Ka kula da tunane-tunanenka domin da sannu za su zama kalmomi.
Kula da tunani
Hoto: Pulse
Marubuci:- Sukairaj Hafiz Imam
Ka lura da kalmominka sosai domin da sannu za su zama ababen aikatawa.
Ka kula da abin da kake aikatawa domin da sannu za su zama ɗabi'unka.
Ka kiyaye ɗabi'unka don su ne za su zama siffofinka.
Ka kula da siffofinka domin a ƙarshe su ne za su yi bayanin Wane Ne Kai, kuma su ne ma'aunin makomarka a duniya da lahira.