Monday, 21 April 2025

Sakonnin Soyayya Da Za Su Sa Mace Dogon Tunani

Tura Wannan Zuwa Ga

A kan son ki na shirya shiga dukkan wani nau'in yanayi. Zan zama jarumin da zan yaƙi dukkan wani wanda zai kawo miki wargi.


Saƙonnin Soyayya Da Za Su Sa Mace Dogon Tunani
Hoto: Stock adobe

Marubuci:- Abdul'aziz Hamza KKR


Wani sanyi nake ji a can cikin tsakiyar zuciyata, a daidai lokacin da nake jin sautin zancen ki yana shiga cikin ƙofofin jikina.


Ke ce salsalar farin cikina, da ke nake tafiya cikin duniyar nishadina. A duk sa'in da na tuna cewa ke ce zaɓin raina dukkan wata damuwa tana rabuwa da ni.


Kusantowar zuwan lokacin da nake son na zo gare ki yana ƙara min ƙaimi wajen ganin na kawo kaina domin na yi tozali da ke.


Babu lokacin zuwan lokaci cikin lokacin da zan iya ɗaukar dogon lokacin da ban yi tunanin ki ba.


Sarauniya mai cikakken iko kina da ɗumbin ladabi da tunani mai zurfi, haƙiƙa zuciyata ba za ta saurara a cikin aikin nuna ƙauna a gare ki ba.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user