Monday 11 September 2017

KARANTA DALILIN DA YASA AKE KASHE MUSULMAI A KASASHEN DUNIYA MUSAMMAN KASAR BURMA

Tura Wannan Zuwa Ga


Babu laifi idan ka bayar da sakan 90 daga
lokacin ka domin Kasan matsalar ((Burma)) da
musulmi a cikin ta.


Kissar a takaice :

Kasa ce mai cin gashin kanta sunanta ARAKAN
tana da musulmi miliyan uku, ta hanyar su sai
musulunci ya fara yaduwa a Kasar da take
makotaka da ita, sunanta BURMA wadda mafiya
yawan mazaunanta mabiya addinin Buddah ne.

A shekara 1784 wato kimanin shekara dari biyu
da talatin da suka wuce, sai mabiya addinin
Buddah suka kullaci musulman ARAKAN dan
haka suka yake su, suka kashe musulmi a
cikinta, suka yi musu aika aika, suka hade Kasar
ARAKAN da Kasar BURMA, suka canja sunanta
izuwa (MYANMAR) ta dawo wani bangare na
BURMA, sai musulmi suka dawo yan kadan bayan
da sun Kasance kasa mai zaman kanta (adadinsu
miliyan uku ko hudu) mafiya yawa sune mabiya
addinin Buddah, adadinsu miliyan hamsin.

Sai musulmi suka samar da yan garuruwa masu
cin gashin kan su, suna gudanar da rayuwar su a
ciki, suna kasuwanci, acikin garuruwan akwai
kungiyoyi da suke kula da masu wa'azin su da
masallatansu.

Sai wadancan yan BURMA wato mabiya addinin
Buddah suka rika kai farmaki a kan garuruwan
musulmi; Saboda su kore su daga gidajensu.

A dan wani lokaci da bai jima da wucewa ba
wasu kashe kashe masu ban tsoro sun afku,
yayin da mabiya addinin Buddah marasa imani
suka tare wata mota mai dauke da mutum goma
na malamai masu kira zuwa ga addinin Allah,
daga mahaddata Alqur'ani wadanda suke
zagayawa garuruwan musulmi, suna haddatar da
su Alqur'ani, kuma suna kiran su zuwa ga Allah,
suna daura musu aure, tare da karantar da su
sha'anin addinin su, wadannan mutane makiya
Allah suka tare motar masu wa'azin nan, suka
rika fito dasu suna dukansu duka mai fasa jiki,
sannan suka rika wasa da wukake a jikinsu,
sannan suka rika daure harshen su daya bayan
daya sannan su cizgo shi tun daga
makogwaronsa babu tausayi ba jin kai, duk
wannan fa Saboda kullacin da suke musu akan
suna kira zuwa ga addinin Allah, kuma suna
koyawa mutane addini da Alqur'ani.

Sannan suka rika sukansu da wukake suna yanke
hannayensu da kafafuwansu, har sai da suka
mutu daya bayan daya

Sai musulmi suka taso dan bada kariya ga
malamansu kuma limaman masallatansu masu yi
musu huduba.

Sai Mabiya addinin Buddah suka fuskanto su
suka fara ƙone garuruwansu daya bayan daya, har
sai da adadin gidajen da aka kona ya kai gida
2600 dubu biyu da dari shida, wadanda suka
mutu suka mutu wadanda suka gudu suka gudu,
mutum dubu 90 kuma suka yi sulale daga
garuruwan ta hanyar kogi ko ta sarari, kuma
yankan da kisan da ake wa musulmi har yanzu
ana ci gaba da yi, kuma an kwace yanmatansu
da yayansu mata da kuma matayensu, ga
matsayin da zai kai zuwa ga kisa akan idon
iyalansu, alhalin suma suna karkashin kaifin
wukake ..

Toh Meyasa bama kishinsu...?

Kowa ya tambayi kansa me zan iya yi musu..?

Abinda ya wajaba gareka a kansu a yanzu abu
biyu ne:

Na daya...

Kayi musu addu'a...

Na biyu... Ka yada yada al'amarinsu dan mutane
su sani... Wannan shi ne mafi raunin imani...

Idan ka gama karantawa.. Toh ka aikata abinda
zuciyar ka ta raya maka, wannan fa idan zuciyar
taka tana raye..?!!!

Allah ya isar mana Madalla da abin dogaro shi...

ku yada shi domin musulmi su san al'amarinsu.

Ni M. Kabiru Muhammad Da sauran 'yan uwa
Musulmai munayin addu'ar ALLAH ya daukaka
musulinci da Musulmai aduk inda su kasance, ya
kuma kaskantar da kafirci da kafirai aduk inda su
kasance...

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki 

Mungode


TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user