Thursday 14 September 2017

Dalilin da ya sa ake min kallon 'yar wiwi — Hauwa Waraka

Tura Wannan Zuwa

Jarumar fina-finan Hausa, Hauwa Abubakar
wacce aka fi sani da Hauwa Waraka, ta ce tana
yawan fitowa a mutuniyar banza ne saboda ta
nunawa al'umma illar rashin kirki.
"Ina fitowa a matsayin karuwa ko 'yar kwaya ko
ballagaza ne saboda na ilimantar da mutane
domin su guji zama irin wadannan mutane", in ji
Hauwa Waraka, a hira ta musamman da BBC.
Ta kara da cewa, "Ban taba karuwanci ba kuma
ban taba yin hulda da karuwai ba, amma idan ina
taka rawa a matsayin karuwa kai ka ce ni
tsohuwar magajiya ce."
A cewar jarumar bai kamata mace da za ta fito
a matsayin karuwa "a gan ta sanye da hijabi ba.
Ko kuma macen da ta fito a matsayin 'yar shaye-
shaye a gan ta ras kamar mutuniyar kirki ba.
"Shi ya sa za ka gan ni ina keta rashin mutunci a
fim kamar da gaske. Kuma abin da ya kamata
kenan."
Hauwa Waraka ta ce sau da dama tana zuwa
unguwa mutane suna "cewa wacce irin kwaya ko
wiwi ko taba za su kawo min na sha. Ba su san
cewa ban taba shan kayan maye ba; wallahi ko
taba ban taba sha ba. Duk abin da ka ga ni a fim
ne".
Da aka tambaye ta kan zargin da ake yi wa 'yan
fim na luwadi da madigo, jarumar ta ce akwai
bara-gurbi sosai a cikinsu "kamar yadda akwai su
a cikin ko da Malaman addini amma bai kamata
a yi mana kudin-goro ba."
Ta bukaci mutane su rika yi musu uzuri
musamman ganin cewa su ma mutane ne kamar
kowa.
Hauwa Waraka, wacce ta ce tana son yin aure,
ta kara da cewa "kai ma wakilin BBC idan kana
sona ka fito. Wallahi aurena ba zai yi tsada ba.
Kai, ni zan hada maka lefe ma akwati shida idan
kana so.
"Ko da yake na san tsoron matarka kake yi kada
ka je gida ta ki bude maka kofa"...(dariya).
.
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba mungode Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
Source By Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: