Sunday 17 September 2017

MAZA MAGANIN MAZA:Takaitaccen tarihin Janar Murtala Ramat Mohammed

Tura Wannan Zuwa
 haifi janar Murtala Ramat Muhammed ranar 8 ga
watan Nuwambar shekarar 1938 a garin Kano, ya
yi karatu a kwalejin Barewa dake Zaria.


A
shekarar 1959 ya shiga aikin soji, inda yayi
karatu a makarantar sojoji ta Royal Military
Academy ta Sandhurst dake Burtaniya.
Janar
Mutala ya samu mukamin Laftanal a shekarar
1961.Gabanin komawarsa Najeriya a shekarar
1962, ya je rangadin aiki a kasar Congo a
matsayin wani wakilin dakarun wanzar da zaman
lafiya na Majalisar dinkin duniya.A shekarar 1964
ya ka bashi mukamin Manjo na wucin gadi,
bayan da aka bashi ragamar kula da sashin
sadarwa a hedkwatar rundunar soji ta
Kaduna.

Janar Murtala ya koma Lagos inda ya
zauna tare da kawunsa Alhaji Inuwa Wada a
lokacin da aka bashi ministan tsaro, kuma ya
kasance a can har lokacin da akai juyin mulki na
farko a shekarar 1966.

Shugaban kasa manjo
janar Aguiyi-Ironsi ya kara masa girma zuwa
Laftanal Kanal koda yake shima na wucin gadi
ne, a watan Afrailun shekarar 1966.Bayan juyin
mulki na farko, sau uku janar Murtala ke neman
hada kan sojojin arewa dake Lagos domin ayi
juyin mulki na biyu, sai dai wannan yunkuri bai yi
nasara ba bisa harbe wasu sojoji da akayi a
Abeokuta.
Janar Murtala Ramat Muhammed ya
taka rawar gani a yakin basasar da akai a
shekarar 1967 lokacin da Laftanal Kanal Ojukwu
ke neman balle yankin Biafra daga Najeriya.A
wannan lakacin janar Murtala ya jagoranci
rundunar sojin da suka murkushe sojojin Biafra
tare da kawo karshen yaki basasar baki daya
kamar yadda ya bada sanarwa a ranar 21 ga
watan Satumbar shekarar 1967.

Yana matsayin
birgediya ne sojojin da sukayi juyin mulki na uku
a Najeriya suka nada Murtala a matsayin
shugaban kasa , inda a watan Janairun shekarar
1976 aka kara masa girma zuwa janar mai anini
hudu, wato kololuwa kenan.

Har ila yau a wannan
lokaci ne janar Murtala ya kirkiro da sabbin
jahohi 7 ya kuma bayyana bukatar mayarda
babban birnin Najeriya zuwa Abuja da kuma
alkawarin mika mulki ga fararen hula a shekarar
1979.

©Muryarhausa24.Com.ng"To masu iya magana kance kana taka Allah
na nashi, ranar 13 ga watan Fabrerun sojoji
karkashin jagorancin Dimka sukayi yunkurin kifar
da gwamnatin sa yunkurin da bai nasara ba, illa
dai kashe-kashen da akayi, inda suka budewa
motar janar Murtala Ramat Muhammed wuta a
lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa ofis".
Bayan
mutuwarsa an nada mataimakinsa laftanar janar
Obasanjo a matsayin shugaban kasa.
Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishadi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHADANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika sakon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com za muyi farin ciki da samun sakon ka/ki Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user