Sunday 24 September 2017

'Yar Nigeria ta shiga jerin mawakan da ke tashe a Amurka

Tura Wannan Zuwa Ga

Wata mawakiya 'yar Najeriya, Simi Ogunleye ta
kafa tarihi, bayan ta shiga jerin mutanen da
wakokinsu ke tashe a jadawalin wakokin da suka
yi fice na Duniya a Amurka.

Da take zantawa da Sashen BBC Pidgin, Simi ta
ce: "da ma na san za a rina, hakan kuma na
nufin cewa kasuwata za ta bude kenan.

Ba zan taba sauya salon kidana ba, don kuwa shi
ne mafarin duk wata daukaka da na samu
yanzu."

Simi Ogunleye dai na gauraya Ingilishi da
Yarbanci ne a cikin wakar tata mai taken 'Belle
Sweet'.

Ta kuma yaba wa masu sha'awar wakokinta, don
kuwa a cewarta "su ne suka kai ni duk matsayin
da na samu kaina yau a cikinsa, su ne suka rika
yayata kundin wakokinta, ba zan taba ba su
kunya ba."

Simi na daya daga cikin fasihan mawakan Afirka
da suka samu shiga sahun mawakan duniya, inda
wakarta ta samu gurbi na biyar a fitattun
wakokin da suke tashe cikin jerin Billboard
Charts.

Shi ne kudin wakokinta na farko da ta sanya wa
lakabin "Simisola".

Simisola ta fara waka ne da wakokin bege a coci,
kafin ta shiga wasu wakokin a shekara ta 2014,
lokacin da ta fitar da wakarta ta farko mai taken
"Tiff and E no go funny."

Bayan wake-wake, Simi tana kuma harkar kade-
kade.

Ana la'akari da adadin kwafen kundin waka nawa
aka sayar cikin mako a fadin duniya, don sanya
waka a jadawalin wakokin da suke tashe na
Billboard Chart.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Al'ummar Nigeria  daga N50 zuwa abinda yasamu duk zaku iya turo da Lambobin katin  ta Email din mu akan officialdadinkowa24@gmail.com  ko Neman Account Number din mu na Bank ga mutanen dabasa cikin Nigeria, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com 
.
Suna addreshin misali..
.
Subject: Fatan Alheri
Suna: Yusuf Tk
Kasa: Nigeria
Gari: Kano
Garin da akeda Zama: Kaduna
Sako: Yaushe Ne zaku cigaba da Labarin Kundin Tsatsuba Littafi na 2 na Madakin Gini? Mungode
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: