Wata kungiyar matasan jam'iyyar APC mai mulki
ta gargadi 'yan siyasa dake kalubalantar Minista
Aisha Jumma'ai Alhasan da cin amanar
gwamnatin Buhari.
Wannan ya biyo bayan furucin da Aisha Alhassan
din ta yi na cewa za ta goya wa Atiku baya a
zabe mai zuwa idan ya tsaya takara, lamarin da
ya sanya da dama daga cikin masu sharhin
siyasa cecekuce.
Kungiyar matasan na APC a wata takarda da ta
fitar wanda ya samu rattaba hannun sakataren ta
Collins Edwin tace babu wani laifi da aka samu
ministan dashi a akan gabatar da ayyukan ta da
kuma gwamnatin da take yiwa aiki.
Takardar ta cigaba da cewa: "Idan har Aisha ta
yasar da Atiku Abubakar wanda shine
ubangidanta a siyasa, to hatta Buhari zai yi
mamaki lura da yanda alakar siyasar su take da
Atiku."
Kungiyar ta yabawa Aisha Alhassan bisa bayyana
ra'ayin ta, inda kungiyar tace ba karamin abu
bane yin hakan a siyasar kasar nan da kowa yake
yasar da ubangidansa saboda mukamin
gwamnati.
Kungiyar tace tana gargadin masu amfani da
wannan saboda shafawa jam'iyyar su ta APC
bakin jini.
Kazalika kungiyar tace har yanzu shugaba
Muhamamdu Buhari bai tabbatar da tsayawarsa
takara ba a zabe mai zuwa idan Allah ya kaimu.
. .
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address dinba mungode
.
Source By Bashir Abdullahi El-Bash
Tuesday 12 September 2017
TURA WANNAN ZUWA GA
Mawallafi: MURYAR HAUSA24 ONLINE MEDIA verified_user
0 comments:
Post a Comment