Friday, 25 April 2025

Gina Goben Ka

Tura Wannan Zuwa Ga
Nasara ana ginata ne a hankali ba da garaje ba. Nasara ba ta zuwa da gaggawa, kuma ba ta samuwa a dare ɗaya kamar yadda rana ke fitowa.

Gina Goben Ka
Hoto: Jeweller Magazine


Ita nasara gini ce da ake kafawa a hankali, tana buƙatar juriya, dagewa da kuma bin hanya mai ma’ana. Kamar yadda ake shuka iri a gona, sai an jira ya girma, a kula da shi, sannan a girbe amfanin.

Wani fitaccen malamin falsafa, Aristotle, ya ce:


“Mu abin da muke yawan aikatawa ne. Don haka nasara ba aiki guda ba ce, ɗabi’a ce.”.


Wannan yana nufin cewa idan mutum yana fatan kai wa wani matsayi ko cimma wata manufa, dole ne ya maida abin da zai kai shi can zama ɗabi’a. wato abu da zai dinga aikatawa kullum.

Misali

Kana son ka zama ɗalibi nagari? To, kada ka jira lokacin jarrabawa ka fara nazari. Ka maida karatu na yau da kullum, koda shafi ɗaya ne. Da haka za ka samu ƙwarewa fiye da wanda ke karatu kwatsam.

Haka ma lafiyar jiki, ba sai mutum yana da damar shiga manyan wuraren motsa jiki ba. Ka iya fara yawo da safe na minti goma, kullum. Wannan abu ne ƙarami, amma da zaran ya zamo ɗabi’a, zai haifar da babban canji a rayuwar mutum.

James Clear, marubuci da masani kan ɗabi’un Ɗan Adam, ya ce:

“Duk wani aiki da kake yi yau, kamar ƙuri’a kake kaɗawa ne don irin mutumin da kake so ka zama gobe.”

Wannan yana ƙarfafa cewa mu lura da abin da muke maimaitawa, domin a cikin hakan ne akwai asalin ginin rayuwarmu.

Confucius kuwa ya ce:

“Koda tafiyarka tana tafiya a hankali, babu laifi muddin ba ka tsaya ba.”

Abin da wannan ke nufi shi ne: komai da ka sa gaba, muddin kana ci gaba, ko da a hankali ne, za ka kai inda kake so.

Misali mai sauƙi shi ne: ɗalibi mai halartar makaranta kullum, yana sauraro, yana tambaya da karatu, ya fi wanda yake zuwa lokaci-lokaci. Sakamakon su a ƙarshe ba zai daidaita ba, saboda mai maimaitawa yana gina fasaha, yana samun ƙwarewa da fahimta.

Don haka, idan kana da buri ko a karatu, ko a sana’a, ko a neman dukiya, sai ka maida hanyar da za ta kai ka ga hakan ɗabi’a.

Ba sai ka fara da abu mai girma ba. Farawa da ƙanƙani, amma a kullum, shi ne hanya mafi kyau. A haka ne za ka gina nasara wacce za ta ɗore.

A taƙaice: Maimaita abu na gari kullum, zai zama ita ce hanyar da kake gina gobenka.

Ɗabi’a mai kyau ita ce ginshiƙin nasara mai ɗorewa.
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user