Tuesday, 22 April 2025

Illar Tunanin Gado

Tura Wannan Zuwa Ga

Tunanin gado shi ne tunanin da mafi yawa suka dogara da shi. Misali yanzu duka mutane ana son ai kuɗi, sai ka tambayi mutum ta yaya kake so kai kuɗi? Sai ka ji ya ce maka ina zuwa kasuwa ko ina kaza da kaza.


Illar Tunanin Gado
Hoto: Vecteezy

Marubuci:- Ibn Rushd II


Mafi yawa sun yarda da haka kuma suna kan hakan, kuma dai da yawa da suke da wannan fahimtar sun san wasu sun rayu da ita wannan fahimtar kuma ba su yi kuɗin ba.


To kai da kake zuwa kasuwa kake son yin kuɗi wanne tsari ne naka a ƙoƙarin ka na cika wancan burin naka?


Tunanin gado (tunanin da ake gada).


- Zai kashe ka.


- Zai binne nasarar ka.


-Zai mai da kai bawa.


-Zai sa ka rasa damar ka.

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user