Friday 27 September 2024

Asalin Labarin Soyayyar Majnun Da Laila (2)

Tura Wannan Zuwa Ga

Ya juyo ya soma tafiya sannan ya waigo ya ce, "Wallahi ba domin kada ka ce na matsa maka ba da na ƙara maka wani saƙon. Muhimmi ne kwarai na mance da shi. Jakada ya ce, "to matso ka faɗa min!" Suka sake rankayawa yana ta faɗa masa saƙo. Haka suka yi ta yi har kafin su ankara sai ga shi sun isa garin da Laila take.


Asalin Labarin Soyayyar Majnun Da Layla
Hoto: Wikimedia Commons

Marubuci:- Auwal Ilyas Adam


Jakada ya yi mamakin irin wannan soyayya, sannan ya ce da Majnun, "Babu buƙatar kai wa Laila saƙo gare ni domin kuwa ga shi mun zo garin da take." Da jin haka Majnun ya cika da farin ciki da murna. Ya faɗi sumamme don tsananin farin ciki.


Bayan ya farfaɗo Jakada ya ce masa, “Ba na so a gan ka, domin jama’a na iya kama ka su yi maka wulaƙanci kafin ka ga Laila. Ga wani kango can ka shiga ka zauna a ciki ka huta domin ka yi tafiya mai yawa. Zan isar da saƙonka ga Laila yanzun nan.”


Majnun ya yarda da shawarar Jakada ya shiga kangon nan ya zauna zuciyarsa na harbawa kamar ta tsage. Sakamakon tafiyar da ya sha duk ya yi futu-futu. Tufafinsa sun yi jawur da ƙura, gashin kansa duk ya kukkulle, ga ƙafafunsa sun yi fato-fato da ƙura da faso da kaushi. Ga shi nan dai yarbajila da shi. Duk da haka, da ya tuna cewar yana garin da Laila ta ke gaba ɗaya sai ya ji ransa ya yi fari fat. Ya cika da murna da farin ciki, zuciyarsa ta cika da bege ya riƙa rera waƙa yana cewa:


Na aika saƙona wajen masoyiya.


Zuciyata da rayukana gaba ɗaya.


Na miƙa su dukansu wajenki gimbiya.


Ke ce tawa haƙiƙa na faɗi gaskiya.


Na sallama miki kaina lahira da duniya.


Daga nan sai gajiya ta kama shi, ya ji yana so ya kwanta. To amma sai ya riƙa tunanin shin a wanne ɓangare Laila take? Domin ba ya so ya kwanta inda ƙafarsa za ta riƙa kallon jihar da take domin a wajensa hakan cin amanar ƙauna ne. Zai iya shurinta bai sani ba. Ya tsaya yana tunani, shin tana gabas ne ko yamma ko kudu ko kuwa arewa? Duk inda ya sa kansa sai ya tuna ƙila a wannan ɓangaren take, sai ya yi maza ya sake waje.


Daga baya dai sai ya samo igiya ya ɗaura a ƙafarsa ya samu gini ya ɗaura ƙafar, ya zamana yana reto kamar jemage. A wannan yanayi kuma bai fasa rera mata waƙa ba yana cewa:


Hajjina da Umarata na wajenki.


Makka ta da Madina na su ne ganinki.


Baitil Mukdis a wurina murmushinki.


Arzikina duk ni dai na ga dariyarki.


Na sallama kaina gaba wurinki.


Ƙishir ruwa na damunsa amma babu ruwa a kurkusa, haka ya haƙura wutar bege na hura shi, tana ƙone masa sassan jiki da zuciya.


Jakada ya yi sallama ƙofar gidansu Laila ta fito, ya ce mata, "Na yi ƙoƙari da gaske domin na yi miki magana, game da masoyinki Majnun wanda ban taɓa ganin tamkarsa ba a fagen so." Ya kwashe labarin duk yadda suka yi ya faɗa mata. Sannan ya ƙara da cewa, "Yanzu haka na bar shi a bayan gari domin gudun kada a wulaƙanta shi idan jama'a suka gan shi." Da Laila ta ji haka sai tausayinsa ya kama ta. Ta tafi wajen uwar goyonta ta ce mata, "Me yake faruwa ga mutumin da ya yi tafiyar mil ɗari da ashirin a ƙasa ba tare da ya huta ba?"


Tsohuwa ta ce, "Wannan mutumin ba zai rayu ba mutuwa zai yi." Laila na jin haka sai ta ji ta shiga damuwa, ta sake ce mata, "babu wani magani?" 


"Magani ɗaya ne a sanina. Dole ya sha ruwan saman da aka ajiye shi aƙalla shekara ɗaya, kuma dole ruwan ya zamana maciji ya sha daga gare shi. Sannan ya ɗaura igiya a ƙafarsa ya zamana kansa na kallon ƙasa zuwa wani lokaci. Idan ya aikata hakan wataƙila zai tsira da ransa."


Da ta ji haka sai ta yi tagumi tana cewa, "Wannan magani akwai wahalar samu, kai ba ma zai yiwu ba." Ta ɗaga hannu sama tana roƙon Allah ta ce, "Ya Allah mai ƙulla soyayya, mai bayarwa mai hanawa ka taimaki Qays Majnun ya samu wannan magani." Ta shafa sannan ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Soyayya ba ta da magani sai ita kanta."


Allah da ikonsa, Majnun na rataye da ƙafarsa a sama ga ƙishirwa na addabarsa sai ya kwance igiyar ya tafi neman ruwa. Bai samu ruwa ba sai wani tsohon kasko a wani lungu. Ya tarar da wani zabgegen maciji na shan ruwan. Ya kore shi sannan ya kafa kai ya shanye ruwan gaba ɗaya. Ya samu waje ya zauna yana waƙe-waƙensa.


Da gari ya waye Laila ta shirya abinci mai rai da lafiya ta kirawo kuyanga a ɓoye ta faɗa mata komai sannan ta nemi ta kai wa Majnun inda yake a bayan gari. Kuma ta ba ta saƙon a faɗa masa cewar ita ma tana nan tana ƙaunarsa kuma tana son ganinsa, amma da zarar ta samu dama za ta zo ta gan shi. Yayin da Kuyanga ta je wajen sai ta tarar da mutane biyu. Ɗaya ya haɗa kai da gwiwa kuma duk ya rame ga kansa nan duguzunzum, ɗayan kuma mai kiɓa jawur da shi, sai dai ya manyanta. Kuyangar ta dube su duka biyun ta ga babu wanda ya cancanci Laila ta so shi.


Ita kanta ma ta ji duk ba su kwanta mata a rai ba, balle kuma Laila. Duk da haka domin cika umarni sai ta ce, "a cikinku wane ne Majnun?" Mai kiɓar ne kaɗai ya ji sai ya taso wajenta ya ce, "Me ya faru?"


Sai ta nuna kwandon abinci ta ce, "cewa aka yi na kawo masa wannan daga Laila." Nan da nan ya karɓe abincin yana cewa "Ni ne Majnun." Ta faɗa masa saƙon Laila ya yi mata ɗan wasa haka sannan ya sa abinci a gaba ya cinye. Ya ragewa Majnun ɗan kaɗan.


Daga wannan rana kullum sai ta kawo masa abinci da saƙon baka, shi kuma sai ya cinye ya rage kaɗan domin Majnun. Kullum Laila kan tambayi Kuyanga, "Me ya ce ki faɗa min?" Sai Kuyanga ta ce, "Wai ya gode madalla da abinci."


Laila ta shiga kokwanto anya kuwa Majnun ɗinta ne? Bayan kwana uku dai da ta gaji sai ta ce da Kuyanga, "Yaya kika ga kamannin Majnun din?" Kuyanga ta ce, "Wani mai ƙiiba yana da saje da ƙasumba...ya manyanta..."


Farat Laila ta ce, "Wallahi ba shi ba ne, wannan Jakada ne wanda ya kawo min saƙonsa. Majnun ba tsoho ba ne kuma ba shi da ƙiba." Ta dubi Kuyanga ta ce, "Su nawa ne a wurin?" Kuyanga ta ce, "Su biyu ne." Laila ta yi ajiyar zuciya ta ce, "to yau ba za a kai abinci ba, amma zan sa ki musu wata jarrabawa domin mu gane Majnun na gaskiya." 


Ta ba ta wuƙa ta faɗa mata abin da za ta yi da ita.


Kuyanga ta tafi wajensu Majnun, ta tarar da Jakada na tsaye yana jiranta. Tana zuwa ya soma yi mata sannu da zuwa. Ya miƙa hannu da nufin ya karɓi gara, maimako haka sai ya ga ta fito da wata sharɓeɓiyar wuka. Ta ce, "Laila ba ta da lafiya, ana buƙatar jinin masoyinta kwalba ɗaya wanda da shi za a haɗa maganin. Shi ya sa na zo wajenka na ɗiba."


Yana ganin haka sai jikinsa ya kama rawa ya ce, "To ni dai ba masoyinta ba ne, kuma ba ni ne Majnun ba, gashi can a zaune." Ta wuce zuwa wajen Majnun ta faɗa masa kamar yadda ta faɗa wa Jakada. Yana jin haka ya karɓi wuƙar da hanzari, ya sumbace ta sannan ya ce, "Na gode wa Allah da ya ƙaddara cewa jinina ne zai warkar da ciwon masoyiyata." 


Ya darzaza wuƙar a hannunsa, maimakon jini ya zubo sai wajen kurum ya yi farat fat, alamar babu jini. Ya sake keta wani wajen, nan ma babu jinin saboda bai ci abinci ba ballantana a samu abin da ake buƙata. Da ya ga haka sai ya soka wuƙar a hammatarsa inda babbar jijiyar jini take, nan jinin ya riƙa ƙwarara. Ya tara ya miƙawa kuyangar wadda tuni tsoro da mamaki sun hana ta motsi. Yayin da ta koma gida ta shaida wa Laila irin abin mamakin da ta gani wajen Majnun, sai Laila ta yi ta kuka tana tausaya masa.


A cikin gari kuwa, labarin Majnun ya cika gari, sai aka samu wasu shaƙiyan matasa suka ɗauko kulake suka nufi inda yake. Tun daga nesa da Jakada ya hango su sai ya hau taguwarsa ya sulale ya bar Majnun yana waƙe-waƙensa yadda ya saba. Matasan na zuwa suka hau bugunsa suna shuri da naushi da yakushi. Suka ɗaure shi da igiya sannan suka tsaya daga nesa suna jifarsa. Da Laila ta ji labari sai ta sheƙo da gudu ta zo ta kare shi daga bugun mutane, ta riƙa zaginsu tana korarsu. Shi kuwa duk da yana ɗaure ga bugun da ya sha amma sai ya ji ransa ya yi fari fat da ganin abar begensa ya riƙa ambaton sunanta yana cewa:


Laila, Laila, Laila tawa ce.


Domin a kanki ne na haukace.


Wasu na kallona wai na karkace.


To amma fa yau na samu dace.


Da ganin haskenki ya masoyiya.


Iyayen Laila suka turo aka tafi da ita gida tana kuka. Da suka ga lamarin ya wuce saninsu sai suka yi shirin yin balaguro na wani lokacin domin a tsammaninsu idan suka tafi suka jima Majnun zai gaji da nemanta har ya saduda ya haƙura.


Suka shirya kaya suka tafi wani gari da ba su ambata ba, gudun kada ya ji ya bi su can. To amma kafin su tashi Laila ta rubuta takarda a ɓoye ta ba wa kuyangarta ta kai wa Majnun. Ya buɗe ya karanta cewar "Masoyina, bulaguro za mu yi wani gari mai nisa, haɗuwar mu za ta yi wuya anan. Idan za ka iya mu haɗu a zangon farko cikin sahara.".


Yana gama karantawa ya ce da kuyangar, "Ki gaishe ta da kyau da kyau, kuma ki faɗa mata cewar ina nan tafe."


DUBA WANNAN: Asalin Labarin Soyayyar Majnun Da Laila (3)


Lokacin da su Laila suka sauka a zangon farko ta tafi ita da kuyangarta zuwa inda ta ce masa ya je za ta same shi.


A tsammaninta bai isa ya zo wurin ba a wannan lokacin..........


Za mu ci-gaba Insha Allah.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user