Monday 2 October 2017

Akwai Bukatar Yin Gyaran Fuska a Wasu Fannonin Kasar Najeriya – Ahmad Joda

Tura Wannan Zuwa

A dai-dai lokacin da kwamitin da jam’iyyar APC
ta kafa ke gudanar da taron jin ra’ayin jama’a
game da batun sake fasali da zamantakewa da
kuma siyasar Najeriya a fadin tarayyar kasa,
wasu dattijai na ganin kasar ba zata rabu ba.

Tsohon dattijo Ahmad Joda, ya ce Najeriya ba
zata rabu ba, ganin irin gwagwarmayar da rikita-
rikitan da aka sha a baya, daga yakin basasa har
zuwa rikicin 12 ga watan Yuni, amma har yanzu
kasar a dunkule take wuri guda.
To sai dai kuma, Ahmad Jodan wanda shi ya
jagoranci kwamitin da shugaba Buhari ya kafa
domin duba hanyoyin tada komadar kasa, na
ganin akwai bukatar gyaran fuska a wasu
fannonin, inda yayi kira da a kirkiro da
gundumomin da jama’a zasu amfana maimakon
mazabun majalisar dattawa da ake da su yanzu
domin magance koke-koke da matsalolin da
jama’a ke ciki.

Tun farko da yake yaye kallabin taron na jihohin
Adamawa da Taraba, gwamnan jihar Adamawa
Sanata Muhammadu Bindow Umaru Jibrilla, ya
ce koda yake akwai bukatar samun gyara a wasu
fannoni da kason da ake baiwa jihohi da kuma
samun yan takara masu zaman kansu to amma
al’ummar jihar basu goyi bayan duk wani yunkuri
na raba kasar ba.

Batun sake fasalin kasar na ci gaba da janyo
cece-kuce, inda wasu ke ganin bai dace ba, yayin
da wasu kuma ke ganin dacewarsa.
Da yake bayyana ra’ayinsa tsohon mataimakin
shugaban kasa Atiku Abubakar ya ce akwai
bukatar duba wasu batutuwa.
Kawo yanzu tuni har wasu yankuna suka dau
matsaya, yayin da watanni uku kwamitin da APC
ta kafa zai kwashe yana gudanar da aikin ji da
kuma tattara ra’ayoyin jama’a kan wannan batu.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By © Ibrahim Abdul' aziz Sarfilu Gumel

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: