Sunday 17 September 2017

Ana Amfani da Kungiyar yarabawa don Kifar da Gwamnatin Buhari-Lai Mohammad

Tura Wannan Zuwa

Ministan watsa labaran Najeriya ya yi zargin
cewa wasu mutane ne da ba sa kaunar Shugaba
Muhammadu Buhari ke daukar nauyin 'yan
kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biafra
domin su kifar da gwamnatinsa.

A wata sanarwa da ya aikewa manema labarai,
Alhaji Lai Mohammed ya ce ''Ya kamata 'yan
Najeriya su faminci cewa baa kafa IPOB domin
neman 'yancin kowanne mutum ko kungiya ba,
sai dai ta zama wani makami da zai wargaza
kasar nan da kuma kawar da hankalin jama'a
daga ayyukan da gwamnatin Shugaba Buhari ke
yi.''

Ministan ya kara da cewa "Wata gamayyar
kungiyar mutanen da suka rasa madafa a siyasa
da wadanda suka sace kudin gwamnati ne suke
daukar nauyin kungiyar IPOB. Sun yi amanna
cewa idan suka dauki nauyin wannan kungiya za
su iya hargitsa kasar nan da kuma tayar da
tarzoma".

Alhaji Mohammed ya nuna mamakinsa kan yadda
tayar da hankalin da 'yan kungiyar ta IPOB ke yi
ya yi kamari a lokacin da aka zabi gwamnatin
Shugaba Buhari, yana mai cewa ''lallai ruwa ba
ya tsami banza".

"Ya kamata a tuna cewa a lokacin gwamnatin
Goodluck Jonathan, Nnamdi Kanu, ya jagoranci
zarga-zargar yaki da Boko Haram da kuma nuna
goyon bayan gwamnati a kofar gidan gwamnatin
Najeriya da ke London. Yanzu kuma ya rikide ya
zama jagoran IPOB da ke son hargitsa kasar
nan,'' in ji ministan.

'Yan Biafra 'yan ta'adda ne — Sojin Nigeria
Wadanne batutuwa Buhari ya taras a
Nigeria?
Ministan ya yaba wa rundunar sojin Najeriya
saboda ayyana 'yan kungiyar IPOB a matsayin
'yan ta'adda.

A ranar Juma'a ne rundunar sojin ta ayyana
kungiyar a matsayin ta ta'addanci.
Wata sanarwa da daraktan watsa labarai na
rundunar tsaron kasar Manjo Janar John
Enenche ya aikewa manema labarai, ya ce
kungiyar, "ta sauya zuwa barazanar tsaro ga
kasar".
Ta kara da cewa, "Bayan mun yi nazari a
tsanake kan abubuwan da ke faruwa a baya
bayan nan, muna son sanar da jama'a cewa
ikirarin da mambobin IPOB ke yi cewa ita ba
kungiyar tayar da hankali ba ce ba gaskiya ba ne.

Don haka abubuwan da suke yi ta'addanci ne"
Sai dai 'yan kungiyar ta IPOB sun ce su ba 'yan
ta'adda ba ne.

Wani dan uwan Kanu mai suna Prince Emmanuel
Kanu ya shaida wa BBC ta wayar tarho cewa
matakin da sojin suka dauka abin dariya ne.
"Wannan kalami abin dariya ne da ke fitowa daga
dakarun soja saboda, na daya, ayyukan da muka
kwashe shekara da shekaru sun nuna cewa IPOB
kungiya ce mai tafiyar da al'amuranta lami lafiya.

"Mun yi ammana da abin da muke yi kuma muna
yin sa yadda ya kamata bisa doka; ba ma kisa
ba ma kuma sa wa wani ya yi kisa da yawunmu.
"Niyyarmu ba ita ce takalar yaki ba; niyyarmu ita
ce mu fargar da kowa cewa muna cikin ukuba a
Najeriya. Kuma irin yadda muke cikin wahala,
haka mutane da dama ke cikin mawuyacin hali a
arewacin Najeriya. Nnamdi Kanu yana yaki ne da
zaluncin da ake yi wa 'yan Najeriya ba ka kawai
kabilar Igbo ba".
.
.
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com
mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website
din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more
rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine
Farn Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar
Zumunci Amin
.
.
Source By Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: