Tuesday 12 September 2017

Takaitaccen Tarihin Sheikh Abubakar Mahmoud Gumi

Tura Wannan Zuwa

An haifi Shaikh Abubakar Mahmud Gumi ne a
cikin garin Gumi dake jihar Sokoto, a shekara ta
1340 bayan Hijira dai dai da shekarar Miladiyya
1922.
Malam ya tashi ne cikin kyakkyawar tarbiyya
da natsuwa da tsafta da neman Ilimi karkashin
kulawar mahaifin sa (Alkalin Gumi a wancan
zamanin).
Haka kuma marigayi Sheik Gumi ya yi karance-
karance na zaure a majalisi daban-daban na
Malaman da suka shahara a kasar Hausa a
wancan lokaci, tare da karatu na nizamiyya daga
nan kasar har kasar Sudan da kasar Saudi
Arabiya.
Shaikh Abubakar Gumi mutum ne mai kokarin
binciken Al-kur'ani da Sunna kan hukunce-
hukuncen Shari’a, tun daga abin da ya shafi
Tauhidi, Hadisi, Fikhu da luggar Larabci, wanda
karantarwar da ya yi ta tabbatar da haka.
Malam ya yi rubuce-rubuce masu yawa, kadan
daga cikin su akwai:- *Al Akeedatus Saheehah bi
Muwaafakatish Shari’ah
*Tarjamar Ma’a’nonin Al-kur’ani Mai Girma.
Tafsirin Al-kur’ani:
*Raddul Azhaan ilaa Ma’aanil Kur’an.
*Tarjamar littafin Hadisin “Arba’uunan
Nawawiy”
Littafi mai suna *Manufata” ko (Where I
Stand).
Wannan littafi ya na da matukar amfani ga sanin
tarin siyasar kasar nan da ta shafi Addini da
Mulki da sauransu.
Sheik Gumi ya rasu ne a ranar 11 ga watan
Satumba, 1992.
.
Allah ya jikan Malam, ya gafarta masa da sauran
Musulmi. Amin
.
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address dinba mungode Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Source By Bashir M. Suleiman

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: