Thursday 14 September 2017

Farin Jinin Shugaba Muhammadu Buhari na kara disashewa a Nigeria

Tura Wannan Zuwa Ga

'Yan Nigeria sun yi lale marhabin matuka da
dawowar Muhammadu Buhari kan mulki karo na
biyu shekara daya da rabi da ta wuce tare da
saka fata mai yawan gaske a kansa.
Kusan hankalin kowa ya kwanta lokacin da ya
karbi ragwamar mulki daga tsohon Shugaba
Goodluck Jonathan - wanda ake yi wa kallon
maras katabus.
Sai dai watanni 18 bayan haka, sai ga shi 'yan
kasar da yawa na tababar ko sabon shugaban
nasu mai shekara 73 na iya shugabantar kasar
mafi yawan jama'a a nahiyar Afirka, ta yin
la'akari da girman matsalolin da take fuskanta
yanzu.
A yayin da ake jinjina wa shugaban kan kokarin
da yake na yaki da cin hanci da karbar rashawa
da kuma yadda yanzu sojojin kasar ke samun
galaba wajen yakin da kungiyar Boko Haram, a
wasu fannonin rayuwa ba wani abin a-zo-a-
gani.'Yan Nigeria sun yi lale marhabin matuka da
dawowar Muhammadu Buhari kan mulki karo na
biyu shekara daya da rabi da ta wuce tare da
saka fata mai yawan gaske a kansa.
Shugaban Buhari dai ya fada da bakinsa cewa
bai shigo da kafar dama ba saboda ya karbi
mulkin ne lokacin da farashin danyen mai wanda
kasar ta dogara kansa ya fadi kasa warwas.
Mannir Dan Ali:
"Kodayake ya kusa yin rabin wa'adinsa, har yanzu
Shugaba Buhari bai nada wasu manyan mukaman
da za su taimaka masa kai kasar inda yake burin
kai ta."
Shugabannin da suka gabata musamman Mista
Jonathan, ba su yi tsimin komai ba daga rarar
kudaden da kasar ta samu lokacin da farashin
gangar mai ke sama ga dala 100 domin irin
wannan lokacin da farashin ya fado zuwa dala 30
kacal.
Bugu da kari kuma wawasar kudaden gwamnati
ba-kai-ba-gindi ta hana kasar ajiye komai daga
cikin kudaden da ta samu ta wasu kafofin.
Kuma hatta kudaden da aka ware domin yaki da
Boko Haram wasu daidaikun mutane sun karkata
su zuwa amfanin kansu da kuma wajen yakin
neman zabe.
Buhari ya amsa cewa ya ji kamar ya gudu ya bar
mulki bayan da ya ga yadda girman matsalar
take lokacin da ya karbi mulki a watan Mayun
shekara ta 2015.
Suka daga dakin kwanansa
A yanzu hakurin wasu magoya bayansa ya fara
karewa.
Daga cikin masu sukarsa har da matarsa, wadda
ta yi wani abu da ba a saba gani ba, na fitowa ta
soki salon shugabancinsa a bainar jama'a a cikin
wata hira da BBC.
Inda ta ce ba za ta goyi bayansa ba idan ya ce
zai sake tsayawa takara a shekara ta 2019, idan
bai sauya salon mulkinsa ba.
Shi ma dai tsohon Shugaban kasar Olusegun
Obasanjo, wanda ya ba shi goyon baya lokacin
zabe, ya fito fili ya nuna adawa da wasu
manufofin gwamnatinsa daga bisani musamman
batun karbo bashi na dala biliyan 30.
''Idan ba mu gyara tsarin tattalin arziki ta yadda
zai ragewa yawancin 'yan Najeriya wahalhalun
da suke ciki ba, nasarar da aka samu wajen yaki
da ta'addanci da kuma cin hanci da rashawa za
ta zama maras amfani,'' in ji shi.
Da ma ta bangaren tattalin arzikin ne aka fi nuna
rashin gamsuwa saboda karayar arzikin da kasar
ta fada a yanzu.
Babban tushen damuwar
Karya darajar kudin kasar Naira, da hauhawar
farashin kayan abinci da kuma rasa ayyuka sun
jefa iyalai da yawa cikin kunci. Sai da kyar ne
wasu ke samu su ci abinci sau daya a rana.
Wannan ne ya sa a kwanan nan 'yan kasar na
wasu maganganu na yanke kauna ga shugaban a
shafukan sada zumunta irin wannan:
''Yanzu ba so muke Shugaba Buhari ya ciyar da
Najeria gaba ba. Muna so ne ya mayar da ita a
yadda take kafin ya zamo shugaban kasa.''
A halin da ake ciki yanzu dai yawancin 'yan
Najeriya na fatan shugaban da mukarrabansa za
su hada karfi wuri daya su fitar da kasar daga
karayar arziki mafi muni tun bayan komawar ta
kan tsarin dimokradiyya a shekarar 1999 - kana
su nuna cewa zabensa ba kuskure ba ne.
.
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba mungode Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By BBC HAUSA

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: