Showing posts sorted by relevance for query Bello Ado Hussaini. Sort by date Show all posts
Showing posts sorted by relevance for query Bello Ado Hussaini. Sort by date Show all posts

Saturday, 15 February 2025

Yadda Sana'o'in Da Aka Raina Za Su Taimake Ku

Yadda Sana'o'in Da Aka Raina Za Su Taimake Ku

Duk wanda ka gani a wani mataki na nasara, akwai matakin da ya fara wanda ba abun burgewa ba ne.


Yadda Sana'o'in Da Aka Raina Za Su Taimake Ku
Hoto: Prostock-Studio/Getty Images

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Sai dai wannan matakin nasa, wanda mai yiwuwa shi ma wasu masu ƙarancin tunani, sun raina matsayin sa a wancan lokaci, shi ne sanadiyyar samun ɗaukakar sa a yau.


Matasa da dama suna ƙin shiga wasu sana'o'i saboda al'umma ta raina masu wannan sana'ar ba tare da wani dalili ba.


Kuma da yawan irin waɗannan sana'o'in za ka tarar abin da ake samu cikinsu, ya fi na mai matsakaicin albashi.


Wasu kuma sukan ɓoye irin sana'ar da suke gabatarwa, saboda gudun raini ko kallon wulaƙanci.


Babbar illar hakan shi ne, ba za ka sami damar ba wa sana'ar taka irin kulawar da ya kamata ba, tunda a ɓoye kake yin ta.


Abin da ya kamata ka sani shi ne, maula da roƙo da zama cikin talauci, su ne abin jin kunya, amma ba ƙaramar sana'a ba.


Alh. Mustapha Ado mai kamfanin AMMASCO OIL, ya fara da siyar da baƙin mai a galan, yau shi ne mai kamfanin Lubricant ɗan ƙasa mafi girma a Nigeria.


Alh Auwalu Abdullahi Rano, A.A Rano, ya fara siyar da kalanzir a garewani (Drum) abin da ake kira da Ɓunɓurutu/Bunburutu, yau kamfanin sa na A.A Rano Nig Ltd yana cikin kamfanonin da suke ɗaukar Crude Oil a Nigeria, baya ga gidajen siyar da fetur sama da 120, da kuma motocin ɗaukar mai sama da 600.


Kai kanka da kake karanta wannan rubutun, ba za ka rasa wasu misalai da suka faru da wasu da ka sani ba, waɗanda su ma an raina sana'ar da suke yi a baya, kuma yau sun zama abin sha'awa da kwatance a cikin al'umma.


Kowacce irin sana'a kake yi, matuƙar halal ce, ka gabatar da abar ka cikin alfahari da godewa Allah.


Elon musk ya ce "Kada ka ji kunyar sana'ar da kake yi komai ƙanƙantar ta. Kada ka sauya manufar neman ka, saboda wani yana kallon ka a maƙasƙanci.".


Kada ka bari wani sakarai ya hana ka gina rayuwar ka, saboda tasa rashin fahimtar da rayuwa.

Sunday, 26 January 2025

Hanyoyi 3 Na Samun Walwalar Zuciya

Hanyoyi 3 Na Samun Walwalar Zuciya

Idan kana fama da damuwa ko rashin walwala a zuciyar ka, ka yi abubuwan nan guda 3.


Hanyoyi 3 Na Samun Walwalar Zuciya
Hoto: Dilok Klaisataporn

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


1. Idan kana da 'yan uwa ko aboki na ƙwarai a wani gari daban, ka kai masa ziyara.


Ma'ana dai ka yi tafiya yadda za ka canja muhalli na wani lokaci.


2. Idan akwai wani abu da ka sa a gaba, kuma ya gagara samuwa, ka watsar da wannan buƙatar, ka haƙura da ita.


Ka kuma yadda ba kowacce buƙata ce take samuwa ba.


Idan kana da hali na wasu 'yan kuɗaɗe, ko kuma wani abu mai amfani, ka farantawa wani rai, da wata kyauta mai ban mamaki.


Insha Allah waɗannan matakai idan ka bi ɗaya daga cikinsu, ko duka ukun, za ka samu sauƙi da maslaha a zuciyar ka.


Allah ya magance mana dukkan damuwar mu, ya kawo mana sauƙi da rangwame Amin.

Wednesday, 1 January 2025

Abubuwa 11 Da Za Ku Fara Yi A Farkon Sabuwar Shekara

Abubuwa 11 Da Za Ku Fara Yi A Farkon Sabuwar Shekara

1. Mu yi nazarin 2024, nasarorin da muka samu, da kurakuran da muka yi.


2. Mu mayar da hankali sosai wajen fahimtar kurakuren da muka tafka, da nufin gano musabbabin su, da yadda za mu kaucewa maimaita su a 2025.


Abubuwa 11 Da Za Ku Fara Yi A Farkon Sabuwar Shekara
Hoto: Good housekeeping 

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


3. Mu yi duba sosai akan abubuwan da suka fi cinye mana lokaci, mu ware waɗanda ba sa amfanar da mu, domin maye gurbin su da ayyukan da suke tallafar rayuwar mu.


4. Mu yi nazarin alaƙar mu da jama'a da nufin ƙara kusantar mutane na ƙwarai musamman waɗanda za mu koyi wani abu daga gare su (Mentors). Mu zare jikin mu daga mutanen da za su iya gurɓata rayuwar mu ko daƙile ci-gaban mu.


5. Ga wanda iyayensa suke raye, mu ƙara kusantar su tare da ƙoƙarin ba su farin ciki, hakan babban dafa'i ne. Kuma zai ƙarawa rayuwar mu albarka.


6. Sakamakon canjin rayuwa da aka samu, dole ne mu binciki yanayin samun kuɗin mu, tare da duba hanyoyin da za mu inganta neman mu, ko ƙara wasu hanyoyin samun kuɗin shiga.


7. Dole ne mu yi watsi da ɗabi'ar nuna isa da ƙasaita mara dalili, mu daina raina kowacce sana'a, matsawar za ta kawo kuɗi na halak.


8. Mu mayar da hankalin mu kan ƙanana da matsakaitan sana'oi waɗanda al'umma ta fi buƙata, akwai sirri da kuɗi mai yawa ga wanda ya fahimci alfanun ƙananan sana'o'i na gama gari.


9. Wajibi ne kowa ya ƙirƙiri asusu na ajiya, ya kuma tabbatar yana ɓoye wani abu komai ƙanƙantar samun sa, saboda ɓacin rana da larurori na bagatatan.


10. Kada mu ji kunyar tattauna matsalolin mu da waɗanda suka dace domin neman shawara ko shiriya (Guidance) don fita ko kaucewa matsalolin da suka dame mu.


11. Mu dinga samun lokacin nishaɗi muna jingine wasu matsalolin ko damuwa domin inganta lafiyar ƙwaƙwalen mu da samawa zuciyoyin mu sauƙi.

Monday, 28 April 2025

Mutane Nau'i 3 Ne A Rayuwa

Mutane Nau'i 3 Ne A Rayuwa

Mutane iri 3 ne, akwai masu ƙaunar hikima, da masu ƙaunar daraja, da masu ƙaunar riba. Idan kana cikin na 3, za kai asarar biyun. Idan kana cikin na 1 za ka samu 2.


Mutane nau'i 3 ne a rayuwa
Hoto: People Images/iStock photo

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Plato ya ce;


1. Wasu mutane suna ƙaunar hikima wato Wisdom. Duk abin da za su yi suna neman iliminsa, tare da fahimtar dukkan abubuwan da ke kewaye da shi.


Suna yi wa rayuwa kallo na fahimta da neman dalili tare da hasashen sakamakon kowanne aiki.


2. Wasu mutanen kuma suna neman daraja da mutunci, wato Honor. Komai za su yi wannan shi ne ma'aunin su, cewa hakan zai sa su samu daraja da mutuntawa idan sun aikata abin da suke son aikatawa.


Sai dai irin waɗannan mutanen a wani lokaci, za su iya aikata wani abu wanda ba hikima a cikinsa, matsawar mutane za su girmama su idan sun yi hakan.


3. Su ne masu neman riba kawai, wato Profits. Duk abin da za su yi riba ce a gaban su, ma'ana dukiya ko wani amfani na duniya.


Irin waɗannan mutane babu ruwansu da hikimomin rayuwa, ballantana maganar mutunci ko kuma a gan su da daraja.


Idan har za su samu kuɗi, za su iya yin komai ba komai.


FA'IDA


Idan ka kasance a cikin mutane masu ƙaunar riba ko dukiya kawai, tabbas za ka rasa hikima da daraja.


Za ka iya samun kuɗin, amma a ƙarshen rayuwa, za ka gane ka yi asara babba, domin ka siyar da kanka ne, ka karɓi abin da zai ƙare ko ya zama mara amfani wata rana.


Amma idan ka zama mai hikima da bin rayuwa cikin tsari, tare da fahimtar dalilai da hasashen sakamakon ɗabi'un ka da ayyukan ka, tabbas za ka samu riba, ta kuɗi da kuma abubuwa masu amfani a rayuwa.


Hakazalika za ka samu daraja da mutunci a tsakanin al'umma, domin ɗabi'un ka da ayyukan ka, za su dinga nuna wani mutum mai cikakken hankali da hangen nesa, tare da kiyaye doka da sunnar rayuwa.


Allah ya sa mu dace Amin.

Saturday, 25 October 2025

Sirrika 5 Da Masu Kudi Da Kwararru Ba Sa Bayyanawa

Sirrika 5 Da Masu Kudi Da Kwararru Ba Sa Bayyanawa

Babban abin da yakamata mu fara la'akari da shi shi ne, yawan jari ko kalar sana'a ba shi zai tara maka kuɗi ba. Da yawan mutane suna gabatar da wani aiki ko sana'a, amma kuma ba sa samun irin kuɗaɗen da suke buƙata na rayuwa.


Sirrika 5 Da Masu Kuɗi Da Kwararru Ba Sa Bayyanawa 
Hoto: Albert shakirov/Dreams time

Marubuci:- Bello Ado Hussaini



To yaya kuma ga wanda zai fara sana'ar yanzu, har yake tsammanin da zarar ya fara sai kuɗi su yi ta shigowa?


Duk wanda ya gina sana'a ko kasuwanci, ya san irin ƙalubalen da ya fuskanta, kuma idan kasuwancin nasa ya tsaya yana kawo riba, ya san hanyoyin da ya bi, da kuma wasu dabaru da ya riƙe, a matsayin sirrin neman sa.


Sai dai bisa ɗabi'ar mutanen mu, da wuya mutum ya gaya ma irin dabarun nasa, musamman idan ya zama sana'ar ku iri ɗaya ce, ko kuma kasuwa ɗaya kuke ci.


Masu kuɗi da waɗanda suka samu nasara a kasuwanci da sana'a, sun fahimci cewa, babu wani wanda yake son rabuwa da kuɗinsa haka kawai.


Sai dai akwai wasu buƙatu da domin su ma yake tara kuɗaɗen sa, kuma a shirye yake ya biya kuɗi domin biya masa waɗannan buƙatu.


Masu kuɗi sun gane cewa, zuba kuɗin su a irin waɗannan buƙatu na al'umma, ko kuma samar da sana'a wacce za ta magance matsalolin waɗanda suke da kuɗin biya, hanya ce miƙaƙƙiya ta gina arziki.


Sun gane cewa akwai buƙatun da dole a zo neman su, kuma da zarar ka shirya yadda za ka magance waɗannan buƙatu, mutane za su yi ta layi suna biyan ka kuɗade, domin warware musu damuwarsu, ko kuma buƙatar su.


Abin da yakamata mai sana'a ko kasuwanci ya fahimta shi ne, wacce irin matsala ko buƙata yake iya warwarewa a cikin aikinsa, saɓanin abokanan kasuwancin sa.


Akwai abubuwa da yawa da za'a iya duba zuwa gare su, amma bari mu kawo kaɗan daga ciki;


1. ƘARANCI


Wannan yana nufin wani abu na buƙatar rayuwa ya yi ƙaranci ko wahala, kai kuma sai ka nemo shi duk inda yake, ko kuma ka samar da shi.


Hakan zai zama dole mutane su biya ka ladar ka, domin ka samar da abin da suke buƙata, yayin ƙaranci.


2. LOKACI


Mutane suna da buƙatu, amma a mafi yawa, buƙatun nasu suna da lokaci.


Matsawar ba za ka iya biya musu buƙatunsu akan lokacin da suke buƙata ba, tabbas za su rabu da kai da kayan ka, ka yi ta hamma ba ciniki.


Wannan ce tasa yanzu da yawa, za ka ga ana yawan tallata kaya, tare da cewa za mu iya kawo maka kayan inda kake, kuma sai ka gani sannan ka biya.


Akwai kuma abubuwan da suke da kaka, wato ƙayyyadadden lokaci, duk wanda ya kawo kayan sanyi cikin tsananin zafi, ya san sai dai ya kai su ma'ajiya.


3. FARASHI


Kusan duk abin da mutum zai saya, kafin ya zo kasuwa ya ƙulla a zuciyar sa farashin da zai iya biya.


Saɓanin wannan zai iya fasa buƙatar, ba don ba shi da kuɗin ba, sai dai buƙatar ba ta kai wannan farashin ba a gurin sa.

Wajibi ne ka warware matsala a farashin da masu buƙata za su iya biya.


Idan farashin ka ya zarta waɗanda kake tare da su, ya zama wajibi ka nemi sabbin abokan hulɗa. 


Wannan shi zai kai mu ga mataki na gaba a ƙasa.


4. MUHALLI


Wannan kamar yadda na zayyana a sama yana da alaka da irin matsalar da za ka warware, su wa za ka warwarewa, kuma a wane farashi.


5. GAMSARWA


Kamar yadda kowa ya sani, duk wanda zai rabu da kuɗinsa, so yake kuma ya rabu da matsalar da ta sa shi kashe kuɗin.


Don haka dole ne ka samar masa da abin da yake buƙata, har ya gamsu cewa biyan ka da ya yi bai yi kuskure ba.


RUFEWA


Wato gaba-ɗaya shi nema, ɗaukar ƙafa ne da kuma ɗaukar dama, abinda ake kira LEVERAGE.


Dole ne kake la'akari da buƙatun al'umma na ƙashin kansu, sai kuma yanayi da wani salo wanda ba kowa ya fahimce shi ba.


Wannan ce tasa za ka ga mutane masu sana'a iri ɗaya, wani lokacin a waje ɗaya, amma wani yana ta bunƙasa, wani kuma sai a hankali kawai.


Masu magana suna cewa, kowa ya ci Zomo, ya ci gudu tukunna.


Allah yasa mu dace Amin.

Monday, 5 May 2025

Darasin Da Ake So Ka Koya A Rayuwar Ka

Darasin Da Ake So Ka Koya A Rayuwar Ka

Idan wata matsala tana yawan faruwa da kai, akwai wani darasi da ka kasa koyo a cikin ta. Misali idan ana yawan cutarka a kasuwanci da ciniki, hakan yana nuna ba ka tantance abokan hulɗar ka, kuma ba ka nazari da bincike kafin ka ƙulla ciniki.


Darasin Da Ake So Ka Koya A Rayuwar Ka
Hoto: Cross walk

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Idan kana yawan samun saɓani da iyalinka ko abokin ka, hakan yana nuna abubuwa guda biyu musamman;


Kodai akwai wata daɓi'a da kake musu cikin mu'amala kuma ba sa jin daɗin ta, kai kuma ka kasa ganewa ka daina.


Ko kuma su suna da wani hali da ka kasa fahimtar yadda za ka mu'amalance su, ko kuma ka yi haƙuri da shi.


Idan kana yawan shiga matsala da jami'an tsaro, hakan na nufin ba ka tantancewa da doka, ko kuma gane iyakokin ta.


Idan kana yawan shiga matsalar kuɗi ko bashi, hakan na nufin ka kasa tsayawa ka tantance samun ka, da kuma irin buƙatun da ya kamata ka yi, da wanda za ka haƙura har matsayin ka ya sauya, samun ka ya ƙaru.


DARASI


Da yawan lokaci mutane kan ɗauka al'amura suna faruwa ne haka kawai, ko kuma rashin sa'a ne ko ƙaddara. Amma fa da yawa akwai abubuwan da muke yi, ko muke barin su, waɗanda ke ba mu irin sakamakon da muke samu.


Don haka idan abubuwan ka suna tafiya daidai, sai ka zage damtse, ka ci-gaba da addu'a.


Idan kuma akasin haka ne, sai ka yi nazarin abubuwan da suke buƙatar sauyi, domin samun sauyin sakamako.


Allah ya sa mu dace Amin.

Monday, 21 April 2025

Hanyoyi 12 Na Zuba Babban Jari Ga Mai Ɗaukar Albashi

Hanyoyi 12 Na Zuba Babban Jari Ga Mai Ɗaukar Albashi

Hanyoyi 12 na zuba jari ga mai aikin albashi, ko kuma mai son ƙarin kuɗin shiga daga gefe. Dukkannin waɗannan sana'o'i ana gudanar da su a ƙauyuka da biranen mu. Masu yi kuma suna samun alkhairi.


Hanyoyi 12 Na Zuba Babban Jari Ga Mai Ɗaukar Albashi
Hoto: Entrepreneur

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


1. Gidan haya ko Rumfa


Mutane suna ɗauka sai kana da maƙudan kuɗi sannan za ka shiga harkar gidan haya ko rumfa da sauran su.


Akwai gurare da dama da za ka mallaki gida na ƙasa da miliyan 5, kuma ake biyan ka haya, sannan darajar gidan tana ƙaruwa.


Bayan gida akwai rumfar kasuwa a ƙananun kasuwanni da za ka mallaka a ƙasa da miliyan 1, kuma ita ma a karɓi hayar ta.


Banda ƙananun shago-shago a guraren da ake sana'o'i.


Na ƙarshe akwai gurare da Gwamnati ke bayarwa tamfurare, wanda za ka biya kuɗi kaɗan, ka gyara kuma ka ba da shi haya.


2. Hayar kayan amfani


Akwai abubuwan amfani na yau da kullum, kamar kayan taron biki ko na siyasa. Irinsu kujeru da tebura da tantuna da kayan sauti. 


Na biyu akwai kayan gini kamar tsani (ladder) da sukafur (Scaffold) da wilbaro da shebur da kayan haƙa da sauran kayan Engineering.


Duka waɗannan kana iya samar da su ka ɗauki ma'aikaci wanda zai tafiyar da harkar.


Akwai arziki mai yawa a ciki, idan ka samu guri mai kyau, da kaya masu inganci.


3. Kiwon dabbobi na nama


Musamman kiwon shanu idan ka fahimce shi, kuma kana da guri da mai kulawa, hanya ce mai kyau ta samun kuɗaɗe baya ga sana'ar ka ko aikin da kake gabatarwa na kullum.


Kawai idan za ka fara ka tuntuɓi ƙwararru da wanda suka jima a harkar.


4. Lambun kayan marmari


Wannan wani nau'i ne na noma a sauƙaƙe, inda za ka samu gona ko fili, ka dasa 'ya'yan itace masu gajeren zango (Hybrid).


Irin waɗannan kayan marmari sukan ba da 'ya'ya sau biyu a shekara, kuma sukan zo da daraja.


Misalin irin su shi ne kamar gajeriyar gwanda (Dwarf papaya) da lemon tsami da sauran su.


A waje ɗaya akwai noman kankana da kokumba, duka ba su ɗaukar lokaci, kuma mai aikin albashi musamman zai iya gabatar da su a kwanakin ƙarshen mako, tare da abokin kulawa.


5. Harkar Gwangwan


Harkar Gwangwan ana yin ta ta wucin gadi, misali ka ƙulla alaƙa da masu samun kaya, wanda a mafi yawan lokaci ba kowa ke da wadataccen jari ba. 


Duk lokacin da aka samu kaya sai ka siya, ka samu sito ka ajiye.


Idan aka samu mai son irin wannan kayan za su neme ka, kuma ana samun alkhairi.


6. Sufuri


Wannan ba ta buƙatar fassara, akwai irinsu ƙurƙura ko keke nafef da kanta kanta da sauransu daidai jarin ka.


Abin da harkar sufuri take buƙata kawai abokan neman arziki na ƙwarai, da kuma tsari mai kyau.


7. Hannun Jari


Wannan yana buƙatar masana harkar wato Brokers, tare da fahimtar yadda hada-hadar hannun jari take.


Mafi muhimmanci a ciki shi ne, mai hada-hadar hannun jari, baya jiran sai ƙarshen shekara kamfani ta biya Dividend.


Yana bibiya ne idan ya sauka ya siya, idan ya hau kuma ya siyar kamar Forex Trading.


8. POS


Wannan ma ba shi buƙatar fassara. Sai dai da yake ba kai z aka zauna ba, akwai buƙatar ka fahimci harkar, kuma ya zamana kai kake ganin irin hada-hada (Transaction) din da ake yi ta wayarka, ma'ana alerts. 


Ta haka za ka riƙa sanin cinikin da aka yi a kullum, da kuma ribar da aka samu.


9. Kayan sanyi


Shi ma wannan a fayyace yake, magana ce ta ka san me ka siyo, kuma me aka siyar.


Sai wuri na jama'a mai kyau da tsari.


Sannan ka samu abokin neman arziki mai amana, ku yi tarayya.


10. Saye domin riba


Wannan wata hanya ce ta siyawa masu buƙatar kayayyaki kowanne iri ne, daga baya su biya ka, kamar yadda bankuna ke yi.


Idan mutum na son wayar hannu misali, sai ka siya masa, kuma ka ɗora riba.


Shi kuma ya biya ka daga baya.


Irin wannan ya haɗa da kayan amfanin gida kamar TV da Fridge da kayan sawa da na gini kamar siminti da kwanon rufi da sauransu.


Shi ma yana buƙatar shawarar ƙwararru da tsari kafin farawa.


11. Sayen kayayyaki


Wannan ya ƙunshi kamar kayan sana'a wanda za a siya wa mutum ya dinga amfani da shi wajen sana'ar sa, yana biya a hankali.


Misali kamar keken ɗinki (Sewing machine) ko Generator ko Mixer ta gidan burodi da sauransu.


12. Sayen kayan da aka tallata


Wannan ma wata hanya ce ta zuba jari da juya kuɗi domin riba.


Yadda ake yin ta kamar Gwangwan ne, sai dai ba ta da gefe.


Duk wani abu na amfani, mai rai ko mara rai, idan ka ji ana neman mai siya, kana iya biya, bayan ka binciki darajarsa a kasuwa, da kuma yanayin buƙatar sa ga jama'a.


Lokacin da farashi ya yi maka daidai ka siyar.


Allah ya sa mu dace.

Saturday, 21 December 2024

Yadda Za Ku Samu Sauki A Lokacin Tsananin Rayuwa

Yadda Za Ku Samu Sauki A Lokacin Tsananin Rayuwa

A yanzu dai muna iya cewa an fara sabawa da tattalin arzikin Tinubu, na janye tallafi daga abubuwan rayuwa na yau da kullum.


Bugu da ƙari kuma, ga sabuwar Naira mara karfin faɗa aji a kasuwa.


Sai dai da yawan mutane haƙuri kawai suka yi, tare da dangana cikin abin da Bahaushe ke kira da tsammanin warabbuka, ko kuma gamu ga Allah bawan sarki ya rasa doki.


Yadda Za Ku Samu Sauki A Lokacin Tsananin Rayuwa
Hoto: Martin-dm/Getty Images

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Amma fa akwai wasu abubuwa guda uku, waɗanda ka iya taimakon mutum wajen samun sauƙi, ko ma fita daga matsalar baki ɗayanta ta, tare da samun sabbin hanyoyin shigar kuɗi.


Waɗannan hanyoyi su ne kamar haka;


 Daidaitawa 


Wannan yana nufin karɓar yanayin da aka samu kai a ciki, tare da yarda cewa rayuwa da ma juyawa take.


Muhimmancin karɓar yanayi shi ne, yana ba da nutsuwar zuciya, yadda mutum zai tsai da hankalin sa, wajen neman mafita.


Dalili idan ka gaza karɓar yanayin da ka samu kanka, to za ka shiga ruɗani har ka faɗa wata rigimar kuma daban.


Rinjaye a kan matsi


Wannan shi ake kira da ɗaukar dama. Wato duk wani yanayi komai muninsa yana zuwa da wasu damarmaki a cikinsa.


Lokacin da Boko Haram ta ɗaiɗaita Maiduguri, sai ƙungiyoyin agaji suka samu dama wadda ba su taɓa samu ba, wajen karɓar kuɗaɗen agaji da kuma ayyukan jin ƙai.


Hakan kuma na nufin baya ga aikin lada, annobar ta ba su aikin yi da samun alawus mai kauri ba Dollar.


A baya bayan nan, lokacin da gwamnati ta rufe kasuwanni, bayan zanga-zangar matsin tattalin arziki, sai 'yan kasuwa suka yi amfani da wannan damar wajen ƙarin farashin kayayyaki.


Wannan kaɗan ne daga misalan ɗaukar dama cikin lokuta ko yanayi na matsi da damuwa.


Kada kuma wani ya ce ana koyawa mutane rashin tausayi, a'a haka sunnar rayuwa take, musamman ta kasuwanci, ko ka yi ko a yi maka.


Sassauci


Wannan na nufin ka gane cewa idan kiɗa ya sauya, to rawa ma sauyawa take. Ma'ana ka kasance kana bin rayuwa yadda ta zo, maimakon ƙoƙarin tafiyar da ita cikin salo na bai ɗaya, koda kuwa yanayin bai dace da tsohon yanayi ba.


Da yawan waɗanda suka fahimci haka yanzu za ka ga suna tantance inda ya kamata su yi amfani da motocin su, da kuma inda za su je su hau Ɗansahu kamar kowa.


Hatta mutanen da ba su da isasshiyar solar a gida, za ka ga sun samo ƙananun fitulu na solar masu sauƙin kuɗi, maimakon kunna Generator.


Haka zalika wasu ƙananan hanyoyin samun kuɗi waɗanda a baya ba su kulawa da su, yanzu za ka ga ba'a wasa da su.


Sai ka aje girman kai, ka je ka buga ƙaramar harka ta ƙananun kuɗi, ka ɗura a aljihunka.


Waɗannan hanyoyi, idan an bi su za'a samu sauƙin rayuwa, har ma da samun ƙarin kuɗin shiga, nutsuwar zuciya da kuma ci-gaban rayuwa.


Allah ya ba mu dacewa Amin.

Friday, 10 January 2025

Kalaman Karfafa Gwiwa Na Sabuwar Shekara

Kalaman Karfafa Gwiwa Na Sabuwar Shekara

Wuta ita take raba dusar ƙarfe da ƙasa, ta tsarkake shi tare da ƙara masa karfi da daraja. Wuta ita take narka zinare ta raba shi da dukkan datti, har ya zamo mai daraja kuma abun kwalliyya.


Kalaman ƙarfafa gwiwa na sabuwar shekara
Hoto: Rawpixel/Getty Images

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Haka kuma ƙalubalen rayuwa yana inganta ruhin Ɗan Adam, ya saita tunanin sa, ta yadda mutum zai ƙara fahimtar hikimar rayuwa da ma'anarta.


Ma'aiki sallallahu alayhi wasallam cikin Hadithi yake cewa;


"Idan Allah (S.W.T) ya so bawa, sai ya jarrabce shi, idan ya jure kuma ya jajurce, sai ya sami mafita da rabo. Abun da ya biyo baya na ƙaiƙayin zuciya kuma, idan aka yi haƙuri, kankarar zunubi ce ga mumini."


Manufa anan shi ne kada mu karaya a kowanne hali, mu kasance masu fata nagari, tare da kyautata zaton samun sauƙi daga kowanne tsanani, domin bayan dukkan tsanani sauƙi ne yake biyo baya.


Marigayi BASHIR OTHMAN TOFA, cikin talifin sa "TUNANIN KA KAMANNIN KA,, Ya ce "Wahala ita ke matso ƙwazo, shagwaɓa kuma kashe shi take yi."


Jarumi DENZEL WASHINGTON, yana cewa; sauƙi ya fi zama barazana ga ci-gaba sama da tsanani.


"Ease is more threat to progress than hardship".


Ba ma fatan tsanani ga kawunan mu, ko ga 'yan uwan mu, sai dai gaskiyar magana shi ne, ba za mu iya kaucewa ƙalubale ba matuƙar muna raye, sai dai mu yi tanadi, kuma mu yi komai cikin hankali da nazari.


Sannan mu yi haƙuri da rayuwa a kowanne hali da lokaci.


Mu sani tsanani ba ya dawwama, kamar yadda sauƙi da jin daɗi su ma ba su da tabbas.


Mu yi ƙoƙarin samarwa kanmu da kanmu farin ciki yayin yalwa ko rashi, mu ƙaunaci juna, mu yi afuwa da uzuri ga juna.


Tabbas ƙauna da soyayya wani sinadari ne da yake maganin cututtukan zuciya da yawa, ya ba ta salama, ya kuma amintar da makusantan mai ita.


Fatana gare mu duka shi ne mun shiga sabuwar shekara da sabon tunani, da sha'awar koyo da saurare tare da fahimta kafin yanke hukunci akan komai da kuma kowa.


Mu sani kowa da yadda yake kallon rayuwa, kuma tunanin kowa zai iya kasancewa mai amfani a wani lokaci.


Mafi muhimmanci shi ne mu gane lokacin da ake buƙatar komai da sa'adda ake buƙatar kishiyarsa.


Mu mutunta juna da ra'ayin juna.


Mu sani Allah (S.W.T) yana ganin mu a cikin kowanne al'amari, kuma shi ne Mai hukunci, daidai da dacewa a wajensa take.


Allah ya kawo mana ɗauki ya tsayar da zuciyar mu akan imani, ya sa mu kasance masu amfani ga kawunan mu da al'ummar mu.


Kada mu cutar kada a cuce mu.


Allah ya sa mun shiga sabuwar shekara cikin ƙaunar juna da taimakon juna da afuwa ga juna, tare da kare harshen mu daga miyagun kalamai na sukar juna Amin.

Sunday, 5 January 2025

Abubuwa 10 Da Ake So Ku Yi A Sabuwar Shekara Don Samun Ci-gaba

Abubuwa 10 Da Ake So Ku Yi A Sabuwar Shekara Don Samun Ci-gaba

1. Ka yi ƙoƙari ka inganta aljihunka, rayuwa ba kuɗi akwai takaici da wahala.


2. Ka cire tsoro ka jarraba wani sabon abun ko za ka dace.


3. Ka rage dogaro da abokai da 'yan uwa, ba koyaushe za su iya taimakon ka ba.


Abubuwa 10 Da Ake So Ku Yi A Sabuwar Shekara Don Samun Ci-gaba
Hoto: 123RF

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


4. Koda wani ya ɓata maka, ka yi ƙoƙari ka hana kanka yin gaba ko ƙiyayya da shi.


Gaba da ƙiyayya suna hana mutum yin tunani yadda ya kamata, har ya cimma manufarsa.


5. Ka koyi yin afuwa, koda ba za ka sake yarda da mutum ba.


6. Duk mu'amalar da za ka yi, ka yi cikin gaskiya. Allah yana taimakon kasuwanci ko duka aikin da aka yi tsakani da Allah.


7. Kyautata zato yana da muhimmanci, amma kada ka bari ka zama sakarai. 


Ka dinga kulawa da manufar mutanen da kake mu'amala da su.


8. Ka rabu da hassada da ƙyashi, domin ita hassada ɓata lokaci ce, ba ta hana wanda kake yi wa cin nasara.


9. Idan kana son wani abu ka tashi ka nema, fata ba ya kawo sakamako sai aiki.


Idan ba ka gane wani abu ba, ka tambaya domin zato yana shigar da mutum cikin ruɗani.


10. Ka koyi haƙuri ka koyi jira, komai yana da lokacin da Allah ya ajiye masa.


Allah ya sa mun shiga sabuwar shekara a sa'a da imani da lafiya da mutunci da kuɗin kashewa Amin.

Friday, 3 January 2025

Abubuwa 10 Ba Ku Buƙatar Su A Sabuwar Shekara

Abubuwa 10 Ba Ku Buƙatar Su A Sabuwar Shekara

Waɗannan su ne abubuwan da ya kamata ka zubar da su a wannan sabuwar shekarar, kada ka ci-gaba da tafiya da su.


Ga su kamar haka:


1. Rabon ka ba ya tsere maka


Wanda ya tashi tsaye ya nema Allah zai taimake shi ya samu.


Abubuwa 10 Ba Ku Buƙatar Su A Sabuwar Shekara
Hoto: Window would

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Wanda ya kwanta kuma sai abin da hali ya yi. Don haka ka tashi ka nema, kada ka jira lokaci.


2. Shugabanni ba sa son taimakon na ƙasa


A wannan ƙarnin da muke ciki shugabanni musamman irin na Nigeria ba ruwansu da kai, ko ka yi nasara ko akasin haka. Don haka ka tsara rayuwar ka cikin irin damar da kake da ita, ka kuma zage damtse wajen kyautata matsayin ka (Personal Development) ka nemi taimakon Allah (SWT).


3. Ƙoƙarin burge mutane


A mafi yawan lokuta abubuwan da kake yi domin burge jama'a kanka kawai kake burgewa. Wanda kake ba wa sha'awa ba ya buƙatar ka sauya komai game da kanka.


Wanda ba ka burgewa kuma kome ka yi ba za ka burge shi ba.


4. Kuɗi ba komai ba ne


Tabbas ba mu zo duniya domin neman kuɗi ba, sai dai da yawan abubuwan da muke buƙata domin mu rayu cikin mutunci da sanin ya kamata, talauci abokin gabar su ne.


Wadata tana sa mutum ya tsare mutuncin sa, ya kiyaye cin haram.


Wani lokaci hatta ibada ta fi tsayawa idan kana cikin hayyacin ka.


Don haka ka dage ka nemi kuɗi.


5. Raina sana'a


Har yanzu akwai waɗanda suke ganin sun fi ƙarfin wata sana'a saboda wasu dalilai nasu, amma fa ba su wuce maula da roƙo ba.


To ka sani yadda Nigeria ta ɗauki zafi yanzu, mai taimakon a baya, shi ma yanzu taimakon yake nema.


Don haka ka kama sana'a komai ƙanƙantar ta.


6. Zage-zage da shirme a shafukan sada zumunta 


Ka sani duk abin da kake yi a shafukan sada zumunta mutane suna kallon ka, kuma da yawa ba za su yi maka magana ba amma duk ranar da mu'amala ta haɗa ka da su, za ka karɓi sakamakon ayyukan ka a hannun su. 


Gwargwadon yadda ka nuna waye kai. Don haka ka saisaita mu'amalar ka a cikin wannan sabuwar shekara.


7. Wasa da alaƙa da raina mutane


Duk wanda ka haɗu da shi a rayuwa, ba ka san hikimar Ubangiji game da hakan ba.


Ta yiwu shi ne mai taimakon ka a rayuwa, kuma komai rashin matsayin sa.


Da yawan lokaci za ka raina matsayin mutum, kuma akwai sirri a tare da shi ko kuma ka kalli wani abu a tare da mutum, amma holoƙo ne, shi ma ta kansa yake yi.


Don haka ka girmama kowa, ko domin Allah (S.W.T) ya yi umarni da hakan.


7. Mummunan zato da yaɗa sharri


Kusan yana neman zama al'ada da zarar wani abu mara daɗi ya faru, sai ya zama abin yayi.


Kowa ya yi ta yaɗawa ba tare da tabbacin gaskiyar al'amarin ba.


Irin wannan ɗabi'a tana cutar da mai yin ta ba tare da ya sani ba.


Domin zaton ka yana shafar tunanin ka, kamar yadda tunanin ka yake zama aikin ka, da kuma makomar ka.


9. Kwaikwayo da yayi


Duk abin da ka ga wani yana yi ba ka san manufar sa akai ba.


Idan ka shiga kwaikwaya ba tare da ilimin abin ba, kana iya samun kanka a inda ba ka so.


Don haka kana iya kwaikwayo, amma inda ya dace da manufar ka.


10. Wasa da addu'a


Duk abin da ka saka a gaba, kada ka yi wasa da addu'a. Akwai abin da idon ka da hankalin ka suke gani, akwai abin da hangen ka ba zai je kansa ba.


Addu'a ce kaɗai za ta magance maka abin da ya fi ƙarfin tunani da hankalin ka.

Sunday, 1 December 2024

Dalilai 3 Da Su Hana Ka Zama Mai Kudi Duk Da Kana Kasuwanci

Dalilai 3 Da Su Hana Ka Zama Mai Kudi Duk Da Kana Kasuwanci

Da yawan mutane suna yi wa kansu wasu tambayoyi a zuciyar su kamar haka;


Yaushe zan yi kuɗi ne?


Me ya hana ni yin kuɗi?


Anya kuwa zan yi kuɗi?


Abinda da yawan mu ba mu fahimta ba shi ne, samun kuɗi fa ko rufin asiri sai ka shirya hakan tun daga zuciyar ka.


Dalilai 3 Da Su Hana Ka Zama Mai Kuɗi Duk Da Kana Kasuwanci
Hoto: Telecoms

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Wasu za su ce wannan maganar ai ba Tauhidi, kuɗi ƙaddara ce kawai.


Eh komai muƙaddari ne daga Allah (S.W.T), shi ne mai bayarwa kuma mai hanawa amma duk mai shekaru irin namu, daga 40 zuwa sama, idan ya tsaida hankalin sa, zai yadda cewa cikin shekarun da ya yi a baya, Allah (SWT) ya ba shi wata dama komai ƙanƙantar ta, yadda zai yi kuɗi ko ya samu rufin asiri.


Sai dai kash ya aikata ɗaya daga cikin waɗannan kurakurai guda 3, ko ma dukansu, shiyasa har yanzu yake cikin talauci.


MENE NE WAƊANNAN KURAKURAI GUDA UKUN?


1. Kana yin sana'a, amma a cikin zuciyar ka ba ka son ta, kana yin ta ne a matsayin ta wucin gadi (temporary) kafin wata sana'ar da kake hange ta samu.


Illar hakan shi ne, wannan sana'ar ba za ka taɓa yi mata tsari ba, ballantana ka gina wani abin kirki a cikin ta, domin hankalin ka ba ya kanta, kawai dai kana yi ne, ba sha'awa ba dogon buri.


Don haka ba za ka godewa abinda kake samu daga gare ta ba, har ka yi tunanin tattali da bunƙasa ta.


2. Kana sana'a kuma kana sha'awar ta, amma ka raina abinda take ba ka, har kana ganin cewa, wannan sana'ar ina mutum za shi da ita? Ɗan wannan abin da ake samu wane tanadi mutum zai yi, har ya gina wani abin arziki amma fa a daidai lokacin da kake yi wa sana'ar taka kallon ƙarama mara riba, 'yar fulani mai siyar da fura da nono a kasuwar sabon gari, ta tara miliyan shida (6 million) ta biya kuɗin Aikin Hajji da wannan cinikin furar, ba wai saniya ta siyar ba.


Ka ga ashe ba ƙanƙantar abin da kake samu ba ne, tsari ne da juriya da tarbiyya, wato horarwa.


3. Kana yin sana'a, kuma kana samun kuɗi gwargwadon hali, wanda sun isheka buƙatun rayuwa.


Sai dai ba ka da linzami wajen kashe kuɗi da buƙatu marasa dalili.


Duk buƙatar da ta zo gaban ka yin ta kake yi. Ka ɗorawa kanka wani ma'auni wato tsayayye, kai lallai sai ka rayu haka, ba za ka jira lokaci ba.


Kai ne canja waya sabuwar shigowa, duk bikin da aka gayyace ka sai ka sa sabuwar riga.


Ko yaya wani abu ya karci motar ka ko babur ɗinka, sai ka je gareji.


Duk sati sai ka je Carwash an yi maka General.


Da yawan mu a wannan ajin muke, shiyasa kuɗin mu bai taru ba.


Kai kanka ka zauna ka yi lissafi idan za ka iya, a cikin 2024 ɗin nan, duk da azabar Baba Bala Blu, nawa ka samu daga Janairu zuwa Nuwamba? Wallahi za ka tarar kuɗaɗe ne masu yawa.


Amma ka gayawa ranka ai ƙasa ta rikice, ya za'ayi ma mutum ya tara kuɗi? Don haka ka cinye kuɗin ka ba tare da ka lura ba.


Mafita ita ce, komai ƙanƙantar abin da kake samu, za ka iya yin tattali ka tara don gobe.


Za ka iya haƙura da wasu buƙatun na dole, ka jure wahala, domin gobe ka samu farin ciki da arziki mai ɗorewa, maimakon yau akwai, gobe babu.


Mutum nawa ne suke ƙin cin abinci a kasuwa sai kame-kame, kuma da kuɗi a jikinsu, sai sun dawo gida.


Mutum nawa ne suka ajiye abun hawan su, su hau keke napep, kuma sun fika samun kuɗi.


Mutum nawa ne suke riƙe waya ɗaya shekaru 3 ba canji, kuma sun fika samun kuɗi.


Amsar ita ce, duk abin da kake son cimma a rayuwa, sai ka yi sadaukarwa.


Sai ka jure wata wahala domin ka ji wani daɗin.


Sai ka yi tanadin yau domin gobe.


Allah ya sa mu gane wannan karatun, har da ni don ni ma so nake na yi maza na yi kuɗin nan kafin Nigeria ta gama rikicewa.


Idan har kuna jin daɗin maƙalolin shafin nan namu, to ku hanzarta sanar da dukkan abokan ku ko ƙawayen ku da dukkan waɗanda ku sani, ku gaya musu adireshin shafin nan namu domin su ma su shigo cikin shafin su dinga amfana da shi kamar yadda ku ma kuke yi a kullum a kyauta.

Saturday, 22 February 2025

Babban Sirrin Kasuwa A Yau

Babban Sirrin Kasuwa A Yau

Babban sirrin kasuwa a 2025 shi ne samar da kayayyaki masu sauƙin kuɗi daga abin da muke samarwa a cikin gida. Domestic Market (Production).


Babban Sirrin Kasuwa A Yau
Hoto: Natali_Mis/Getty Images

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Bincike ya nuna cewa a iya shekarar 2023 kawai, kamfanoni da masu shigo da kaya, sun gaza siyar da kaya na sama da Naira biliyan ɗari uku da hamsin.


Ma'ana ₦350 billion na kaya da ke jibge a sito babu mai siye.


Lissafin kuma ya ci-gaba har cikin shekarar 2024.


Hakan na nuni da sukurkucewar ƙarfin aljihun al'umma, wajen iya sayen kayan amfanin yau da kullum, da na buƙatar rayuwa, wato Purchasing Power.


Waɗannan alƙaluma suna tabbatar da cewa, masu amfani da kaya (Consumers) dole sun haƙura da wasu kayayyakin, sannan kuma sun nemi musayar wasu masu sauƙin kuɗi, Alternative consumer goods.


Wannan tabbas matsala ce ga manyan kanfanoni, a waje ɗaya kuma zai iya zama wata dama (Opportunity) ga ƙananan kamfanoni da masu sana'a.


Tambayar itace; Ta yaya za mu iya cin gajiyar wannan ƙalubale?


Dole ne masu ƙananan masana'antu da 'yan kasuwa su ɗauki damar da take cikin abubuwa guda 3, abin da ake kira Leveraging.


Ma'ana su shigar da waɗannan abubuwa cikin sabon fasali a ayyukan su, yadda kayan da suke samarwa, za su ƙara inganci, tare da rage kuɗaɗen da suke kashewa wajen samar da kayan, da kuma yin amfani da taƙaitaccen lokaci a hannu guda.


Waɗannan abubuwa su ne;


Fasaha


Dole ne masu son cin wannan gajiya, su yi amfani da fasahar zamani, wajen inganta ayyukan su.


Wannan ya haɗa da kayan aiki na zamani masu saukin kuɗi, Machine and Tools, da kuma fasahar kwaikwayo wato Artificial intelligence.


Makamashi


Kowa yasan tasirin makamashi wajen tafiyar da ayyukan masana'antu da masu sana'ar hannu.


Haka kuma kowa na sane da yadda farashin makamashin da aka saba amfani da shi (Conventional Energy) yake tashi sama, daga farashin wutar lantarki zuwa na man Diesal da fetur da iskar gas.


Dole ne mu samo wata hanya mafi sauƙi da arha, kamar Renewable energy irinsu hasken rana (Solar) Sharar gona da ta kamfanonin sinadarai, inda za'a ƙona kamar buntun shinkafa, ƙonannen baƙin mai, domin samar da tururi zuwa makamashi (Black furnace) cikin sauƙi.


Hanya


Ya zama wajibi mu samo hanyoyi masu nagarta, na tafiyar da ayyukan mu cikin tsari da gwaninta da ilimi, yadda za mu horar da ma'aikatan mu, da mu kanmu wajen gudanarwa, yadda za mu taƙaita ta'adi (Waste) da ɓata lokaci (Time management).


Hakan zai haɓaka yawan kayan da muke samarwa, cikin gajeren lokaci, da kuma ingancin kayan.


Wannan kuma shi zai ba wa masu dillancin kaya (Whole sellers) ƙwarin gwiwa, cewa za su iya dogara da kayan gida ba tare da yankewa ba, wato Supply Chain Management.


Ƙaruwar abokan hulɗa kuma, zai iya magance matsalar ƙarancin jari.


Dalili idan ka inganta ayyukan ka, za ka samu waɗanda za su saka order, ma'ana su zuba kuɗi su jira kaya.


Hakan zai ba ka damar yin amfani da dabarar nan ta (OPM). Other people's money.

Sunday, 8 December 2024

Dalilai 3 Da Su Hana Ka Cimma Nasara

Dalilai 3 Da Su Hana Ka Cimma Nasara

Dalilai uku da suke zama tarnaƙi ga samun nasara a rayuwa.


Ga su kamar haka:


1. KARAYAR ZUCIYA DA HANGEN GAZAWA


Wani lokacin mutum da kansa ya kan karya zuciyarsa da jin cewa wani abu ba mai yiwuwa ba ne a wajensa, ba kuma tare da ya gwada ba.


Dalilai 3 Da Su Hana Ka Cimma Nasara
Hoto: Freepik

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Wani kuma wasu ne za su nuna masa cewa abu kaza ya fi ƙarfin sa. Daga nan sai ya ɗauka koda ya gwada ɗin ba zai yi nasara ba.


Abin da bai gane ba shi ne, da yawan lokaci Ɗan Adam ba ya sanin ƙarfin sa, har sai ya gwada tukunna.


Kada ka karya zuciyar ka akan komai, kuma kada ka saurari wanda ba zai ƙarfafa maka gwiwa ba.


2. LALACI DA NEMAN SAUƘI


Wannan ba ya buƙatar fassara da yawa, domin kowa ya san illar lalaci, sai dai ba kowa ne ya fahimci cewa, neman sauƙi a cikin komai na iya zama tarnaƙi ga ci-gaba ba.


Denzel Washington yana cewa; Sauƙi ya fi zama tarnaki ga ci-gaba sama da tsanani.


"Ease is more threat to progress than Hardships."


Masu hikima kuma suka ce; Tsanani na haifar da jarumta. Ita kuma jarumta tana kawo mafita. Mafita kuma tana kawo sauƙi.


Ka ga kenan idan kana kwance kawai, kana neman sauƙi, ba za ka zama jarumi ba, ballantana ka samo mafita, wadda ita ce ke kawo sauƙi.


3. KWAƊAYIN GIDA DA TSORON SAUYI


Bahaushe yana cewa sabo turken wawa, ma'ana wanda ya kasa barin abin da ya saba da shi, ya kuma karɓi wani yanayi sabo domin ci-gaban sa, to ya yi wauta.


Da yawa mutane ba sa son barin gida ko sauya fasalin rayuwar su, domin samun ci-gaban da suke buƙata.


Hakan kuma ba ƙaramin tarnaƙi ba ne ga samun nasara, dole wani lokacin sai ka bar gida, ko sauya fasalin rayuwar ka, kafin cimma burin ka.


Allah yasa mu dace Amin.

Wednesday, 8 January 2025

Dalilai 6 Da Su Hana Ka Fita Daga Talauci Da Matsalar Rashin Kuɗi

Dalilai 6 Da Su Hana Ka Fita Daga Talauci Da Matsalar Rashin Kuɗi

1. Rashin lissafi da ƙididdiga


Rashin tsari da fasalin abin da kake samu, da yadda za ka sarrafa shi bisa la'akari da buƙatu na wajibi da wanda ba wajibi ba, zai ci-gaba da jefa ka cikin rashin kuɗi da matsi, ko nawa kake samu.


Dalilai 6 Da Su Hana Ka Fita Daga Talauci Da Matsalar Rashin Kuɗi
Hoto: Poznyakov/Dreams time

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Dole ne kake bibiyar abin da ya shigo aljihunka, da abin da zai fita, da kuma abin da kake saran samu tare da lokacin da wannan samun shi ma zai shigo aljihunka.


NB: Ka yi nazari akan Cashflow Analysis.


2. Yawan cin bashi


Yawan karɓar bashi hanya ce mai sauƙi ta ci-gaba da zama cikin rashin kuɗi da talauci.


Duk lokacin da ka karɓi bashi na kuɗi ko kaya, hakan na nufin ka cinye kuɗaɗen da za ka samu nan gaba, ta yadda ko ka samu kuɗi, biyan bashi za ka yi da su, ga shi kuma buƙatu ba sa ƙarewa matuƙar kana da rai.


Dole ka koyi rayuwa a cikin ɗan samun ka, ka gujewa cin bashi sai ya zama dole.


3. Rashin danne zuciya akan buƙatu


Idan ka kasance duk abin da ka ga kana so sai ka saya matuƙar da kuɗi a jikinka, za ka jima a matsalar kuɗi.


Dole ka koyi danne zuciyar ka, kan wasu buƙatu da ba dole ba, koda kuwa kana da kuɗi.


Financial discipline yana matsayin jigo wajen kaucewa matsalar rashin ƙudi da yaƙar talauci.


4. Rashin tattali da tanadi


Na jima ina magana akan tsimi wato Savings. Rashin tattali ba ƙaramar matsala ba ce wajen yaƙar talauci.


Dole ya zama ka yi wani tanadi na abin da yake zuwa ba tare da zato ko shiri ba, kamar rashin lafiya ko hatsari da sauransu.


5. Rashin neman shawarar ƙwararru


Neman shawara da taimakon ƙwararru akan harkar kuɗi ba wai sai ka zama Ɗangote ba.


Duk wanda yake sana'a ko aiki akwai lokutan da yake buƙatar shawarar ƙwararru.


Idan samun ka ya ƙaru, kana buƙatar shawarar abin da za ka yi da wannan ƙarin da ka samu.


Idan samun ka ya ragu, shi ma kana buƙatar shawarar yadda za ka saisaita al'amura, domin kaucewa faɗawa matsala.


6. Maƙalewa sana'ar da ta ƙi gaba ta ƙi baya


Akwai sana'o'i da suke da wa'adi, akwai ayyukan da su ma ana wuce lokacin yin su.


Misali akwai sana'ar da za ta iya riƙe matashi, amma ba za ta ɗauki nauyin iyali ba.


Haka ma aiki akwai na matashi da na mai ɗaukar nauyi.


Akwai kuma ayyuka ko sana'ar da ba ta dace da kai ba.


Duka wannan na nufin idan ka jarraba abu, kuma ka ɗauki lokaci babu haske, kana buƙatar sauya salo, ko kuma wata sana'a ko aiki daban.


Sai dai wasu sukan maƙale akan abubuwan da suka tabbata cewa ba su da nasara ko nasibi a kansu.


Allah ya ba mu ikon kaucewa waɗannan matsaloli, ya inganta samun mu Amin.

Saturday, 26 April 2025

Dalilin Rashin Cinikin Ka

Dalilin Rashin Cinikin Ka

Na  farko a kasuwancin ka shi ne ka tabbatar ana buƙatar abin da kake kawowa kasuwa. Na biyu ka tantance masu buƙatar da yadda suke son kayan ka.


Dalilin rashin cinikin ka
Hoto: Flickr

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Mutane da yawa suna kukan rashin ciniki, wani lokacin sai a gaya musu wai ba su kaɗai ba ne, ai babu kuɗi a gari.


Amma mafi yawan lokaci kai ne ka kawo abin da kasuwa ba ta buƙata.


Wani lokacin kuma, rashin tantance masu buƙatar kayan ka (Target customers) da yadda za ka same su, shi ne babban dalilin rashin cinikin ka.


Me ya kamata ka yi?


Ka tabbatar akwai buƙatar abin da za ka kawo kasuwa, kuma ka tantance masu buƙatar, da ƙarfin aljihunsu, da kuma yadda za ka same su.


Don haka kana buƙatar ka yi nazari akan abubuwa guda 5;


1. Kaya ko sana'a.


2. Abokan ciniki.


3. Ƙarfin ajihun abokan hulɗa.


4. Wajen kasuwancin.


5. Talla da jan hankali.

Thursday, 30 January 2025

Kyakkyawan Darasi Daga Rayuwar Rarara

Kyakkyawan Darasi Daga Rayuwar Rarara

Mutane da yawa suna samun nasara a abubuwan da kake ɗauka shirme ne. A lokacin da mawaƙi Dauda Kahutu Rarara ya ce, ya ba wa shugaban Niger Tchiani kwana 20 ya sauka daga kujerarsa, mutane da yawa sun ɗauki hakan a matsayin tsabar jahilci da rashin hankali.


Kyakkyawan Darasi Daga Rayuwar Rarara
Hoto: Real Dauda Kahutu Rarara/Facebook

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


Kuma a zahiri faɗin hakan zai iya zama wauta da rashin hankali.


Amma ni da na ji wannan shurbucin na Rarara, ban ɗauka da gaske yake ba.


Haka kuma na yi imani cewa shi ma Rarara, ba ya tsammanin wai shugaba Tchiani zai mayar da shugaba Bazoum, saboda tsoron waƙar mawaƙin na siyasa.


Amma abin da ya kamata mutane su yi nazari akai shi ne, mene ne aikin Rarara?


Kuma yaya yake tafiyar da al'amuran sa, har yake samun irin kuɗaɗen da yake samu?


Babban aikin Rarara shi ne waƙoƙin siyasa, waɗanda su ne suka ɗaukaka shi zuwa matsayin da yake a yau.


Kasuwa kowacce iri ce tana buƙatar ciniki (Sales) yau da kullum.


Ciniki kuma yana buƙatar talla (Advertisement) don sake jawo hankalin abokan cinikin ka, da ma sababbin kwastomomi, don ci-gaba da samun ciniki.


Rarara ya yi ma Bazoum yaƙin neman zaɓe da waƙoƙin sa, tare da abokan aikin sa 'yan fim ɗin Hausa. Kuma ya samu arziki mai yawa daga wannan aiki.


A fahimta ta, mawaƙi Rarara ya yi amfani da wani salo na sakarci, cikin sani da hikima, domin buɗe wani ciniki mai riba, koda kuwa a yanzu babu yaƙin neman zaɓe a Nigeria ko Niger.


Faɗin cewa ya ba wa Tchiani kwana 20, ya jawo cece kuce mai yawa, musamman ga masu ganin rashin hankalin mawaƙin.


Bayan cikar wa'adi da kuma Publicity, wato ɗaukar hankalin da mawaƙin ya yi, Rarara ya saki waƙoƙi kamar yadda ya alƙawarta.


Kowa ya san irin kuɗaɗen da kafofin sada zumunta (Social Media) suke biya akan bidiyoyi, musamman YouTube da TikTok, inda suke biyan daloli akan yawan kallon da aka yi wa waƙa ko wasan barkwanci.


Idan ka ziyarci shafukan mawaƙin, za ka iya fahimtar irin alkhairin da ya samu daga waɗannan waƙoƙi.


Hakazalika wannan shiririta ta mawaƙi Rarara za ta faranta ran magoya bayan tsohon shugaba Bazoum, tare da ci-gaba da nuna da'awar tsohon shugaban cewa, shi ne halastaccen kuma zaɓaɓɓen shugaba.


Don haka makusantan Bazoum tabbas za su yi farin ciki, kuma za su biya mawaƙin ladan aikin da CFA mai yawa.


A taƙaice dai mawaƙi Rarara yana sane ya mayar damu shashashu, mu ka yi ta kumfar baki da nuna jahilcinsa, amma a zahiri ya san wasan da yake shiryawa. Kuma kwalliya tana biyan kuɗin sabulu.


Babban saƙon shi ne, kowa ya iya allonsa ya wanke.


Kuma mu daina ɗaukar cewa mun fi kowa wayo da basira, saboda mun yi boko mun shiga manyan ofisoshi.


Wannan misali ne guda ɗaya, na irin abubuwan da muke musu kallon shirme, amma a zahiri mai yin su ya san abin da yake yi, da manufar da yake son cimmawa.


Allah ya sa mu koyi talla (Advertisement) da jan hankali na kasuwa, (PR) irin na Dauda kahutu Rarara Amin.

Tuesday, 7 January 2025

Amfanin Zama Da Abokai Masu Mabambantan Dabi'u

Amfanin Zama Da Abokai Masu Mabambantan Dabi'u

Kada ka yarda a abokan ka babu mai kuɗi. Kada ka yarda a abokan ka babu mai karatu. Kada ka yarda ba ka da aboki Ɗan duniya.


Amfanin Zama Da Abokai Masu Mabambantan dabi'u
Hoto: Medium

Marubuci:- Bello Ado Hussaini


MAI KUƊI


Idan ya kasance duk abokan ka babu mai kuɗi, zai zama babu zaburarwa wato ƙwarin gwiwa.


Idan babu zaburarwa, zai zama babu zaƙuwa wato sha'awa ko buri ko muradi.


Shikenan sai ku yi zaman ku a waje ɗaya cikin talauci, har lokaci ya ƙure muku.


MAI KARATU


Idan a abokan ka babu mai karatu, to ba za ka san yadda duniya ke canjawa ba, da kuma irin damar da zamani yake zuwa da ita ba.


Sai ku yi zaman ku cikin duhun kai. 


Komai ya faru ku ce ƙaddara ce, tun da bakwa nazari.


Idan kuka ji labarin abin da ya shallake hankalin ku, ku ce ƙarya ne hakan ba zai yiwu ba.


Har zamani ya tafi ya bar ku.


ƊAN DUNIYA


Idan duk abokan ka kamammu (Reasonable) ne, kullum sai kuke ɗauka duka duniya gyararriya ce, ba mutumin banza.


Don haka za ku yi ta faɗawa tarkon mugayen mutane kuna cutuwa.


Amma idan kana da aboki Ɗan duniya, ya san komai da ɗabi'ar mutane daban-daban.


Ko wayo ya ga za a yi maka, zai gaya maka abokina ka buɗe idanun ka, kada a yi ma kure-mure.


Idan ma ta kama a yi wani rashin mutumci da ba za ka iya yi ba, sai ya tsaya maka a yi duk wadda za a yi.


Tarihi ya tabbatar da a kowacce al'umma da ta yi nasara, sai da aka samu kalolin mutanen nan guda 3 a cikin ta.


Kuma kowa ya ba da irin gudummawar da shi kaɗai zai iya bayarwa.


A ci-gaba da nazarin rayuwa, Allah ya sa mu dace, kuma idan mun dace mu dafe.

Monday, 6 May 2019

KARANTA JERIN SUNAYEN MALAMAI DA ALARAMMOMIN DA JIBWIS TA KASA TA TURA TAFSIRIN RAMADAN NA 1439AH 1440H/2019 A JAHOHIN NAJERIYA DA KASASHEN DUNIYA

KARANTA JERIN SUNAYEN MALAMAI DA ALARAMMOMIN DA JIBWIS TA KASA TA TURA TAFSIRIN RAMADAN NA 1439AH 1440H/2019 A JAHOHIN NAJERIYA DA KASASHEN DUNIYA

JAMA’ATU IZALATIL BID’AH WA IKAMATIS SUNNAH SUNAYEN MALAMAI DA ALARAMMOMIN DA JIBWIS TA KASA TA TURA TAFSIRIN RAMADAN NA 1439AH 1440H/2019 A JAHOHIN NAJERIYA DA KASASHEN DUNIYA.




JIBWIS NIGERIA




1. Sheikh Abdullahi Bala Lau Da Alaramma Nasiru Salihu Gwandu - Jimeta, Adamawa

2. Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo Da Alaramma Mustapha Jalingo - Jalingo, Taraba

3. Sheikh Usman Isa Taliyawa Da Alaramma Abubakar Muhd Gombe - Gombe, Gombe

4. Sheikh Abbas Jega Da Alaramma Abubakar Adam - B/Kebbi, Kebbi

5. Sheikh Ibrahim Sabi’u Jibia Da Alaramma Aminu Salisu Jibia - Masjid Hamza Jibia, Katsina

6. Sheikh Yakubu Musa Hassan / Saifuddeen Yakubu Musa Da Alaramma Usman Birnin Kebbi - Katsina, Katsina

7. Sheikh Dr Isma’il Kumo Basirka Da Alaramma Usman Barikin Ladi - Jos, Plateau

8. Shk Dr. Abdullahi Saleh Pakistan Da Alaramma Abbas Iliyasu - Kano, Kano

9. Sheikh Muh’d Kabir Haruna Gombe Da Alaramma Ahmad Sulaiman - T/Wada / Malali, Kaduna

10. Sheik Dr Ali Mustapha Da Alaramma Mato Gumau - Gashua, Yobe

11. Sheikh Abubakar Giro Argungu Da Alaramma Saifullahi Musa Makera - Masjid Haruna Danja Zaria, Kaduna

12. Sheikh Aliyu Abdullahi Telex Da Alaramma Muhsin Ishaq - Aleiru, Kebbi

13. Sheikh Surajo Muhammad Gusau - Gusau, Zamfara

14. Sheikh Mas’ud Ibrahim Offa - Rimi College, Kaduna

15. Dr Muhammad Sani Umar R/lemo Da Alaramma Abubakar Muhammad Rariya - Masjid Gwallaga, Bauchi

16. Sheikh Sani Yakubu Da Alaramma Ridwan Kaduna - Zaria, Kaduna

17. Sheikh Abubakar Abdussalam Baban Gwale Da Alaramma Tukur Jakada - Alkhulafaur Rashidun, Alpa Nla, Agege, Lagos

18. Sheikh Ahmad Muhammad Boyi Da Alaramma Muhammad Aliyu Babangida - Masjid Finance Jalingo, Taraba

19. Dr Ibrahim Abdullahi Sani R/Lemo Da Alaramma Yusuf Suru - Area 11 Masjid, Abuja

20. Mall. Aliyu Ladan Da Alaramma Nasiru Dan Malam - Life Camp, Abuja

21. Mal AbdulRazak Yahaya Haifan Da Alaramma Kabir Hussaini Daura - Gwagwalada, Abuja

22. Mal. Abdullahi Umar Zaria Da Alaramma Salihu Gumi - Garki Village, Abuja

23. Mal. Auwal Mai Gaskiya Da Alaramma Aliyu Ibrahim Paki - Fed. Min. of Works, Abuja

24. Mal. Abdullahi Karshi Da Alaramma Abdulkrim Akwanga - Villa, Abuja

25. Mal. Sahibul Kuwa - Dakkwa, Abuja

26. Mal Abdulrahman Alzamfari Da Alaramma Saifullahi Kira - Berger Masjid, Abuja

27. Dr Ahmad Atiku Auwal - Gwarimpa Masjid, Abuja

28. Mal. Tajuddeen Imam Da Alaramma Murtala Muhammad - Prince & Princes, Abuja

29. Mal Adda’urrahman Alhassan Saeed - Gumel, Jigawa

30. Dr. Bashir Imam - Masjid Amb. Yola, Adamawa

31. Dr. Sadau Salihu - Yola, Adamawa

32. Dr. Abdulqadir Saleh Kazaure Da  Alaramma Idris Gashuwa - Jimeta, Adamawa

33. Dr Abubakar Bama - Masjid Nyanya, Abuja

34. Dr AbdulRahman Sani Yakubu Da Alaramma Sulaiman Abdullahi Azare -Juwa Emirate Council, Abuja

35. Mal Usman AbdulHamid - Numan, Adamawa

36. Mal. Alkali Sulaiman Yusuf Da Alaramma Dauda Muh’d Zukku - Masallachin Adamu Jumb, Bauchi

37.. Mal. Aliyu Saeed Gamawa Da Alaramma Saeed Adamu - Peoples Bank Masjid Gamawa, Bauchi

38. Dr. Ibrahim Adam Umar Disina- Masjid Rahama, Bauchi

39. Mal. Abba Abdullahi Gwale Da Alaramma Idris Saminaka - Lapai, Niger

40. Mall Abdul aziz Dan lami Da Alaramma
Nafiu A A saeed - Tilden Fulani, Bauchi

41. Mal. Abubakar Mala Da Alaramma Bala Bako - Alkaleri, Bauchi

42. Dr. Zubairu Madaki Da Alaramma Kabir Abdullahi - Masjid Umar bn Al khattab, Kofar Wambai, Bauchi

43. Shk Ahmad Tijjani Yusuf Guruntun Da Alaramma Muhammad Zahruddeen - Masj S19 Dutsen Tenshe Bauchi, Bauchi

44. Mal. Abubakar Mukhtar Yola - Masallachin Nepa Jimeta, Adamawa

45. Sheikh Abubakar Usman Pakistan Da Alaramma Farouq Jada Tambuwal - Makurdi, Benue

46. Mal. Nura Khalil - Apo, Legislative Quarters, Abuja

47. Mal Yaqub Isah Da Alaramma Adam Mahmud - Kwayakusar, Borno

48. Mal.Abba Musa Da Alaramma Aminu Ibrahim Potiskum - Maiduguri, Borno

49. Shk Muhd Abubakar Kachalla Da Alaramma Ahmad Jiha Ismail - Maiduguri, Borno

50. Mal Zainu Usman Baban Tine - NNPC Kaduna, Kaduna

51. Dr. Umar Dokaji Da Alaramma Auwal Ung Maikawo - Sapele, Delta

52. Mal. Nazifi Hashim Zaria Da Alaramma Hassan Musa Funtua - Cattle Market Benin City, Edo

53. Mal. Shafi’I Salihu Kazaure Da Alaramma Sani Ibrahim Mainiyya - Ung. Sabo Ile-Ife, Osun

54. Mal. Mustapha Yusuf Hadejia Da Alaramma Muhd Auwal Jalingo - P/Harcourt, Rivers

55. Mal. Adam Muhammad Adam Da Alaramma Abubakar Jibril Bula - Gombe, Gombe

56. Dr Abdallah Umar Gadon Kaya Da Alaramma Baba Lawal - Kan Bariki,( Water Board) Kumo, Gombe

57. Mal. Usman Bello Santuraki Kumo Da Alaramma Nafiu Ismail - Kazaure, Jigawa

58. Mal. Sulaiman Abubakar Birnin Kudu - Yalwan Damai, Jigawa


59. Mall Isa Abdullahi Da Alaramma Hamza Isa Abdullahi - Hadeja, Jigawa

60. Mal. Alkasim Hotoro Da Alaramma Yunus Isma’il - Potistum, Yobe

61. Dr Abdurrahman Idris zakariyya Da Alaramma Auwal Iliyasu - Saminaka, Kaduna

62. Mal. Musa Asadus Sunnah - Sokoto, Sokoto

63. Mal. Murtala Nasir Almisry Da Alaramma Aliyu Dahir - ASD Motors, Kaduna

64. Mall Abdulrahman Maiduguri Da Alaramma Shamsuddeen Haruna - Rigachikun, Kaduna

65. Mal Abubakar Usman Bolari - Oshogbo, Osun

66. Mal. Hamza Alhassan Sa’eed Da Alaramma Abubakar Rano - Sani Zangon Daura Estate, Kado, Abuja

67. Mal Nura Kofar Mata Da Alaramma Abubakar Umar Balarabe - Ojo-Express T/Sunnah Ibadan, Oyo

68. Mal. Ibrahim Abdullahi Bauchi Da Alaramma Kabiru Yawuri - Ado-Ekiti, Ekiti

69. Dr Idris Alhassan Abubakar Da Alaramma Shamsu Ahmad Mairuwa - Gboko, Benue

70. Sheikh Abdul Hadi Aliyu Daura Da Alaramma Yunusa Abubakar - Dan Fodio Masjid, Kaduna

71. Mal. Usman Zagga Da Alaramm Safiyan Abdullahi - Rijau, Niger

72. Mall Shuaibu Salihu Zaria Da Alaramma Abdullahi shu”aibu sal - Al-Islah Foundatn Zaria, Kaduna

73. Mal. Muhammad Sani Alhamidy - Bebeji, Kano

74. Mal. Abdul mudallib Ahmad Muhammad Da Alaramma Salihu Muhd Usman - Masjid Triump, Kano

75. Mall Abdul mudallib Gusau Da Alaramma Umar Ramadan - State Univ.Wudil, Kano

76. Mall Saifullahi Adam Shuaib Da Alaramma Tasiu Sabiu - Huguma Takai Kano, Kano

77. Mal Muhd Adam Algargawy - Kura, Kano

78. Mall Ibrahim Idris Zakariyya - Tudun Wadan Dankade, Kano

79. Mall Surajo Mahmoud Kankia - Govt Printing Katsina, Katsina

80. Mal. Aminu Liman Mustapha - Zaria Rd Masjid FT, Katsina

81. Mal. Mukhtar Usman Jibia - Govt. House, Katsina

82. Mal. Aminu Yammawa - Masjid. G.R.A, Katsina

83. Mal. Yahaya Salihu Isah Da Alaramma Auwal Umar - Masjid Kerau, Katsina

84. Mal. Musa Mansur Da Alaramma Salihu Ahmad - Masjid Karama Daura, Katsina

85. Mal. Hassan Yusuf Da Alaramma Haruna Salisu - Masjid Senator (Madawaki)Daura, Katsina

86. Dr Jamilu Zarewa Da Alaramma Ashiru Rawayau, Masj Bilal Ibn Rabah N/Low-Cost, Katsina

87. Mall Safiyyu Alqasim Saulawa Da Alaramma Mukhtar Salisu Jibiya - Bakori, Katsina

88. Mal. Jamilu Albani Da Alaramma Abuzaid - Lafia, Nasarawa

89. Mal. Umar Jiga Da Alaramma Shukranu Yelwan Shandam - Sokoto, Sokoto

90. Mal. Muhammad Rabi’u Isah Fatawa Da Alaramma Adam Muhammad Fana - Bena, Kebbi

91. Mal. Ahmad Ahmad Kura - Dutsin-ma, Katsina

92. Mal. Imam Aliyu Bunza Da Alaramma Amiru Ibrahim Argungun - Argungun, Kebbi

93. Mal.Umar Sadiq Jega Da Alaramma Iliyasu Birnin Gwari - Suleja, Niger

94. Sheikh Mukhtar Zinder - Illela, Sokoto

95. Mal. Imam Dahiru Lokoja Da Alaramma Ishaq - Lokoja, Kogi

96. Mal. Imam Yahaya Iddah Da Alaramma Auwal Muhammad - Iddah, Kogi

97. Mal. Yusuf Umar Da Alaramma Rabi’u Ibrahim - Obajana, Kogi

98. Mal. Salihu Muhammad Da Alaramma Ahmad Muhammad - Kaiama, Kwara

99. Mal. Attahiru Kaiama Da Alaramma Ibrahim Kaima - Ilorin, Kwara

100. Dr Abdulmajid Umar - Rimi Collage, Kaduna

101. Mal. Hussini Isa Abubakar Da Alaramma Nafi’u Bena - Yawuri, Kebbi

102. Dr Muhammad Sani Suleiman Ft Da Alarramma Abubakar Kaura - Gombe, Kumo, Gombe

103. Mall. Bukhari Yakubu Da Alaramma Muhammad fari - Agege Lagos, Lagos

104. Mall Adamu Salihu Gusau - Tambuwal, Sokoto

105. Sheikh Imam Sulaiman - Masjid 1004, Lagos

106. Mal. AbdulRahim Sabi’u Rafindadi Da Alaramma Sani Danwarai - Kontagora, Niger

107. Mall Adam Ibrahim Al-madani Da Alaramma Abbas Dahir Abubakar - Karu Masjid JIBWIS, Nassarawa

108. Mal Rufa’i Nasir Da Alaramma Ibrahim Abubakar - Keffi, Nasarawa

109. Dr Umar Gumi Da Alaramma Sulaiman Hussaini Doma - Doma, Nasarawa

110. Mal. Muh’d Sani Ahmad Almuhadis Da Alaramma Abubakar Bawa - Wawa, Niger

111. Mal. Lawal Shu’aibu Abubakar Da Alaramma Abdulrashid Jega - Minna, Niger

112. Mal. Mujittaba Yakubu Musa Da Alaramma Jamilu Isah Dallaje - Kafanchan, Kaduna

113. Mall Isah Shehu Ruga Da Alaramma Abubakar Ung Madi - Ganye, Adamawa

114. Mall.Muhammad Auwal Rijau Da Alaramma Abubakar A. Abubakar Kagara - Mariga, Niger

115. Mal. Abba Musa Da Alaramma Aminu Ibrahim - Maiduguri, Borno

116. Mall Musa Mujaddadi - Lafai, Nigrer

117. Mal.Bukhari Ibn Ishaq Albayani Da Alm Anas Abdullah Yalwan Shandam - Shiroro, Niger

118. Mal Isah Ibrahim Bawa Mai Shinkafa Da Alrm Ismail Abdullahi Mangu - Yalwan Shendam, Plateau

119. Mall Muhammad Aminu Muhammad Saminaka Da Alaramma Yusuf Dabai Mai  60 - Bukur, Plateau

120. Mal. Muhammad Barkindo Jungudo Da Alaramma Abdullahi Badejo - Jalingo Masjid Ummah, Taraba

121. Mall Nuruddeen Tukur Numan Da Alaramma Bashir Gombe - Jami’u Hajara Plaza Funtua, Katsina

122. Mal. Yunus Saeed Abdul-Hamid Da Refinery Depot, Rivers

123. Mal. Abdulbasir Ung MaiKawo Da Alarmma Sani Mulumfashi - Koko, Kebbi

124. Mal.Aliyu Aliyu Muhammad Jos Da Alaramma Bala Abubakar Tambuwal - Hadeja, Jigawa

125. Mal. Umar Mai Damma Da Alaramma Auwal Adam Sokoto - Masjid Sheik Abubakar Gumi Sokoto, Sokoto

126. Mal. Abubakar Ladan Mai Idigami Da Alaramma Muhammad Auwal - Masjid Lokoja Road Sokoto, Sokoto

127. Mall Sani Abubakar Tambuwal - Sultan Ibrahim Dasuki Mosque, Sokoto

128. Sheikh Dr. Mansur Ibrahim Sokoto Da Alaramma Abubakar Ghani - MasjidAbu Huraira, Sokoto

129. Dr Muhammad Rabi”u Collage Da Alaramma Sidi Ali - Ningi, Bauchi

130. Mal. Gambo Kyari Maiduguri Da Alaramma Mustapha Hamza Jarmai - Wukari, Taraba

131. Mal Khalid Usman Khalid Da Alaramma Salisu Ung. Kanawa - Gummi, Zamfara

132. Mal Hassan Bako - Shagamu, Ogun
133. Imam khidir Bello Manufa Da Alaramma Hudu Usman Aleiru - Bukkuyum, Zamfara

134. Mal. Attahiru Muhammad Tilde - Jaji Maji, Yobe

135. Mal Abdulaziz Ibrahim Bauchi Da Alaramma Sulaiman shafi’I FTA - Matazu, Katsina

136. Mal Aliyu S. Mafara Da Alaramma Usman Tagule - Kamba, Kebbi

137. Mal.Ibrahim Damaturu Da Alaramma Sani Nguru - Damaturu, Yobe

138. Dr Umar Musa Kano Da Alaramma Bello Argungu - Anka, Zamfara

139. Mal. Usman Arabi - Malumfashi, Katsina

140. Mal. Aminu Numan Da Alaramma Amir Abdullahi Dorawa - Mangu, Plateau

141. Mal. Abubakar Salihu Dengi - Ibadan, Oyo

142. Mal. Anas Assalafy - Ketaren Waya, Benue

143. Mal. Abubakar Musa Azi - Ebonyi, Ebonyi

144. Mal. Shuaibu Adam Makoli - Dangi, Plateau

145. Mal. Aminu Khalil U/Barau - Masjid Ahlil Sunnah Ikorodu, Lagos

146. Mal Surajo Umar Maga Da Alaramma Alkasim Musa - Masjid Hausa Qtrs Ugella, Delta

147. Mal Musa Usman Alkanawi Da Alaramma Mu’awiyya Adbdulrahman - Masjid Ujole, Ekpoma Town, Edo

148. Mal Abubakar Usman Da Alaramma Anas Abubakar - Masjid Lagos Str Benin City, Edo

149. Sheik Muhammad Fatihu Da Alaramma Ibrahim Adam Futua - Apo Legislative Qtrs Zone A, FCT

150. Sheik Ibrahim Lawal (USAMA) Alaramma Zaharadden Surajo - Apo Legislative Qtrs Zone B, FCT

151. Mal. Muhammad Abubakar Da Alaramma Fadlu Muhammad - Apo Legislative Qtrs Zone D, FCT

152. Mal Yahaya Gidadawa Da Alaramma Mustapha Hamza Jarmai - Onitsha, Anambra

153. Mal Murtala Bello Da’a Da Alaramma Ibrahim khamis Saminaka - Benin city, Edo

154. Mal Hussaini Yusuf Mabera Da Alaramma Mustapha Argungu - Warri, Delta

155. Mall. Muhammad Auwal Isah Jere Da Alaramma Murtada M. Namadi - Bakin Gareji,Jere, Kaduna

156. Dr Abubakar Usman Ribah Da Alaramma Muhammad Bunza - Bargu, Niger

157. Mall Rabi’u Aminu Bebeji - Geidam,  Yobe


GHANA

1. Mal. Muhammad Umar Abdulhanna Da Alaramma Abdulrahman Abubakar - Masjid Ib Abbas Ghana

2. Mal. Ahmad Ibrahim - Masjid Khulafa’urrashi
dun

3. Mal. Muh’d Bello Muh’d Saminu - Masjid Bilal

4. Mal. Sanusi Yusuf Muh’d - Masjid Furqan

5. Mal. Abdul Razak Kumasi Da Alaramma
Abdullahi Ibrahim - Masjid Daraarul Hadith

6. Mal. Abdul Malik Idris - Masjid Attaqwa

7. Mal. Muhammad Kaamil Da Alaramma Abubakar Idris - Masjid Ta’afo

8. Mal. Muhammad Addo - Masjid Zuraak

9. Mal. Muhammad Suwaid - Annaduwa

10. Mal. Manir Saeed - Bilal Accara

11. Mal. Sulaiman Adam Aljamzuri - Masjid Jami’ul Rahma

12. Mal. Muhammad Taufeeq Abdulrahman Kulusey - Masjidul Nurul Ameen


TOGO


1. Mal. Muawiyya Umar Mukhtar Ali Da
Alaramma Mukhtar Ali - Masjid Abu Ubaida

2. Mal. Salihu Saaya - Masjid Furqan

3. Mal. Abubakar Ali - Masjid Attaqwa

4. Imam Ahalil Sunnah (Abdulwahab Abdallah) Da Alaramma Dan Mairogo - Babban Masallacin Zango

COT’D VOURE


1. Mal. Jibirilu Musa Da Alaramma Usman Muh’d - Masjid Khausar Farbi Abidjan

2. Mal. Alhassan Musa Da Alaramma Abubakar - Apobo Abidja

3. Mal. Muh’d Abdulkarim Da Alaramma Abubakar Musa - Masjid Alh. Yusha’u Usaini Abidjan

4. Mal. Abdulsalam Shu’aibu Da Alaramma
Ukasha Alasan - Masjid Hausa Bugu Korgu

5. Mal. Khalil Abubakar Da Alaramma Abubakar Madu - Masjid Hausa Sempedro

6. Mal. Idris Haruna Da Alaramma Buhari Sale - Fresh Zeal Abidja

7. Mal. Muhammad Hariz Da Alaramma Abdullahi Yusuf Yakubu

8. Mal. Hamza Abdullahi Da Alaramma Abdullahi Abdulrahman - Yamasukuro

9. Mal. Hamza Idris - Yamasukuro

NIGER REP.


1. Mal. Imam Abdullah Umar - Masjid Imam Malik Niamey

2. Mal. Hussaini Hassan - Masjid Usman Ibn Affan Niamey

3. Mal. Abdul rahman Hussaini - Masjid Imamul Bukhari Niamey

4. Mal. Kasim Ali - Masjid Umar bn Khattab Niame

5. Mal. Iliyasu Abdullahi Da Alaramma Adam Muh’d Ibrahim - Masjid Karkada Zinder

6. Mal. Nazir Manzo Magarya Da Alaramma Abubakar Alhassan - Magarya

7. Mal. Abubakar Ibrahim - Magarya

8. Mal. Murtala Ibrahim - Maradi

9. Mal. Murtala Ibrahim - Tassawa

10. Mal. Adamu Salihu - Dosso

11. Mal. Abba Ghana - Tahoa

12. Mal. Nuhu Muhammad - Tahoa

13. Mal. Khamis Ahmad Da Alaramma Abubakar Usman - Galmi

14. Mal. Muhammad Khulud Ahmad - Maine, Soroa

15. Mal. Adam Ibrahim - Dosso

16. Mal. Abdulrahman - Teleberi

17. Mal. Dauda Nuhu - Teleberi

18. Mal. Yakubu - Teleberi

19. Mal. Yunus Chilakaro - Diffa

20. Mal. Abba Ghana - TahoaMal.

21. Ishaq Adam (Barrister) Da Alaramma Abdulhay. - Umar bn Alkhadab Gaya

22. Sheik Shuaibu Muhammadu Da Alaramma Sulaiman Abubakar - Masjud Al’ansar Niamey

23. Mal. Aliyu Muhammad Sani Adarawa Da Alaramma Ibrahim Yahuza Bauchi - Niamey

24. Mal.Muhammadu Haruna Gaya Da Alaramma Nuhu Adamu - Masjid Imam Malik

25. Mal.Muhammad Usman Da Alaramma Khalil Iarhim - Masjid Muhajirin

26. Mal.Sanusi Abubakar Da Alaramma Muhammad Abubkar - Masjid Round Point Ba Are

27. Mal. Salifou Abdullahi Maradi Da Alaramma Kamissou - Masjid Marad

28. Mal. Buhari Muhammad Da Alaramma Idrissa Issofou - Masjid Tahoa

29. Mal. Salissou Garba Da Alaramma Massa-oudour Hussaini - Masjid Diffa

30. Mal. Laminou Da Alaramma Aliou Moussa - Masjid Zinder

31 Mal. Khalid Hassan Da Alaramma Abdullbaki - Masjid Niamey

32. Mal. Ousseini Abdoulaye Da Alaramma Laouali - Masjid Arlit

33. Mal. Bachirou Yahaye Da Alaramma Ibrahim - Masjid Tillaberi

BURKINA FASO


1. Mal. Yakubu Tanko - Kantchari

2. Mal. Hamma Zakariya - Namuno

3. Mal. Dr. Kindo Muhammad - Ougadougou

4. Mal. Muhammad Bashir Da Alaramma Yahaya Adam - Falagountou

5. Mal. Aufon Muhammad - Falagountou

6. Mal. Muhammad Usman - Masjid Furqan


BENIN REP.



1. Mal. Muhammad Kabir - Zango Cottonou

2. Mal. Suleiman Abubakar Da Alaramma Abu Sambo - Malabil

3. Mal. Abdulganiyu Raji Da Alaramma Shuaibu Latifi - Malabil

4. Mal. Jibril Abubakar Da Alaramma Ibrahim Abdullahi - Cotonor

5. Mal. Umar Garba Da Alaramma Zubair Mairiga - Cotonor

6. Mal. Idris Ishaq Da Alaramma Mujahid Dahir - Zuggu

7. Mal. Usman Abdulwahab Da Alaramma Hudu Abdullatif - Zuggu

8. Mal. Marwan Umar Da Alaramma Abdul Mateen - Kandee

9. Mal. Haruna Alhassan Da Alaramma Nasir Ishaq - Kandee

10. Mal. Dr. Dauda Da Alaramma Isa Adam - Kandee

11. Sheikh Abdullahi Banji Da Alaramma Jibril Ahmad - Malabil

12. Mal. Khalid Zakariya Da Alaramma Dauda Abubakar - Boyiko

13. Mal. Mukhtar - Farako

CAMEROUN


1. Sheikh Saidu Makoli - Bamenda

2. Sheikh Dr. Abu Umar Bala - Bamenda

3. Sheikh Suleman - Douala

4. Sheikh Bello - Younde

5. Sheikh Hadi - Younde

6. Sheikh Godabe - Doula

7. Sheikh Usman - Younde

8. Sheikh Sule Adam Labo - Masjid
ITTIHAD, Doula

9. Sheikh Abu Umar - Masjid Nur, Baminda

10. Sheikh Usman Biyagoro - Masjid Mgyengai, Younde

11. Sheikh Bello - Masjid Alhaji Garbati, Younde

12. Imam Mahmud Aliyu - Baban Masallacin Sarki, Gamdare

13. Sheikh Abdullahi - Masjid Alhaji Adam Bertuwa

14. Sheikh Zakariya Dotti - Masjid Salam, Doula

15. Sheikh Yakubu - Masjid Rahma Walhidaya, Doual

16. Sheikh Nasara Ismail Bagori - Masjid Taqwa

SENEGAL


1. Mal. Abdulkarim Yahaya - Dakar
GUINEA CONAKRY

1. Dr. Mourris Abubakar - Conakry
CENTRAL AFRICA

1. Dr. Badiga Moussa - Bangui

SAUDI ARABIA

1. Shiekh Rajab - Masjidu Ameera Makkah
United State Of America (USA)

1. Mal. Kassim Muhammad Bella - Masjid Mumineen 8875 Benning, Dr Houston Texas 77031, USA

2. Mal. Firdaws Ladan - Masjid Ibn Taymiyyah 8000 martin luther king Jr Hwj,Glen, Arden,MD, USA
Europe(UK)

1. Mal.Muhammad Mubarak Abdulai (M Bature) - Mrkazul Tauheed NO.1 rectory Road,St 1,Stoke on Trent, Staffordshire, UK


2. Mal.Muhammad Saifuddeen Abubakar - Masjidul Salaam Comunidad Islamica De Benidorn Juzgados, Benidorm, Alicante, Spain

3. Mal.Mu’azu Shu’aib Bamba - Masjidul Sunnah Uppsala, Bandstolvagen,37,75648

4. Mal.yousuf Umar Jallo - Masjidul Rahma (Hamburg) Beim Gesundbrunnen 1 ,20537,hamburg, Germany

5. Mal.Muhammad Brussels - Masjid Abubakar Sddiq Rue de la Colonne, 32,Bruxells 1080. Belgium

Allah ya taimaka, ya bada ikon aiki da abun da za'a gabatar. Amin.



Sanarwa: Sakataren kungiya na kasa
Sheikh Dr. Kabiru Gombe.


Via: Ibrahim Baba Suleiman
Director General, Jibwis
Social Media.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu


Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode






Source: Jibwis Nigeria