Monday 2 October 2017

Kasar Amurka Ta Taya Najeriya Murnar Cika Shekaru 57 Da Samun ‘Yancin Kai

Tura Wannan Zuwa Ga

Najeriya na bikin cika shekaru 57 da samun
'yancin gashin kanta daga turawan mulkin
mallaka na Birtaniya a daidai lokacin da Amurka
ke jaddada shirinta na tallafawa kasar wajen
yaki da kungiyar Boko Haram.

Sakatare harkokin wajen Amurka Rex Tillerson,
ya jaddada kudurin kasar na taya Najeriya yaki
da kungiyar Boko Haram da kuma rassan
kungiyar ISIS da ke yankin yammacin Afirka.
Tillerson ya kuma bayyana shirin Amurkan na
tallafawa gwamnatin Najeriyar agazawa miliyoyin
mutanen da rikicin na Boko Haram ya shafa
domin su koma rayuwarsu ta da, tare da samar
da makoma ta gari ga daukacin kasar.

Sakataren harkokin wajen Amurka, ya bayyana
hakan ne a wata sanarwa da ya fitar, wacce
Muryar Amurka ta samu, kan taya Najeriya
murnar cika shekaru 57 da samun ‘yancin gashin
kai, yayin da kasar ke bikin a yau daya ga watan
Oktoba.

“Muna taya al’umar Najeriya murnar cika shekaru
57 da samun ‘yancin gashin kai.” Sanarwar ta
bayyana.

Tillerson ya kara da cewa dangatakar Amurka da
Najeriya, an gina ta ne akan muhimman tubalan
da suka shafi tsaro da tattalin arziki da mulki na
gari da kuma zimmar samar da kyakkyawar
makoma.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Voa Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: