Saturday 16 September 2017

ALLAH yayiwa Lil Ameer fitaccen Mawaki kuma Matashin Hip Hop Rasuwa

Tura Wannan Zuwa

Hakika masana’antar nishatarwa ta Arewa tayi
babban rashi da rasuwar dan matashi mawakin
hausa hip hop, amma indai ajalin mutum ya
kai babu wanda zai iya kubutar dashi.
Ameer Isa Hassan ya rasu ranar 14 ga watan
Satumba a garin Kano sanadiyar hatsarin
mota. Anyi jana’izar shi ranar juma’a a layin
massalacin juma’a na tarauni.

ga wandada basu san labarin wannan matashin

Ga abubuwa 5 da ya kamata ku sani;
1. Haifafan Dan jihar kano ne
An haifi marigayi Ameer a cikin 2003 a jihar
Kano

2. Har zuwa lokacin rasuwar sa mawakin yana
koyan darasi a makaranta
Duk da kasancewar shi wanda ya fara shahara
a harkar wakoki marigayi bai bari harkar ta
dauki hankalin shi wajen koyan darasi. ya kan
tafi makarantar boko kuma idan ya tashi yaje
na islamiyya. sai karshen mako yake samun
damar yin aikin waka. babban burin marigayi
shine in ya gama karatu ya zama matukin jirgin
sama.

3. Iyayen sa sun mara mai baya
hakika iyayen suka bashi damar fara waka
kuma uwar take taimaka masa wajen rubuta
wakokin.
Ameer ya canza makarantu domin masoyan sa
sukan tunkare shi idan yana koyan darasi.

4. Ya fara waka tun yana jjs 1 na makarantar
sekandare
matashin ya fara waka ne domin tun yana dan
karami yake muradin waka. ya fara waka ne
domin ya nuna ma duniya cewa matasa daga
yankin arewaci kasar nan na iya rera waka
kuma su yi nasara.

5. Yayi wakoki da dama kuma yayi wasa tare
da sauran shaharren mawaka
cikin wakokin da marigayi yayi akwai “boss”,
“champion”, “ilimin boko da addinin musulunci”,
“dance for me” da dai sauran su.
Matashin wadda ake wa lakabi “karaminsu
babbansu” yayi waka tare da shaharraru da
dama kuma yayi wassanni da dama a wurare
daban-daban

.
.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayoyin Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum farin cikin Ku shine Farn Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com ALLAH yabar Zumunci Amin
.
.
Allah ya jikanshi da rahama, Ameen
.
.
Souce By ©Pulse Hausa Nigeria

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: