda maza suka kwanta dama. Suka ci gaba da zagayawa cikin fadar suna ganin abubuwan mamaki, ga karagu nan na zama da 'yan ƙananan tabkunan wanka na jin daɗi. Ba su gushe ba suna zagaya cikin fadar har suka iso ga wani babban dakali da aka yi domin cin abinci, an gina dakalin da duwatsu masu daraja, an tsayar da shi bisa shishiniya huɗu na zumarrazi. A bisa dakalin an rubuta:


"Wannan dakali ne da sarakuna dubu masu ido ɗaya na dama, da wasu dubu masu ido ɗaya na hagu, da wasu dubu masu ido biyu suka ci abinci a bisa gare shi. Dukkansu sun mutu suna cikin kaburbura ababen shafewa."


Duka waɗannan abubuwan mamaki da Sarki Musa ya gani ko ya ji an karanta masa, ya riƙa rubuta su a cikin takarda. Bayan sun gama zagaya fadar nan duka sai suka fita ba tare da sun ɗauki ko allura ba a cikin fadar, sai fa 'yar takardar nan da Sarki Musa ya yi rubutu a cikin ta. Bayan sun fito daga wannan fada sai suka ci gaba da tafiya tsawon kwanaki uku, Sheik Abdussamadu na nuna musu hanya. Ba su gushe ba suna tafiya har suka iso ga wani tsauni wanda a kansa akwai mutum-mutumi na wani mahayi wanda aka yi da tagulla. A hannun mahayin akwai wani mashi mai faɗin kai, mashin na ƙyalli cikin rana har yana ɗaukar ido. A jikin kan mashin an rubuta wannan saƙo:


"Ya kai wannan mutum da ka zo wannan wuri, idan ba ka san tafarki mai saduwa da Birnin Nuhas ba, to, ka murza hannun wannan mahayi, mahayin zai juya ya fuskanci jihar Birnin Nuhas. Ka bi wannan jiha da mahayin ya fuskanta, kada ka ji tsoron komai, za ka sadu da Birnin Nuha.


Yayin da Sarki Musa ya ji abin da ke rubuce a kan mashin mahayi, sai ya matsa ya murza hannunsa, nan da nan mahayin nan ya juya kamar walƙiya, da ya gama juyawa sai ya tsaya cak, ya fuskanci jihar da da ma nan suka nufa. Suka ci gaba da tafiya bisa wata 'yar ƙaramar hanya matsattsiya. Ba su gushe ba suna tafiya kwana da kwanaki, ba dare ba rana, har suka yi tafiya mai nisan gaske. Suna cikin tafiya wata rana sai suka tarar da wani ginshiƙi na bakin dutse, an kwakware cikinsa, an mayar da shi kamar murhun wuta. A cikin wannan ginshiki an cusa wata irin halitta mai ban tsoro. Daga ƙafafu har zuwa ƙirjin wannan halitta an cusa su ne cikin dutsen. Wannan halitta tana da fika-fikai biyu, da hannuwa guda huɗu. Hannuwanta biyu irin na 'yan Adam, biyu kuma tamkar dagin zaki, da farutta zaro-zaro. Jikinta duka baƙi ne ƙirin lulluɓe da gashi irin na dawaki. Wannan halitta da muni take matuƙa. Idanunta 'yan ƙanana kamar na kyanwa, ga su jajaye kamar garwashin wuta. Haka kuma tana da ido na uku a tsakiyar goshinta wanda tartsatsin wuta ke fita daga cikinsa. Wannan halitta sai kururuwa take yi tana cewa, "Tsarki ya tabbata ga Ubangiji wanda ke azabtar da ni wannan azaba har zuwa ranar tashin ƙiyama."


Yayin da mutanen Musa suka ga wannan halitta sai suka tsorata suka firgita har wasu daga cikinsu suka juya da baya da nufin gudu. Musa ya tambayi Abdussamadu, "Ya Sheik, wannan wace irin halitta ce?"


Abdussamadu ya ce, "Wallahi ban sani ba, Allah ya ba ka nasara."


Musa ya ce, "Matsa ka tambayi labarinta, wataƙila ta faɗa mana dalilin zamanta a wannan wuri."


Abdussamadu ya ja da baya ya ce, "Allah ya taimakeka, Wallahi ina jin tsoron ta halaka ni."


"Kada ka ji tsoro ya Sheik. Ai ɗaure take cikin ginshikin, ba za ta iya motsawa daga inda take ba balle har ta cutar da kai." In ji Musa.


Da Abdussamadu ya ji haka sai ya yi ƙarfin hali ya matsa kusa ga halittar, ya tsaya inda ya san ko ta miƙo hannu ba ta iya cim masa. Ya ɗaga murya ya ce mata, "Ya ke wannan halitta, menene sunanki? Menene sababin zamanki wannan wuri?"


"Ni Ifiritu ne daga cikin jinsin aljanu," halittar ta amsa wa Abdussamadu, "sunana Dahishu ɗan A'amashu, ni kamamme ne, ɗaurarre abin azabtarwa. Allah mai girma da ɗaukaka ya ɗaure ni wannan wuri yana azabtar da ni, ba zan iya fita daga wannan ɗauri ba har sai ranar da Allah ya fitar da ni, domin shi ne mai cikakken ƙarfi da iko a kaina."


Musa ya ce wa Abdussamadu, "Tambaye shi, me yasa ake azabtar da shi a cikin ginshiƙin dutse." Abdussamadu ya juya ya tambayi aljani abin da Musa ya tambaya.


Ifiritu ya amsa musu, "Labarina abin al'ajabi ne, ku saurara ku ji: akwai wani ɗan Ibilis wanda ya sana'anta wani gunki na tagulla, ya saka ni mai kula da wannan gunki. Shi wannan ɗan Ibilis sai ya ƙawata wa wani Sarkin aljanu da jama'arsa bautar wannan gunki. Sarkin nan kuwa babban Sarki ne wanda ke mulki da manyan tekuna da tsibirai. Sarki ne mai ƙarfin askarawa, ya mallaki askar dubu bisa dubu masu taurin rai wurin yaƙi, suna jan takubba a gabansa suna amsa kiransa a duk lokacin da ya kira su. Amma wannan Sarki da jama'arsa duka a ƙarƙashina suke, saboda ni ne mai kula da allan da suke bautawa. Ni da su duka mun yi tawaye ga mulkin Sulaimanu ɗan Dawuda. Idan Sarki da jama'arsa sun zo wurin bautar gunki, sai in shige cikin gunkin ina musu magana ba tare da sun san ni ke maganar ba, in hore su da aikata abin da nake so in hane su da barin abin da ba na so.


DUBA NA BAYAKaranta Kayatacciyar Hikayar Birnin Tagulla (4)


To, akwai wata 'yar Sarkin wadda take da himma ƙwarai wajen bauta wa wannan gunki, wani lokaci sai ta zo ita kaɗai ta yi ta yin sujuda a gaban gunkin. 'Yar Sarkin nan kyakkywawa ce ƙwarai da gaske, babu ma wata mace da ta kai ta kyau a wannan lokaci.


Daga littafin LABARUN DARE DUBU DA DAYA

Fassar:

Ibrahim Malumfashi

Danladi Haruna

Bukar Mada


Za mu ci-gaba Insha Allah.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user