Tuesday 12 September 2017

Ni ba barawo bane zanyi Yaki da Cin hanci da Rashawa wanda Ba'a tabayinsa ba In Ku Zabe Ni a 2019-Atiku Abubakar

Tura Wannan Zuwa

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku
Abubakar ya kalubalanci masu cewa ya yi sata
lokacin da yake da rike da mukaman gwamnati
su bayar da hujja ko kuma su yi shiru.
Wata sanarwa da ofishin ya fitar ta ambato shi
yana cewa, "A ko da yaushe mutanen da ba su
da hikima ta yin kasuwanci suna tunanin cewa
kowa barawo ne kamar su. Suna ganin cewa
wani ba zai iya gina kansa ba ba tare da ya yi
sata ba".
Atiku ya kara da cewa zai yi yaki da cin hanci da
rashawa "yadda ba a taba yi ba" idan aka zabe
shi a matsayin shugaban Najeriya, yana mai
cewa "abin haushi mutanen da suka gaza kawo
hujja su ci gaba da yi min zargin cin hanci da
rashawa".
"Duk da binciken da aka gudanar a baya domin
alakanta ni da cin hanci da rashawa da kuma
shari'ar da aka yi wa William Jefferson a Amurka
a shekarar 2009, an kammala ba tare da an
tuhume ni da cin hanci ba", in ji babban jigon na
jam'iyyar APC.
.
Tsohon dan takarar shugabancin na Najeriya na
yin wadannan kalamai ne a daidai lokacin da ya
zargi gwamnatin Shugaba Buhari da rashin yin
abin a-zo-a-gani wurin magance matsalolin
kasar.
Alhaji Atiku Abubakar, wanda bai taba boye
kwadayinsa na son shugabancin Najeriya ba, ya
ce Shugaba Buhari ya mayar da shi saniyar-ware
tun da ya zama shugaban kasa duk kuwa da
cewa da kudinsa aka yi amfani wurin yakin
neman zabensa.
A kwanakin baya ne dai ministar harkokin mata
ta Najeriya, Aisha Jummai Alhassan, ta shaida
wa BBC cewa ba za ta sake goyon bayan
Shugaba Buhari ba idan ya sake tsayawa takarar
shugaban kasa, tana mai cewa "zan goyi bayan
uban dakina Alhaji Atiku Abubakar, wanda shi ne
ya sa ni a gwamnatin Shugaba Buhari".
Ta sha suka daga wurin magoya bayan Shugaba
Buhari bisa kalaman nata, inda takwaranta na
ma'aikatar wasanni Mr Solomon Dalung ya yi kira
ga shugaban kasar ya sallame ta
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address dinba mungode
.
Source by BBC HAUSA

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: