Showing posts sorted by date for query Imran Musa Jahun. Sort by relevance Show all posts
Showing posts sorted by date for query Imran Musa Jahun. Sort by relevance Show all posts

Friday, 3 January 2025

Kalaman Kiran Waya Na Barka Da Rana

Kalaman Kiran Waya Na Barka Da Rana

Ke ce hasken raina, ke ce jina, ganina da duk wani abu nawa, son ki daga Allah ne, a lokaci ɗaya da ganin tsararren hotonki na ji kibiyar son ki ta ratsa ruhina. Ke kaɗai ce a gare ni da zuciyata, son ki azimun ne. Ina son ki da gaske.


Kalaman Kiran Waya Na Barka Da Rana
Hoto: Every pixel

MarubuciImran Musa Jahun


Amincin Allah Ya tabbata a gare ki jinin jikina. Da soyayyarki ilahirin jiki na yake motsi, sanyi ko zafi hakan ba ya sanya ni kasalar kallon hotonki, tsanani ko azaba ba sa sanyawa na rufe bakina da ambaton kyakkyawan sunanki. 


Tabbatuwa mafi bayyanuwa a raina shi ne soyayyarki. Ƙaƙƙarfar iskar son ki ta lula da ni cikin sararin samaniya ta yadda ba na hangen duk wata 'ya mace face ke, babu wata juriya ko ƙarfi da ke wanzuwa gare ni face da ƙarfin ambaton harafofin sunayenki.


Idanuwana sukan makance na rasa ji da gani a duk sa'adda kyakkyawar surar jikin ki ta sauka a idanuwana, sautin muryarki ya kan narkar mini da zuciya har na ji kunnuwana sun gaza tantance zaƙin muryarki illa iyaka ta fi duk wani sauti zaƙi da daɗi. 


Bakina ya kan zama tamkar idanuwana a buɗe a duk sa'inda yalwataccen murmushin ki ya bayyana a gare ni.


Ƙafafuwa da hannayena ba sa iya ɗaukar jikina a duk lokacin da kika furta min lafiyayyun kalamanki. Ki so ni mai kyau!

Wednesday, 25 December 2024

Zafafan Kalaman Soyayya Da Karamar Yarinya

Zafafan Kalaman Soyayya Da Karamar Yarinya

Zarah ki ke cikin taurari, Sarauniya cikin Sarakuna haka Gimbiya kike cikin kuyangi. Ke daban ce ga komai, ƙaunarki ita ce jarina, na kan manta da komai na tuna ki.


Zafafan Kalaman Soyayya Da Karamar Yarinya
Hoto: Adobe Stock

MarubuciImran Musa Jahun


Amincin Allah ya tabbata a gare ki motsin zuciyata. Raunanniyar zuciyata ba za ta iya juriyar rashin ki a gare ni ba, babu wani daɗi da zai kai matsayin daɗin da zan ji idan kika kasance tare da ni ma'ana ki aminta da ni ki ce kina sona. 


Ƙunci ko damuwa ba ya hana ni ambaton haruffan sunayenki domin ko su ne mafi daɗi a gare ni a jerin sunayen 'yammata.


Kyawunki ya kai matuƙa ta yadda ba zan iya jeranta shi da dukkan wani kyau ba.


Rurutacciyar ƙaunarki ta cinye dukkan komai nawa, da sonki zuciyata ke rayuwa.


Na kamu da son ki a sa'ilin da ban yi aune ba, ina son ki, zan ci gaba da son ki har abada. Ke ce kawai a zuciyata, ke ce alfaharina, da ke nake a kodayaushe. Ki so ni.


Tsiron son ki ya yalwatu a ruhina a lokaci ɗaya da na kalli kyakkyawar surar jikin ki, kina da kyawun da duk wani ɗa namiji sai ya jinjina miki, ko cikin kyawawa ke ce Sarauniyar su. 

Wednesday, 18 December 2024

Gajerun Kalaman Soyayya Na Dare

Gajerun Kalaman Soyayya Na Dare

Ba na tunanin samun kamar ki domin raina gabaɗaya ya kamu da son ki. Na sani cewa zan yi alfahari da ke idan kika furta kalmar ina son ka a matsayin amsar ki gare ni.


Gajerun Kalaman Soyayya Na Dare
Hoto: Pinny Pinny/Dreams time

MarubuciImran Musa Jahun


Lambar yabo a gare ki mai sona.


Zinariya masoyiyar raina.


Gimbiya alkhairin rayuwata.


Sarauniya cikon farin cikina.


Tauraruwa hasken ruhina.


Lokaci ɗaya rurutaccen son ki ya ruru a zuciyata, sai dai sanin cewa ke wata daban ce cikin 'yammata, ma'ana ke tamkar sarauniyar su ce, shi ya sanya na miƙo gaisuwar ban girma a gare ki sahibata.


Ina son ki da wani irin so mai ɗauke da sinadarin ratsa dukkan sassan jiki. Ke ɗaya ce mafi haske da dawwama a zuciyata. Ina son ki.

Friday, 13 December 2024

Gajerun Kalaman Soyayya Da Kwaila

Gajerun Kalaman Soyayya Da Kwaila

Bayan dubun gaisuwa mai fesar da tsantsar so da ƙauna, mara misaltuwa, jinjina da yabo da kirari su ƙara tabbata a gare ki yake burin zuciyata, fatana shi ne mallakarki a matsayin uwar 'ya'yana abar alfaharina, burina mu kasance tare ba na fatan rasa ki domin muhimmancin ki a gare ni.


Gajerun Kalaman Soyayya Da Kwaila
Hoto: Prostock Studio/ISTOCK PHOTO

MarubuciImran Musa Jahun


Zuciyata da ruhina suna azabtuwa ta dalilin son da nake miki, ƙishin ruwan son ki ya gallabi dukkan ilahirin sansanin zuciyata na rasa yadda zan yi, domin samun sassauci daga raɗaɗin da zuciyata ke faman yi shi ne nuna soyayyar ki a gare ni, rashin samun haka daga gare ki kan iya janyo barazana ga rayuwata.


Na ɗauki alƙawarin samar miki da farin cikin zuciyar ki, ba zan taɓa sa wa ki ji ba daɗi a cikin zuciyar ki ba. Ina son ki.


Ke na ba mulkin zuciyata ki mulke ta yadda kike so taki ce kuma mallakin ki ce.


Ina son ki, ina ƙaunar ki ba na fatan rabuwa da ke, saboda irin son da nake miki.


Rashin samun soyayyar ki a gare ni zai iya zama silar faruwar komai, burina shi ne ki ba ni dama domin nuna miki soyayya ta haƙiƙa.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu sunan adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.

Saturday, 7 December 2024

Ma'anar Bege A Tsakanin Masoya

Ma'anar Bege A Tsakanin Masoya

Mene ne Bege a soyayya?


Bege shi ne mutum kodayaushe ya dinga tunanin wanda ran sa ke so, ba wai ana nufin ya zauna kodayaushe ba shi da aiki sai tunani ba. Abin da ake nufi anan shi ne babu dai yadda za a yi a ɗauki lokaci ba a yi tunanin masoyiya ko masoyi ba.


Ma'anar Bege A Tsakanin Masoya
Hoto: Times of India


MarubuciImran Musa Jahun


So tamkar mayafin rufa ne shi ya sa ma wasu kan yi wa so laƙabi da suna marurun zuciya.

Friday, 6 December 2024

Zazzafan Sakon Karshe Ga Saurayi Mayaudari Daga Budurwa

Zazzafan Sakon Karshe Ga Saurayi Mayaudari Daga Budurwa

Ka cuce ni, ka yaudare ni, ka ha'ince ni, tsakanina da kai sai tsinuwa kodan da ma an ce ku maza haka halin ku yake na mugunta da cin zali ga duk wata mace, musamman waɗanda suka amice muku.


Zazzafan Sakon Karshe Ga Saurayi Mayaudari Daga Budurwa
Hoto: Pathdoc/Stock Adobe

MarubuciImran Musa Jahun


Allah ya isa ita ce kalmar da zan aika maka, mayaudari kawai, ba zan taɓa yin wani abu da sunan yafiya a gare ka ba.


Kaicon ku tir da halin ku, daga tsohuwar budurwar ka.

Sakonnin Soyayya Ga Budurwar Da Za A Raba Ku Don Janyo Hankalin Ta

Sakonnin Soyayya Ga Budurwar Da Za A Raba Ku Don Janyo Hankalin Ta

Da yawan masoya na rabuwa saboda tilastawa daga wajen mahaifan ɗaya daga cikinsu, idan irin hakan ta faru gare ka, ga kaɗan daga irin saƙon da za ka tura mata domin jawo hankalin yarinyar gare ka.


Sakonnin Soyayya Ga Budurwar Da Za A Raba Ku Don Janyo Hankalin Ta
Hoto: Raw pixel

MarubuciImran Musa Jahun


Ga su kamar haka:


Me ya sa ake son na rasa rayuwata tunda sauran ƙuruciyata?


Ban taɓa ganin inda aka raba hanta da jini ba kuma aka rayu ba.


Babu sauran numfashi daga ranar da zuciya ta daina amsar jini.


Babu sauran farin ciki daga ranar da aka raba uwa da ɗan ta.


Rayuwa za ta zamo mai ƙunci gare ni daga ranar da aka raba ni da ke.


Me ya sa ake son rusa tanadin da na daɗe ina yi miki don kyautata rayuwarki?


Zan iya jurewa duk ƙaddara amma ban da ta rasa ki, har yanzu ina kallonki a matsayin matata. 


Har gobe zuciyata tana muradinki, kuma rayuwata ta ginu saman farin ciki saboda tarayyar soyayyar mu, yanzu aka raba mu mece ce makomar rayuwar mu?

Monday, 2 December 2024

Sakonnin Soyayya Na Bayyana Damuwar Zuciya Ga Budurwa

Sakonnin Soyayya Na Bayyana Damuwar Zuciya Ga Budurwa

Ba ni da laifi domin ko shawara zuciyata ba ta nema ba a lokacin da sonki ya kawo ziyarar bazata, sai dai kawai na ji farin cikina,burina,walwala da annashuwata duk suna a cikin duban tsaleleiyar fuskarki ne.


Saƙonnin Soyayya Na Bayyana Damuwar Zuciya Ga Budurwa
Hoto: Mirror

MarubuciImran Musa Jahun


Yanzu na yi laifi idan na nemarwa raina abinda ya fi so? Koda ba za ki so ni ba, to ina alfahari da cewa ba za ki taɓa samun wanda ƙaunarki ta cuɗanya da farin cikinsa ba tamkar ni.


Ban da laifi, ki yi tunani za ki tabbatar da hakan domin burin zuciya samun abin da take so. Don haka ya zama dole na sanar da ke cewa ke ce zuciyata ke so.


Ni kaina ban san lokacin da zuciyata ta kamu da tsananin ƙaunarki ba.


Sau da yawa na kan rasa bacci saboda tsananin zafin son ki, na daɗe ina zama dirshan a hanyoyin wucewarki domin kawai na ga tafiyarki irin ta ƙasaita. Ke ce kaɗai ke wahaltar da tunanina, ki yi mini uzuri.


A ƙarshe ina fatan kalamaina za su zamo masu sauƙin fahimta a gare ki.

Friday, 29 November 2024

Alamomi 9 Na Gane Mace Ba Ta Son Ka

Alamomi 9 Na Gane Mace Ba Ta Son Ka

1. Idan budurwa ba ta sonka to ba za ta taɓa yi maka maganar aurenku da ita ba, ko maganar yadda tsarin aurenku take so ya kasance ba.


Alamomi 9 Na Gane Mace Ba Ta Son Ka
Hoto: Shutterstock

MarubuciImran Musa Jahun


2. Idan budurwa ba ta son ka, za ta yi ta maka ƙorafi akan ƙananun buƙatunta.


3. Idan budurwa ba ta son ka to za ta yi maka wasa da dariya da murmushi ne kawai a lokacin da za ka ba ta kuɗi (money), ko kuma a lokacin da take so ka ba ta kuɗi.


4. Idan budurwa ba ta sonka ba za ta iya kiranka a waya da kuɗinta ba sai dai ta yi maka filashin don haka iya mutuncin da za ta iya maka kenan ta yi maka filashin amma ba za ta taɓa iya kiranka a waya ba.


6. Idan budurwa ba ta son ka to ba za ta taɓa raka ka wani waje ba, kuɗin da ita za ta karɓa daga wajenka kawai ta fi so.


6. Idan budurwa ba ta sonka ba za ta ringa ba ka shawara akan rayuwarka ba, sannan ba za ta nemi ka ba ta shawara akan rayuwarta ba.


7. Idan budurwa ba ta son ka ba za ta taɓa kawo muku ziyara a gidanku ba.


8. Idan budurwa ba ta son ka to ba za ta taɓa gaya maka gasakiya akan labarin kanta ba, sai dai ta yi ta maka ƙarairayi.


9. Idan budurwa ba ta sonka to ba za ta taɓa yarda a ce ka karɓi wayarta ka gani ba, saboda akwai lambobin samarinta da yawa a ciki.

Wednesday, 27 November 2024

Zazzafan Kalaman Soyayya Na Rarrashin Budurwa

Zazzafan Kalaman Soyayya Na Rarrashin Budurwa

Kin san ina sonki!!! Me ya sa za ki guje ni a daidai wannan lokacin da na kamu da matsananciyar soyayyarki a zuciyata? 


Zazzafan Kalaman Soyayya Na Rarrashin Budurwa
Hoto: Lysenko Andrii/Shutterstock

MarubuciImran Musa Jahun


Wannan ba wani abu ba ne da ba ki sani ba, ni kaɗai ne saurayi na farko da ya fara ganin ki ya ce yana son ki a duniya, ba don ba ki da kyau ba, babu wani namijin da zai gan ki bai yi fatan ki zama masoyiyar shi ba. 


Wannan shi ne abin da nake ji a zuciyata tun lokacin farko da na ɗora idanuwana a kan hotan fuskarki.


Ina son ki kuma ina ƙaunarki, ki amince da ni, ki amshi batuna, ki riƙe shi bisa amana domin zan ba ki kulawa har ƙarshen rayuwar mu.


Ya kamata ki saurare ni, kuma ya kamata ki yi wa kalamaina fahimta mai kyau.


Amsar ki nake jira masoyiya.

Sunday, 24 November 2024

Zafafan Kalaman Karfafa Soyayya Ga Masoyiya

Zafafan Kalaman Karfafa Soyayya Ga Masoyiya

Duk da cewa da akwai kyawawan 'yammata a duniya da yawa amma sai na ga kin yi musu zarra, ma'ana kin kere su wajen kyau da haɗuwa.


Zafafan Kalaman Ƙarfafa Soyayya Ga Masoyiya
Hoto: Next luxury

MarubuciImran Musa Jahun


Ke mai kyau ce, dole a ce kina da kyau, haka surar ki kyakkyawa ce wadda ko maƙiyinki ya san da hakan.


Ina son ki kodayaushe.


Rurutacciyar wutar ƙaunarki tana ci-gaba da ruruwa a zuciyata wanda hakan ya sanya son ki yake sake kwaranyuwa a cikin zuciyata.


Na ji son ki ne a take a yayinda idanuwana suka yi arba da tsaleliyar kyakkyawar fuskarki. 


Sai na ji bugun zuciyata yana fita da ƙarfi, dukkan wani kuzari na rasa shi, kin dolantar da ni sosai hakan ya sa na zama mara wayo.


Tauraruwarki ba za ta taɓa disashewa a zuciyata ba, abadan da'iman son ki yana tare da ni.


Haƙiƙa kin ɓoye ni a cikin hazo na so ta yadda ba na kallon kowacce 'ya mace sai ke. 

Tuesday, 5 November 2024

Shawara Ga Sabon Saurayi Mai Son Fara Soyayya

Shawara Ga Sabon Saurayi Mai Son Fara Soyayya

Kar ka zurfafa soyayyarka ga abin da ba ka da tabbas a kansa, domin soyayya ta zama tamkar ruwan sama ne a yayin da yake sauka daga sama zuwa ƙasa, wanda babu tabbas akan yanayin shi.


Shawara Ga Sabon Saurayi Mai Shirin Fara Soyayya
Hoto: Marriage

MarubuciImran Musa Jahun


Akwai lokutan da yake kasancewa ruwan sama ya zo da ƙarfi, kar ka bayar da amannar cewa da ƙarfin za'a ɗauke shi, akwai lokacin da ruwan sama zai sauka a hankali kar ka bayar da gaskiyar cewa a hankali zai ɗauke.


Ka kwatanta waɗannan misalan a matsayin soyayyarka, babu tabbacin yadda ake son ka da farko haka za'a ci-gaba da sonka har abada. Don haka soyayya ba ta da tabbas.


Idan ka ɗauki soyayya da zafi, tamkar kana matsanancin gudu ne kan titi cikin duhun daren da ba za ka iya koda ganin hannunka ba, kenan a kodayaushe za ka iya faɗawa rami ko ka haɗu da abin da ba ka yi tsammani ba.


Haka soyayya ta ke, sai da lura.

Monday, 30 September 2024

Gajeren Sakon Nuna Amincewar Soyayya Ga Masoyi

Gajeren Sakon Nuna Amincewar Soyayya Ga Masoyi

Ka buɗe mini zuciyarka tare da barka na shiga ciki ta zamo sirrina.


Saƙon Nuna Amincewar Soyayya Ga Masoyi
Hoto: Medium

MarubuciImran Musa Jahun


Tabbas ina son ka a cikin raina, kai kaɗai kake ɗebe mini kewa, idan na ji muryarka.


Ka kewaye dukkan zuciyata gami da ruhina.


Son ka shi ne komai a gare ni.


Muradina gare ka shi ne ka zamo uban yarana.

Sunday, 29 September 2024

Gajerun Kalaman Sanyaya Zuciyar Masoyiya

Gajerun Kalaman Sanyaya Zuciyar Masoyiya

Kar ki manta da ni a rayuwarki, haka ni ma zalika duk rintsi kina raina.


Kalaman Sanyaya Zuciyar Masoyiya
Hoto: Discover hubpages

MarubuciImran Musa Jahun


Na miƙa mukullin zuciyata gare ki, ki buɗe min zuciyarki na cike dukkan guraban da suke marhabin da ni, wanda ba wani mahaluki da zai iya mallakar zuciyarki idan ba ni ba.


Ki ce mini ni ne naki na har abada, ni ma zan ce hakan don mu kasance cikin jin daɗin duniya.


Ma'anar kalmar ina son ki (I LOVE YOU).


I = Na sallama, ke ma ki sallama

mini zuciyarki.


L = Ji! Ni ne irin wanda za a so.


O = Lura sannan ki bari na samu gurbi a zuciyarki.


V = Tabbas ina son ki tawa.


E = Kin kewaye dukkan zuciyata.


Y = Son ki shi ne nawa farin cikin.


O = Ki buɗe ƙofar zuciyarki na shiga.


U = Kafin na shigo ki mini kyakkyawan gurbi a cikin zuciyarki.


Ki tuna fa cewa duk inda ya zama ba so, duniya za ta zama cikin halin ƙunci na ba ranar da za ta daina, rayuwa za ta zama mara amfani gare mu, mutane za su kasance cikin rashin zaman lafiya a tare da su.


So shi ne sirrin rayuwarmu.


So shi ne farin cikin mu da nasarorinmu na rayuwa.


Na sallama zuciyata gami da ruhina gare ki.


So shi ne ya haɗa komai da komai na jin daɗin duniya, saboda Adamunmu shi da Hauwa'u sun zamo uwa gare mu tunda tsatsanmu ya zo ɗaya, mu daina ƙin junanmu.


Ku kasance da ni zan ci gaba da nishaɗantar da ku a kodayaushe.

Monday, 23 September 2024

Zafafan Gajerun Kalaman Yabon Kwalliya Da Ado Na Masoyiya

Zafafan Gajerun Kalaman Yabon Kwalliya Da Ado Na Masoyiya

Kina burgeni idan har na ga kin yi kwalliya da jan kayanki, ba na jin shakkar nuna wannan kyakkyawar fuskar taki.


Kalaman Yabon Kwalliya Da Ado Na Masoyiya
Hoto: Deposit photos

MarubuciImran Musa Jahun


Murmushin da ki kai ne ya haddasa fitowar fararan haƙoranki, a sannan ne na yi tozali da tsagaggiyar wushiryarki, bayan kin lumshe daradaran idanunuwan nan naki a lokaci ɗaya kika ƙara tafiya da zuciyar da na mallaka miki.


Kina ƙara yin kyau idan har ki kai wa daradaran idanuwan nan jagira.


Kina ƙara shiga zuciyata idan na ga kin shafa siririn hancin nan naki, musamman ma a ce kin yi mini farin da kike da idanuwanki.


Dukkan rayuwata na ba ki, na san ba za ki wasa ba, za ki riƙe ta da hannunki, roƙona ga Allah shi ne yasa na zamo mijin ki.


Ba na tunanin komai, hatta mafarki ba ya zuwar min sai da sunanki, koda abinci zan ci sai na haɗa da kallon hotanki, koda hira za ai da ni dole sai an sako min maganar ki.


Kin ce kin amince da ni har na zamo Uba ga 'ya'yanki, na kan yi farin ciki idan na tuno ba kya wasa da addininki.


Kin kasance rayuwata, ni kuma na zama taki, ki ba ni kulawa, ni kuma na ɗauki alƙawarin ninka taki.


Kullum burin rayuwa na tarairayeki, duk mai san farin cikina to ya faranta miki.


Bayan kallon kyawawan haƙoranki na shiga shauƙi har na manta kaina saboda kyawunki, kin iya kwalliya musamman ma na ga kin shafa jambaki a ɗan ƙaramin bakin ki.


Ina jin farin ciki saboda na same ki da tarbiyyarki, ba na jin kiran da ba shi da alaƙa da sunan ki.

Wednesday, 18 September 2024

Abubuwa 20 Da Za Ku Yi Mace Ta Makance A Soyayyar Ku Kamar Tsafi

Abubuwa 20 Da Za Ku Yi Mace Ta Makance A Soyayyar Ku Kamar Tsafi

Ya kai ɗan uwana ka sani ɗabi'ar 'ya mace kamar iska ce da take kaɗawa a hankali, idan ka furta wa 'ya mace kalma mai kyau to za ka tashi a tutocin soyayyarta. Idan kuma kai mata magana mara daɗi koda kalma ɗaya ce za su rusa soyayyarka.


Abubuwa 20 Da Za Ku Yi Mace Ta Makance A Soyayyar Ku Kamar Tsafi
Hoto: Shutterstock


MarubuciImran Musa Jahun


Lallai ne ana son namiji ka siffantu da waɗannan siffofi ashirin ɗin domin ka samu cikakkiyar soyayya da ƙauna a wurin

matarka.



1. KA MUTUNTA MATARKA: Ka nuna mata kai da ita duk abu ɗaya ne ba bambanci kana da buri ita ma tana da shi, kana da sha'awa ita ma haka, lallai ne ka mutunta ta, kamar yadda kai ma kake son ta girmamaka.


Manzon Allah (S.A.W) yana cewa "Duk wanda ya samu mace to ya girmamata.". Don haka kuskure ne da jahilci a hanawa mace 'yancin faɗar ra'ayinta ko neman shawararta, ko tattaunawa da ita a cikin wasu al'amura.


Kar a maida ita kamar kayan

wasan yara, ba a nemanta sai za a buƙaceta, duk wanda yake wa mace irin wannan ɗabi'ar tabbas zai rasa soyayyarsa a cikin zuciyar matarsa.


2. KA ZAMA ABOKIN MATARKA: Ma'ana ka yi mu'amala da ita ta kowanne ɓangare, kada ka bar wata kafa a buɗe ta yadda za ta fahimci ba ka damu da ita a wannan ɓangaren ba, lallai ne ka zama mai ɗebe mata kewa ta kowanne ɓangare, mai saka ta farin ciki da nutsuwa.


3. KAR KA ZAMO MAI CIN DUNDUNIYAR TA: Ma'ana kai a kullum burinka so kake ka ga ta yi laifi kai kuma ka buɗe mata wuta. A'a! Ka zama tamkar mai koya mata yadda

za ta yi rayuwa, inda ta kauce sai ka saitata domin a kullum ita mai raunin tunani ce idan har ta aikata mara kyau, to kada ka sakamata da mara kyau. A'a! Sai ka saitata da mafi kyau, tabbas za ka dace da soyayyarta.


4. LALLAI NE KA ZAMA MAI JURE WAUTAR 'YA MACE: Ka zama mai kyautata zamantakewarka gare ta, ka saki fuskarka

gare ta, ta yadda ba za ta rainaka ba, ma'ana kada ka yi sakacin da za ta iya raina ka.


5. KA ZAMA MAI TAIMAKONTA: Yayinda ta

shiga tsanani, kada ka yi banza da ita.


6. Ka zama mai ɗebe mata kewa yayinda

take ita kaɗai.


7. Ka zama shimfiɗar kwanciyarta yayinda

ta buƙaci bacci.


8. Kar ka nuna mata ƙosawa ko ka fara gajiya da ita.


9. Idan ta kamu da cuta kar ka share ta, ka yi iya ƙoƙarin ka wajen nema mata waraka.


10. Idan za ka shigo mata gida to ka shigo da murmushi, kuma idan za ka fita ka fita da murmushi. Hmmmmm.


11. Kar ka tozarta ta yayin da ta nemi wata

buƙata a gare ka, kuma idan har za ka yi mata alkhairi, to kada a yi mata mafi ƙaranci.


12.  Idan ta yi abu mai kyau, ka yabe ta ka gode mata.


13. Idan ta yi kuskure, ka yafe mata.


14. Kar ka yabi wata mata a gabanta.


15. Ka zama mai tsafta da kwalliya.


16. Kar ka zama mai yawan mita da dawo da kuskuren da ya wuce.


17. Ka zama mai kishin iyalinka, kar ka zama Dayyus.


18. Ka zama mai girmama 'yan uwanta,

musamman iyayenta.


19. Ka zamo mai kiyaye sirrinta, kada ka

zama mai yaɗa kuskurenta a cikin ɗaiɗaikun jama'a.


20. Kar ka zama mai son kai, wato ka girmama kanka, ita kuma ka wulaƙantata.


Da fatan za mu kiyaye.


Domin ci gaba da samun ire-iren waɗannan abubuwan, sai ku ci gaba da kasancewa tare da mu a kodayaushe.

Wednesday, 4 September 2024

Karanta Kirarin Masoyi Mai Dadin Gaske

Karanta Kirarin Masoyi Mai Dadin Gaske

Kai ne ɗaya wacce zuciyata ke hange.


Na gaishe da jarumina.


Mai kyawun idanuwa.


Kirarin Masoyi
Hoto: Kinda Reiter

MarubuciImran Musa Jahun

Takawar ka lafiya Habibina.


Sannu, sannunka ya kai mai wanke zuciyata.


Saraki kake Ɗan Sarki.


Na gai da gwarzo, hamshaƙi a zuciyata.


Mai tausasasshiyar murya.


Mai daidaitaccen baki.


Gaishe ka ma'abocin iya kalamai.


Ina son ka. Ina ƙaunar ka.


Abadan da'iman kai ne dai tauraron 'yan maza.

Friday, 30 August 2024

Karanta Kirarin Masoyiya Mai Ratsa Zuciya

Karanta Kirarin Masoyiya Mai Ratsa Zuciya

Na gaishe da sarauniyar kyawawan duniya.


Ma'abociyar yalwatacciyar kyakkyawar fuska.


Mamallakiyar haskakakken fararen idanuwa.


Kirarin Masoyiya Mai Ratsa Zuciya
Hoto: Freepik

MarubuciImran Musa Jahun

Sannu, sannun ki gimbiya mai tsararriyar halitta mai kyau da diri.


Takawar ki lafiya ƙasaitacciya, ɗawisu kike mai tafiyar ƙasaita.


Zarah kike mai haske na sirri.


Na gaida ma'abociyar iya lumshe idanuwa.


Dukkan kuyangin 'yammata a bayan ki suke, sahiba ta masoyiyata.


Na gaida ke zinariya.


Zabiya kike mai siririyar zazzaƙar murya.


Ba su kai ba, kuma sun gaza kamo ki.


Ke ce kaɗai tilo mai haske gani na.

Sunday, 11 August 2024

Wasikar Yabo Ta Soyayya

Wasikar Yabo Ta Soyayya

Sallama a gare ki tare da tausasan kalamai masu tausasa zuciya.


Wasiƙar yabo
Hoto: City living


MarubuciImran Musa Jahun


Ki sani yake masoyiyata tun da Allah maɗaukakin sarki ya yi ni ban taɓa ganin ko jin zazzaƙar murya mai tausasa zuciyata cikin daƙiƙa ɗaya tamkar taki ba.


Kyawun fuskar ki tare da kyawun halayenki sun zarce a misalta su  ko a suffanta su.


Domin ko farin wata bai haska ba ba wanda bai shaida cewa ke kyakkyawa ce ba.


Ki huta lafiya. 


Daga masoyinki mai tsananin ƙaunarki, IMRAN MUSA JAHUN.

Tuesday, 6 August 2024

Sirrin Yadda Ake Bayyana Soyayya Ga Saurayi Ko Budurwa

Sirrin Yadda Ake Bayyana Soyayya Ga Saurayi Ko Budurwa

Ana isar da saƙon soyayya ta hanyoyi da dama, wasu hanyoyin sun haɗa da wasiƙa da zuwa da kai, su ne hanyoyi mafi dacewa ko mafi ƙarfi da aka fi isar da saƙon soyayya kuma aka fi saurin gasgata cewa lallai wanda ya isar da wannan saƙo na soyayya  ya kamu matuƙa.


Bayyana soyayyar ku
Hoto: Independent


MarubuciImran Musa Jahun


NA MAZA


Zuwa da kai ya fi saƙo, shi ne mutum ya shirya, musamman ya je gidan su wadda ya gani yake so ya tura a kirawo ta, cikin shigar kamala, da nuna halin kawaici.


Idan ta fito ka isar mata da saƙon da kake tafe da shi, cikin kyakkyawan lafazi da tausasa murya, kada ka sanya ƙarya a zancenka ko batun da hankali ba zai ɗauka ba, ƙwaƙwalwa ba za ta amince da shi ba.


Abin da ya kamata ka fara shi ne ka gabatar da kanka a gare ta.


MISALI


Sunana Imran,  ba don komai na zo gare ki ba face sai don na isar miki da saƙon da nake ɗauke da shi a cikin zuciyata.


Wanda wata ƙila ya yi miki daɗi ko akasin hakan.


Na san kin san cewa Allah ta'ala shi ne wanda ya halacci soyayya, sannan ya sanya ta a tsakanin halittunsa, musamman ga jinsin mace da namiji walau Namiji ya kamu da son Mace ko Mace ta kamu da son Namiji.


To ni dai ina daga cikin waɗanda Allah ya yi

halittar so a zuciyarsu.


A wannan lokaci, a sanadin ganin ki, jin sautinki, tarbiyarki, halayenki, musamman tarbiyarki da kuma iliminki.


Saboda waɗannan halaye naki na zo domin na isar miki da saƙon zuciyata zuwa gare ki, zuciyata ta kamu da soyayyar ki, a sakamakon gamsuwa da ta yi da tarbiyarki, kuma ta ga dacewar ƙulla alaƙar  soyayya da ke.


A taƙaice wannan shi ne saƙon da nake ɗauke da shi.


Zan so ki aminta da ni, ki ba ni damar zuwa

gare ki, wata ƙila zuciyar ki ta aminta da ni kamar yadda tawa ta aminta da ke.


Wannan ita ce kawai alfarmar da nake nema a gare ki.


NA MATA


Mace ma tana iya isar da saƙon soyayyar ta kwatankwacin hakan, ta hanyar zuwa wajen wanda ta kamu da soyayyar sa ta isar masa da saƙonta, wata ƙila kunya ta hana ta, don haka sai ta rubuta wasika.



MISALI


Assalamu alaikum, bayan shimfiɗaɗɗiyar sallama wadda addinina ya tanadar, ya harkokin yau da kullum ya lafiyarka?


Bayan haka, kada ka yi mamakin ganin wannan wasiƙa tawa, ko kuma Shaiɗan ya yaudare ka cewa kada ka amince da ni domin na yi tallan kaina a gare ka.


Sam-sam kada ka yarda da hakan, ya zo a

hadisin Manzon Allah ( S. A. W) cewa a zamaninsa mata suna zuwa ga maza suna neman amincewar su domin su yi aure, don haka neman soyayyar namiji a wajen mace ba rashin aji ba ne, ko zubar da kima.


Wannan shi ne cikakken aji da kyautatawa, domin mun yi koyi ga bayin Allah na gari.


Sunana Khadijah, wataƙila ka san ni, wata

ƙila kuma ba ka san ni ba.


A wata rana ina tafiya na haɗu da kai a hanya, cikin ikon Allah sai na ji na kamu da soyayyarka sakamakon ganin tsananin kamalarka, ilimi, hankalinka, ga tsafta.


Zuciyata ta aminta da kai, ta fara azabtar da

gangar jikina.


Lallai ina buƙatar agaji daga gare ka, don haka zan so ka ziyarce ni.


Zan ci gaba daga inda na tsaya a mako mai zuwa.