Saturday 16 September 2017

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903

Tura Wannan Zuwa

GABATARWAR
Muhammad Sani Umar
Da
John Hunwick

A wani lokaci a shekarar 1902, wani matashi mai
suna Abdullahi ya riski kano daga arewa, ana
tsammanin daga Ghadamus yake. Bamu samu
labarin komai dangane da dalilin zuwan saba, da
kuma danginsa, amma dai wannan labarin daya
rubuta na daga madogarar mu dangane da
labarin nasa.

Domin acikin labarin ne ya bayyana kansa a
matsayin ɗalibi, amma ba'a fuskanci a
takamaimen fannin da yake ɗalibtar ba, domin
babu wata alama dake nuna yazo kano ɗaukar
karatu a gurin masana, amma mun samu labari
cewa wasu shekaru da suka shuɗe yayi aikin
tafinta ga kawunsa na wajen mahaifi dake zaune
a kano, wanda hujjoji sun tabbatar da cewa
balaraben Ghadamus ne da kasuwanci ya kawo
shi kano.
Abdullahi Al Ghadamasi ya riski kano watanni 8
kafin turawan mulkin mallaka su riski kano, har
su cita da yaki a shekarar 1903. Don haka muna
iya cewa shi ganau ne ba jiyau ba akan yadda
yakin ya kasance.
Haka kuma, bamu samu komai dangane da hakan
ba sai a wajajen shekarar 1907, zuwa 1908
sanda Abdullahin ya amsa kiran C.L Temple na
neman wanda zai taimaka masa a fannin tafinta
masanin Arabi da Hausa. A wannan lokaci C.L
Temple na kokarin tafiya hutu ne burtaniya,
watakila bayan ya kammala ayyukansa a sokoto
kenan a watan janairun 1908.
Koda yake, ance aikin Abdullahi da Temple baiyi
tsawo sosai ba sabili da yadda akace an nusar
da Temple cewar akwai rashin gaskiya/cushe a
aiyukansa na fassara.
Babu Jimawa ne kuma akace Abdullahi
Alghadamasi ya shiga aiki da H.R Palmer, wanda
a lokacin babban aikinsa shine tattara haraji
daga loko da sakunan kasar kano.
Kuma kamar yadda muka fahimta, Palmer yayi
mu'amala dashi saɓanin yadda Temple yayi dashi
ta hanya mai kyau harma yana yawan godiya
gareshi. Kai, muna iya cewa ma babu shakka,
Abdullahi ne matashin da Palmer yake nufi da
'matashin balarabe' a farkon littafinsa na sunayen
sarakunan kano mai suna 'Kano chronicle' wanda
yace ya ɗauka aiki, har kuma yana iya fahimtar
larabcin Tripoli dana Ghadamus.
Sannan, Babu takamaimen dalilin daya sanya
Abdullahi Alghadamasi ya rubuta wannan tarihi,
amma tana ita yiwuwa Palmer ne ya karfafe shi
yayi. Haka kuma bamu da takamaimen sanin
halin da Abdullahi ya cigaba da kasancewa bayan
Palmer ya tafi hutu Burtaniya. Koda yake, ance
Palmer yayi nufin tafiya tare dashi Burtaniya
ɗinma, amma yayin da suka riski Birnin Ikko, Sai
Abdullahi ya karaya, har ya yanke shawarar bazai
iya jure doguwar tafiya cikin teku ba.
Don haka, samun wannn tarihi muna iya cewa
abu ne mai kyau a garemu, domin mahangan da
tarihin ya kalla. Da fari dai, Abdullahi yana cikin
kwaryar kano turawa suka zo, don haka ya gani
kuma yaji abinda zai iya bada labari akansa.
Sannan kuma tarihin ya kalli kasar hausa daga
fuskar turai, tunda yayi aiki da turawan harma
turawan sun gyara masa wasu aiyukan nasa.
Yadda Turawa Suka Riski Kano.
Ali ɗan Abdullahi Alfallati (Aliyu Babba Zaki) ne
sarkin kano na wannan lokaci, kuma yana kan
mulki sai labarin yaki ya zowa wannan gari.
Ali, sarkin wannan gari yana sane da labarin yaki.
Amma sai yayi shiru bai yayata ga jama'a ba.
A lokacin da tsoro ya cika masa zuciya, sai ya
tattara amintattun sa, sannan yace musu "Kuyi
sani yaku jama'a, nayi niyyar yin tafiya zuwa
sokoto. Don haka waɗanda duk sukayi biyayya
dani suna iya bina wannan tafiya"
Daga nan sai ya shiga tattara jagororin yakinsa,
da manyan jarumansa da barori, ya sanar musu
da shirinsa na tafiya sokoto domin ziyartar iyaye
da kakanninsa. Don haka a iya watanni biyu suka
kammala shiri.
Da lokacin tafiya yayi, sai sarki Ali ya kira
yaronsa mai lakabin Sarkin Shanu, yace masa "Ya
kai sarkin shanu, lokacin tafiya sokoto ziyartar
iyaye da kakanni na yayi. Gashi kuma kai zan
dankawa kasarnan a hannunka ciki da kewayenta
da dukkanin hakimanta. Wannan mukamine dana
sanya a hannunka, don haka kayi kokarin rike shi
da amana da kuma gaskiya. Kuma na sanar da
Ma'aji Usmanu ya tallafeka wajen tsare wannan
birni, tare da larabawa mazauna mutanen Tripoli
da Ghadamus.
Idan wani abu ya faru abirni, ko makiya suka zo
daga ko ina, to ina umartarka kayi aiki da
nutsuwa, kuma ka nemi shawarar larabawan nan
wajen yanke hukunci.
Bayan nan kuma, sai ya sake kiran Ma'aji
Usmanu yayi magana dashi da cewa "Kayi sani
ina shirin tafiya sokoto ziyartar iyaye da
kakannina. Kuma na sanya kasarnan a hannunka
dakai da Sarkin Shanu. Idan wani abu ya auku a
birni, ko ka samu labarin zuwan makiya daga ko
ina, to kuyi aiki da nutsuwa tare da larabawan
nan mazauna birnin nan. Kunga muna da iyali,
bayi da tarin dukiya, don haka ku nemi shawarar
su don samun sahihiyar mafita, lalle ne suƴ
mutane ne masu ingantacciyar fahimta.

Saboda haka kada kayi watsi da ra'ayinsu. Ni
yanzu zan tafi. Idan Allah Ubangiji ya tabbatar
zan bar gari ranar 4 ga watan shawwal
( shekarar 1320 kenan, dai-dai da 3-1-1903.)
Ita kuwa kofar kansakali. Kada ku rufeta domin
tanan zamu rinka sadar da manzanni a tsakanin
mu.
Sarkin kuma ya sake shaidawa Sarkin shanu
cewa "Kai wakili nane, don haka duk abinda ya
faru bayan rabuwar mu ka sanar dani ta hanyar
wasika, kuma kada ka bari aike ya tsaya a
tsakaninmu daga gareka da ma'aji. Amma
lamurorin sharia, sai kubar su a hannun Alkali, ku
kuma kuji da abubuwan da suka shafi Sarauta.
Don haka, idan Allah ya dawo damu kano lafiya,
muka sameku kunyi aiki da nagarta kun cika
umarninmu, to hakika zan saka muku da abinda
zai faranta muku zuciya. Ku sani Allah Ta'ala
yace 'babu abu mafi kamantuwa da sakayya ga
alheri sai alheri' (Q 55:60). Allah ya haɗa
fuskokinmu da alheri Amin
..
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine Farn Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Source By SADIQ TUKUR GWARZO

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: