Thursday 14 September 2017

Ko kun san kasar da ake cin kyankyaso a Afirka?

Tura Wannan Zuwa

Duk da yake yawancin mutane na ganin
kyankyasai abin kyama ne, amma wani matashin
dan kasuwa mai suna Rwehura Daniel daga
kasar Tanzania ya samo wata hanyar kiwon su
da kuma sayar da su ga masu bukata.
Masana sun tabbatar da cewa kyankyasai na da
sinadarin gina jiki na protein da yafi na dukkan
halittu a fadin duniya.
To ka taba tunanin cewa kyankyasai na da
amfani ta bangaren abinci mai gina jiki?
Rhewura Daniel ya sami karfin gwuiwar kiwon
kyankyasai masu yawa kuma wannan harkar ta
zame masa hanyar kasuwanci mai kawo masa
kudaden shiga.
Ga abin da Rwehura Daniel ya ce: "Wannan
dabarar ta zo min ne a lokacin da nake neman
hanyoyin sarrafa bola domin in samu kudi.
Birnin Dar es Salaam cike yake bola kuma na
san zaka yarda da ni cewa inda bola ta yi yawa,
akwai kyankyasai ma masu yawa".
Ya kara da cewa, "To a lokacin ne muka yi
tunanin cewa kyankyasan na da amfani a
matsayin abinci mai gina jiki ga rayuwar dan
Adam, kuma wannan damar ta fadada min
tunanina, har na kai ga samun karuwar hanyoyin
kudaden shiga.
A halin yanzu na zama mai horas da mutane kan
dabarun samun kudi daga kasuwancin
kyankyasai, kuma ina samun kudaden shiga masu
yawa.
Mariam Nyamwaira kwararriya ce dangane da
nau'in abinci mai gina jiki a asibitin kasa na
Muhimbili, kuma ta ce kyankyasai na iya
taimakawa jikin dan Adam fiye da yadda ake
tsammani.
Yadda kyankyasai za su iya ceton rayuwa
Kwaron da ya fi gudu a duniya
Amma da alama mutanen na da tababa dangane
da sanya kyankyasai cikin jerin abinci.
"Sunana Elizabeth. Gaskiya ba zan iya cin
kyankyasai ba, kuma ma ina tsoron su ma. Mai
zai sa in ci kyankyaso bayan ina iya samun
sinadarin protein daga nama ko kifi?"
Shi kuwa James M. cewa yake, "Lallai na taba
cin kyankyasai. Na ci su ne a yayin da nake
karatu a kasar Thailand. Dandanon su iri daya
yake da na fara. Amma na ci ne saboda
kwaikwayon al'adar mutanen Thailand, domin su
suna cin kyankyasai."
Hukumar Abinci ta Duniya, FAO, ta ce akwai
nau'in kyankyasai 4,500 a fadin duniya, amma iri
30 ne ake dauka a matsayin masu datti, kuma
hukumar ta ce sauran na da amfani ga rayuwar
dan Adam.
.
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba mungode Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
Source By Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: