Saturday 23 September 2017

Najeriya ta na cikin barazana - Buratai

Tura Wannan Zuwa Ga

Shugaban hafsin sojin kasa na Najeriya
Laftanar Janar Tukur Buratai ya bayyana
cewa, ya kamata a hankaltu domin kuwa
akwai kalubalen barazanai da Najeriya ta
ke fuskanta a hanlin yanzu.

Janar din ya bayyana hakan ne a ranar
Jumma'ar da ta gabata yayin ganawa da
manema labarai a babban birnin
Fatakwal, inda ya bayar da dalilai na
gudanarwar dakarun sojin ta
'Murmushin Kada' da kuma 'Rawar
Damatsiri' a yankunan Kudu dake kasar
nan.

A yayin ganawar ta sa a taron manema
labarai da aka gudanar a babban birnin
Fatakwal dake jihar Ribas, Buratai
wanda babban soja mai kula da
harkokin yankin na Fatakwal Manjo
Janar Enobong Udoh ya gabatar da shi
ya bayyana cewa, dalilin gudanarwar
dakarun soji ta Murmushin Kada da
Rawar Damtsiri ta biyu shine don
magance kalubalen ta'addanci, garkuwa
da mutane da kuma fasa bututun mai.

Ya kuma ce dalilin gudanarwar 'Mesa' a
jihohin Arewa da kuma jihohi bakwai
da ke tsakiyar Najeriya shine don kawo
karshen sace-sacen shanu, rikicin
makiyaya da kuma satar mutane da
neman kudin fansar su.
Naij.com ta ruwaito kalamansa, "Kasar
mu ta na fuskantar kalubale na
barazanai daban-daban kama daga,
rikicin Boko haram a Arewa maso
Gabashin kasar nan, fashi da makami,
tsafe-tsafe na kungiyoyin asiri, satar
mutane da garkuwarsu, satar danyan
mai, fashe-fashe na butun mai, rikicin
makiyaya, tayar da kayar baya na
kungiyar IPOB da makamantansu".

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Isma'il Ishaq

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: