Thursday 26 September 2024

Abubuwa 10 Masu Kawo Nasara A Farkon Fara Sana'a

Tura Wannan Zuwa Ga

Mene ne marabar wanda yanzu haka a lokacin nan da nake wannan rubutun yake samun riba, yana mayar da canji cikin aljihu da ragowar ku waɗanda kullum za ku tashi daga bacci, sannan ku koma ku kwanta da dare ba tare da samun ko ƙwandala ba? Tsoro.


Abubuwa 10 Masu Kawo Nasara A Farkon Fara Sana'a
Hoto: Business News daily

MarubuciBello Galadanchi


Ko sau nawa mai son ya yi sana’a ya tabbatar wa kanshi abin da yake da niyyar yi.


Karanta waɗannan abubuwa goma da duk wani mai so ya fara sana’a yake tsoro da hanyar shawo kan su. 


1. RASHIN SANIN DAGA INDA ZA A FARA.


Yawancin masu so su fara sana’a, ba su san daga inda za su fara ba bayan yanke shawarar hada-hadar da suke son yi. Ka fara da neman wani wanda ya cimma sak irin burin da kake son cimmawa. 


Yi bincike akan wannan mutum, da irin kasuwancin sa sannan ka tuntuɓe shi ka gani ko zai iya ba ka shawara da bayanai. 


Idan ba shi da lokaci ko sha’awar ya yi maka magana, to za ka gane cewa ya samu nasara, kuma kai ma za ka iya. 


Ka ci-gaba da gashi sannan ka yi abun da ya fi mayar da hankali, kana ci-gaba da tafiya, hanyar na ƙara maka haske. 


2. RASHIN ƘWAREWA.


Ta yiwu ka san abubuwa da yawa akan hajar ka ko sana’ar ka domin amsa duk wasu tambayoyi da kwastomomi za su yi maka, da ma warware musu duk wasu matsaloli da ka iya tasowa. Saboda haka kar ka damu kanka idan kana ji kamar ba ka son komai a wannan fannin ba. 


Dangane da abubuwan da ba ka sani ba, za ka iya samo amsoshi. Babu kunya wajen neman ilimi. Maganar gaskiya, wannan abu ne ma da ya kamata ka ringa yi kullum idan kana so ka ci-gaba, komai girman sana’ar ka. Ba za ka taɓa daina koyo ba: Ka saka rigar ƙwararre sannan ka sadaukar da kanka wajen tabbatar da sana’a mai burgewa. 


3. ANA MAKA KALLON MARA HANKALI.


Mutane da yawa za su yi maka kallon mara hankali a lokacin da kake fara sabuwar sana’a, kuma gaskiya suka faɗa. 


Abu mafi sauƙi na yi shi ne kar ka taɓa ɗaukar kasada, ka je ka yi ta yi wa wani aiki har ƙarshen rayuwar ka. 


Ya ka ji a ranka dangane da abun da na rubuta yanzu? Saboda kai ɗan kasuwa ne, kuma kasada a cikin jinin ka take. Ba za ka iya rayuwa babu ita ba. 


Dole a yi maka kallon mara hankali mana a lokacin da za a ga ka fara abu ƙarami, kawai ka yi imani da baiwar da Allah Ya ba ka, kuma ka jawo hankulan ragowar mutane domin su ma su yi imani da shi. Ka rungumi rashin hankalin ka, kuma ka ƙaunace shi saboda waɗanda ake kira marasa hankali su ne suke yin arziki da suna a duniya.


4. RASHIN JARI.


Fara kasuwa zai yi matuƙar sauki idan duk wanda yake da shawara zai iya shiga cikin banki kai tsaye a ba shi kuɗi ko ya samu wanda zai ba shi jari. To saboda wannan duniyar ba mafarkin ka ba ne, mai so ya fara sana’a ba tare da jari ba, dolen dole su fara ko ta halin ƙaƙa. 


A farko ba ka da jarin da kake buƙata, nan bada jimawa ba za ka gane cewa farawa sannu a hankali ba tare da komai ba ya fi. 


Ni ma da ₦1,500 na fara a watan Maris ɗin 2016. 


5. BA A YARDA DA KAI BA.


Ko kana shakkar cewa mutane za su mayar da hankali akan sana’ar ka saboda takardun ka ko jinsin ka, ko launin fatar ka, kai dai ka ɗauki ciniki da muhimmanci sannan ka faranta wa kwastoman rai. 


Mutane za su iya yanke shawara saboda siffar ka, amma babu wanda zai gardama da ƙwarewa da hazaƙa. Ko a farko babu wanda ya yarda da kai, a hankali mutane za su fahimta kuma za su yi imani da yadda kake gamsar da duka kwastomomin ka. 


6. RASHIN SAMUN KWASTOMOMI.


Akwai matuƙar fargaba a lokacin da kake tallata wa duniya baiwar ka ko sana’ar ka a karo na farko, kana damuwa ko za a daraja ta ko saɓanin haka. Sai idan ka fara kasuwancin ka ne a lokacin da dama kana da mutane da yawa da suka san ka, kuma suka amince da kai shi ne za ka ga an fara ba ka kuɗi, idan ba haka ba, to wallahi ba za ji an cika maka inbox ko WhatsApp da saƙonni ba.


Idan ka tunkari kasuwanci cikin nishaɗi da raha, akai-akai kana cika alƙawura, to babu shakka za ka ga canji a ɗan lokaci. A halin yanzu, sai ka dage wajen tsara yadda za ka ringa yin talla, sannan ka yi nazari domin ƙara ƙwarewa wajen sanin sana’ar, kuma ka yi wa kanka adalci saboda ka kai inda jama’a da yawa ba su kai ba. 


7. RASHIN SANIN YADDA ZA KA RIƘE SANA’AR BAYAN KA YI NASARA.


Gazawar rashin samun ƙalubalen da kusan duka masu fara sana’a suke fuskanta shi ne gabatar da sana’ar da duniya ta daɗe tana jira. 


Yi tunanin da ka kawo kaya ko ka buɗe shago, mutane sun yi layi suna son ganin ka ko kayan ka. Shin wannan abun baya razana ka? Kana tsoron samun nasara ne, ko fargabar rashin iya biyawa kowa buƙata?


Ba kai kaɗai ba ne. Samun nasara na jawo kaɗaici, amma dole sai an samu wani a sama domin gabatar wa duniya abin da take buƙata. 


8. SAKA IYALINKA DA ‘YAN GIDAN KU A WANI HALI.


A lokacin da kake fargabar cewa wannan sabuwar sana’a ba za ta iya biya wa iyalanka buƙatun su ba, ko za a iya shan kunya, to idan wani ya gaya maka cewa iyalanka da ‘yan gidanku su ma suna buƙatar wannan horo domin ƙara danƙon zumunci da iyali? Matar ka ko mijin ki, ko iyaye na buƙatar ba ka kafaɗar hutawa. 


‘Ya’yan ka za su so su ga ka sayo wannan motar ko ka gina wannan gidan da kake ta so. Saboda haka ka yi wa iyalin ka magana, ka gaya musu me ka saka a gaba, kuma za ka yi ƙoƙari wajen tabbatar wa ba su wahala ba, ko ka bar su da yunwa. Ka gaya musu ɓaro-ɓaro irin kasada da haɗari dake cikin wannan sabuwar sana’a da muhimmancin zuba lokacin ka da ƙarfin ka domin cimma nasara. Ka shirya iyalanka ko ‘yan gidan ku yadda ya kamata sannan ka tambaye su su yi wannan tafiya da kai. 


9. KUƊAƊEN DA KAKE SAMU BA ZA MA SU BIYA UWAR JARIN DA AKA SAKA BA.


Shi fa ɗan kasuwa musamman mai fara sana’a shi ne mutumin da yake buga-buga da ɗaukar babbar kasada wanda ba kowa ne zai iya ba. 


Idan ka zuba uwar jari a cikin sana’a, kuma ba ka ga riba ta fara fitowa nan take ba, kawai ka ci-gaba da gashi. Idan har ka miƙa wuya kafin ka fara samun riba, to ba za ka taɓa samun riba ba. Idan kuma har ka yanke shawarar daina sana’ar kafin ka fara samun riba, to ka tuna cewa a baya ka samu jari, saboda haka za ka iya sake samowa. 


10. KOMAI BA YA TAFIYA YADDA YA KAMATA


Ko ƙaramin yaro ba ya kawai miƙewa ya fara tafiya lokaci ɗaya. To idan ya tashi, sannan ya faɗi me ya kamata ya yi? Ya zauna ya yi ta kuka? A'a, ya ƙara miƙewa sannan ya sake gwadawa. 


Miƙewa tsaye na daga cikin wannan harka. Idan matsaloli suka addabi sana’a, wannan kawai ya nuna cewa ka sake miƙewa ne ka ƙara gwadawa.


A matsayin ka na ɗan kasuwa, na tabbata za ka iya samun nasara, saboda haka kar rugujewar sana’a ta firgita ka. Za ka iya sake miƙewa ka gwada. 


Yanzu da ka gama karanta wannan rubutun, je ka yi abu ɗaya da ya fi maka amfani a wannan rubutun. 

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user