Idan muka yi la’akari da adadin mata a al'ummarmu, za’a iya cewa sun fi maza yawa. Sanin kowa ne cewa mata musamman masu aure sun fi kowa rashin ƙarfi a Najeriya, duk da ƙwazonsu da hikimarsu.
Marubuci: Bello Galadanchi
To da waɗannan mata za su kasance suna da sana’o’i masu tafiya yadda ya kamata, shin ta yaya hakan zai shafi tattalin arzikin Najeriya da sauran ƙasashen yammacin Afirka da halin yanzu ake fama da matsi na rayuwa? Idan mata suna da sana’o’i masu inganci da tasiri da albarka, to babu shakka duka mutanen al'umma za su fa’idantu, kama daga mazajensu, da ‘ya’yansu, har zuwa matasa waɗanda za su riƙa taimaka musu.
Kuma idan mata suka ƙware a harkar sana’a, to ba za su ringa shiga wahalhalu ba idan miji ya samu matsala, ko aurensu ya mutu. Abun takaici shi ne mata masu yawan gaske suna nan yanzu haka a gidajen mazansu babu sana’o’in yi, babu kuɗin kashewa, kuma babu ilimi ko ƙwarewa wajen juya naira da kwabo.
Da yawansu suna yunƙurin fara sana’a, amma babu wahala sana’ar ta karye, komai ya lalace. To yanzu za mu duba irin matsalolin da mata masu zaman aure ke fuskanta, da hanyoyin warware su.
1. BA’A ƊAUKAR SANA’O’IN MATA DA MUHIMMANCI: Mutane da yawa suna yi wa sana’o’in da matan aure suke farawa kallon hadarin kaji, ba don komai ba, saboda mata ne. Wannan ya samo asali ne daga al'adun baya waɗanda suka hana mata ‘yanci, illa zaman gida da kula da yara. To yanzu zamani ya canza, kuma addini ya yarda mata su nemi kuɗi idan har ba a karya ƙa’idojin da addini ya gindaya ba.
Idan akwai wanda ya raina sana’arki, kuma yake kashe miki gwiwa, kar ki bari ya ɓata miki rai. Ki zage damtse wajen aiki tuƙuru domin ba shi kunya. Ki samu ƙawayenki ko ‘yan uwa domin mara miki baya, da ƙara miki ƙarfin gwiwa.
2. RASHIN ILIMIN KASUWANCI: Al'umma ta fi marawa mata baya su nemi ilimi a ɓangarori kamar kimiyya, koyarwa, likitanci ko kuma nazarin harkokin gida.
Adadin mata dake nazartar ilimin kasuwanci ba shi da yawa.
Idan har kina da ƙwazo kuma kina sha’awa, kar ki yi la’akari da adadin mata dake neman ilimin kasuwanci. Ke ma ki nema. Ilimi makami ne. Idan kasuwa filin daga ne, to ai ke ma kina buƙatar makaman da za ki iya amfani da su wajen cimma nasara da samun ganima. Ilimin kasuwanci zai buɗe miki idanu domin fahimtar duniyar kasuwanci, kuma idan har kika raba da ‘yan uwanki mata, to al'umma za ta samu ci-gaba.
3. KINA FARGABAR BAYYANA NASARORIN KI: Mata na samun ƙalubale wajen bayyana wa duniya irin nasarorinsu na rayuwa gudun kar a yi musu kallon haka-haka. Shi kuwa namiji sarkin alfahari ne. To kasuwanci abu ne da dole jifa-jifa sai mutum yana bayyana nasarorinsa domin kwantar da hankula da jawo abokan sana’a.
Kar gwiwar ki ta yi sanyi. Ki bayyana wa duniya baiwa da basirar da Allah Ya ba ki.
Kin san ko me yasa Hajiya Maryam Ikon Allah ta yi suna a kwanakin nan?
4. AIKATUWA: Mata na gudun ɓata wa jama’a rai. Kina so komai ya kasance a ƙarƙashin ki, sannan kina ɗaukar ayyuka da yawa. Hakan kuwa zai sa ki yi saurin gajiya.
Idan har kina so ki gina sana’arki domin nasara, to ki koyi rarraba aiki ga waɗanda za su iya, ko ki koya musu. Sannan kuma ki koyi cewa “a’a” idan abu bai kwanta miki a rai ba. Dole sai kin kasafta lokacinki yadda ya kamata, tare da daidaita rayuwar iyali, da ta kasuwanci.
5. KINA FARGABAR FAƊUWA: Tun mata na ‘yan ƙanana ake nuna musu cewa ba za su iya cimma burinsu yadda namiji zai iya ba. Wannan kuwa ya zama babban dalilin da ya sa mata ke tsoron faɗuwa a koda yaushe, kuma yana kashe musu gwiwa tun kafin su fara tunanin irin sana’ar da za su yi. Dole Ɗan Adam ya yi fargaba, amma kar ki bari hakan ya tsorata ki.
Rayuwar nan dole sai an faɗi ake tashi. Ko tsuntsaye da haka suka fara. Lamarin ya zama darasi a gare ki. Kar ki bari faɗuwar ki ta hana ki tashi. Ko ɗan jariri ba lokaci ɗaya yake fara tafiya ba.
6. BASHI: Saboda mata suna so su farantawa kowa rai, shi yasa mafi yawancin masu fara sana’a suke bada bashin kaya a lokacin da sana’a ‘yar ƙarama ce, ba ta kai ta kawo ba. Babu wani nazarin kasuwanci ko ilimi da ya nuna hasken haka.
Ki tara kayanki, har sai wanda zai bada kuɗi ya kawo. Idan har kika fara bada bashi, to kasuwancinki ba zai ci-gaba yadda kike so ba. Bashi yana hana ruwa gudu.
7. TUNANIN CEWA SAI SANA’AR MATA ZA SU YI: Mata da yawa sukan kulle kawunansu a cikin sana’o’i waɗanda al'umma ta gindaya musu a matsayin na mata. Idan sana’ar ba ta karya dokokin addini ba, to buɗe idanunki, ki zaɓi sana’ar da ranki yake so, ko wankin hula ne, ki fara. Idan ba ki iya ba, ki samu matasa su ringa yi miki, ke kuma kina biyansu. Kar ki bari tunanin al'umma ya zama katanga tsakaninki da burin ki.
A ƙarshe babu shakka mata suna fuskantar wani irin nau’i na ƙalubale wajen fara sana’a, amma ina gaya miki babu abin da ba za ki iya cimmawa ba idan kika sa kanki.
Idan kuwa har kika yi nasara, to za ki ƙarawa sauran mata ƙarfin gwiwa, kuma za ki raba ilimi da hikimar da kika koya da su.
Hakan zai taimaka sosai wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar mu ta gado.