Thursday 14 September 2017

An Haramtawa Shugabar Kasar Myanmar Halarci zaman MDD na shekara a Majalisar Dinkin Duniya

Tura Wannan Zuwa Ga

Shugabar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi, ba
za ta halarci babban zama na Majalisar Dinkin
Duniya da za a yi a mako mai zuwa, saboda
rikon sakainar kashin da ake zargin ta yi kan
halin da tsirarun musulmi na kabilar Rohingya,
da kuma kin daukar mataki don kare su.
Musulmi 'yan Rohingya 370,000 akai amannar
sun tserewa jihar Rakhine, zuwa makobciyar
kasar Bangladesh, tun bayan barkewar rikici a
yankin a watan da ya gabata, inda aka kona
kauyukan da musulmin ke zaune.
Majalisar Dinkin Duniya dai ta zargi gwamnatin
da zuba ido ana kokarin shafe wata al'umma
daga doron kasa.
A nasu bangaren sojojin Myanmar sun ce suna
yaki ne da 'yan gwagwarmaya na Rohingya, tare
da musanta kai hare-hare kan fararen hula.
'Yan kabilar Rohiongya marasa rinjaye na zaune
ne a jihar Rakhine da mabiya addinin Buddha
suka fi yawa, sun dade suna fuskantar cin zarafi
da gallazawar da ake yi musu.
Suna fuskantar hare-hare saboda a cewar 'yan
kasar, Rohingya ba 'yan kasa bane sun shigo
kasar ne a matsayin fatake ko 'yan cirani da
suka shigo kasar ba bisa ka'ida ba, don haka ba
za a ba su shaidar zama 'yan kasa ba.
Gaba kadan ne kwamitin tsaro na Majalisar
Dinkin Duniya zai yi zama na musamman kan
halin da 'yan kabilar Rohingya su ke ciki.
Ko Shugaba Aung San Suu Kyi ta sauya tunani?
Ana dai sa ran Mis Suu Kyi za ta shiga
tattaunawar da za a yi kan batutuwa da dama da
Majalisar Dinkin Duniya za ta jagoranta a birnin
New York na Amurka, da za a fara a ranar 19
zuwa 21 ga watan nan.
Mai magana da yawun gwamnatin Myanmar
Aung Shin, ya shaidawa kamfanin dillancin
labarai na Reuters cewa, watakila shugabar na
da batutuwa masu muhimmanci da ya kamata ta
warware da suka shafi kasar dalilin kenan da ba
za ta halarci zaman ba.
Ya kara da cewa ba ta taba jin tsoro ko karaya
kan sukar da ake mata ba, sannan babu wata
matsala da ta taso da gwamnatinta ta gagara
magancewa.
A jawabi na farko da ta taba yi wa zaman
Majalisar Dinkin Duniya a bara a irin wannan
lokaci, ta yi kokarin kare gwamnatinta kan
namijin kokarin da ta ke yi don ganin an
magance rikici da barazanar da musulmin kabilar
Rohingya ke ciki a kasarta.
Ana yabawa Shugaba Suu Kyi wadda ta taba
daukar lambar yabon zaman lafiya ta Nobel, da
kuma aka taba yi mata daurin talala na shekara
15, saboda gwagwarmayar da ta ke yi na
tabbatar da Dimukradiyya ta samu gindin zama a
kasar Burma, da gwarzuwa kuma jaruma mai
magana daya da ta samu jan ragamar kasar duk
da irin kalubalen da ta fuskanta.
Masu goyon bayan gwamnatin Mis Suu Kyi a
kasashen yammacin duniya, na sukar lamirinta a
yanzu saboda gazawa da kawo karshen rikicin
kabilanci da na addini da ke faruwa a jihar
Rakhine.
Ko a makon da ya gabata ta ce zuki ta malle ce
da kuma zuzuta halin da ake ciki a kasar.
Sauran 'yan uwanta da suka karbi lambar yabon
ta Nobel ciki har da jagoran mabiyar addinin
Buddha Dalai Lama, da Archbishop Desmond
Tutu na kasar Afurka ta Kudu, da Malala
Yousafzai, sun yi kira ga Mis Suu Kyi ta kawo
karshen kashe-kashen mutanen da ake yi a
kasarta.
Wai me ke faruwa ne a jihar Rakhine?
Kiyasi na baya-bayan nan na adadin 'yan
Rohingya da suka tsere daga muhallansu ya fara
ne daga ranar 25 na watan Agusta da ya wuce,
sakamakon hare-haren da sojoji da 'yan sanda ke
kai musu.
Wadanda suka tsere sun ce sojojin Myanmar sun
maida martani kan wadanda ba su san hawa ba
bare sauka, kan harin da wasu da ake zargin 'yan
gwagwarmaya na kabilar Rohingya ne suka kai
wasu ofisoshin jami'an tsaro.
Wani dattijo ya shaidawa BBC cewa a kan idonsa
aka hallaka dansa, da surukarsa da kuma jikansa,
daman tun wancan rikicin na farko aka hallaka
mai dakinsa.
Iyaye mata na goyo da yaro a baya, sannan jaye
da wasu, ga fagon kaya dauke akansu, cikin
gajiya da galabaita, wannan shi ne yadda
hotunan da ke yawo a shafukan sada zumunta
ke wallafawa.
Wani hoton mai tashin hankali, shi ne na wani
tsoho da kwale-kwalensu ya kafe a cikin ruwa,
ya yi shahadar dauko wasu yara uku, daya a
kafadarsa, biyu a janye a hannunsa.
A kan nuno hotunan mata zaune sun hada kai da
gwiwa, cikin tsananin bukatar taimakon ruwa da
abinci, ya yin da yara kanana mata da maza ke
zaune babu suturar kirki a jikinsu saboda an fito
cikin dimuwa da neman tudun muntsira.
Hatta jarirai ban da kuka babu abinda suke
tsanyarawa, babu suturar da ta rufe su ruf, ga
ruwan sama da ake shekawa kamar da bakin
kwarya, sannan iyayen ba su ci abincin da zai
kawo musu isasshen ruwan nonon da jariran za
su sha.
Sun ce an yi ta kai musu hare-hare babu
kakkautawa, ta inda suke ganin tamkar so ake a
share su daga doron kasa baki daya.
Sai dai babban wakilin Myanmar a Majalisar
Dinkin Duniya, ya dora alhakin abubuwan da ke
faruwa kan tsirarun musulmi na kabilar Rohingya
da ke yankin Rakhine da ya ce suna ta da zaune
tsaye, da kai wa jami'an tsaro hare-hare kuma
gwamnati ba za ta amince da ayyukan
ta'addanci ba.
Duk da cewa an tsaurara matakan tsaro a yankin
Rakhine, ta yadda 'yan jarida da kungiyoyin agaji
suka gagara isa don taimaka musu. Rashin
kyawun hanya na daya daga cikin manyan
matsalolin da ake fuskanta ta isa wurin su, sai
kuma uwa uba kankane ko'ina da sojojin
Myanmar suka yi don ganin ba a isa yankin ba.
Wakilin BBC Jonathan Head na daga cikin
tsirarun 'yan jaridar da suka samu damar shiga
Jihar Rakhine bisa jagorancin wakilan gwamnati,
ya rawaito cewa an kona kauyuakn da musulmai
ke ciki, yayin da wadanda ba a kona ba kamar
kufai babu kowa a ciki.
Mata sun zubar da kayayyakinsu, ga kayan yara
a yashe a kasa, maza sun zubar da kayan
aikinsu na noma, yayin da amfanin gonar ma an
gudu an bar shi.
Wani abin mamakin shi ne akwai jami'an tsaro
tun daga soja har 'yan sanda amma babu wani
yunkuri da suka yi na hana hakan.
Yayin da musulmin Rohingya kusan 400,000 suka
tsere daga muhallansu, Majalisar Dinkin Duniya
ta ce 'yan gudun hijira sun cika kasar
Bangladesh da tafi makobtaka da Myanmar,
sannan ko a baya kasar ta dade da daukar wasu
'yan gudun hijirar.
A halin da ake ciki wasu dubban 'yan Rohingya
su na gararanba a sansanin da aka kafa na cikin
kasar, cikin fargaba da tashin hankalin rashin
sanin makomarsu.
.
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba mungode Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
Source By Bbbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: