Sunday 22 October 2017

SHARHI AKAN FIM DIN "OMAR SERIES". (TARIHIN SAYYADINA UMAR R.A)

Tura Wannan Zuwa Ga

Tin  a shekara ta 2012 ne, gidan talabijin din MBC suka nuna wani fim mai dogon zango wanda suka kira da suna "Omar Series".

Fim din ya nuna takaitaccen tarihin Sayyadina Umar R.A tun yana shekaru 18 har izuwa lokacin da yayi wafati, a zahirin gaskiya sunyi matukar kokari wajen kwatanta wannan tarihi, domin kuwa an bibiyi tarihi sau da kafa, kuma anyi abin bajinta a wannan shirin.

Fim din wanda suka rabashi kaso 30 (30 episode), kowanne daya daga ciki kuwa kusan minti 45 ne zuwa 50, (sannan kuma a memory card yakai kimanin 4GB gaba dayansa), ya bayyana tarihin garin Makkah kafin aiko Manzo Allah S.A.W, lokacin aikoshi, wahalar da musulmai suka sha a wancan lokacin, hijirarsu zuwa Habasha, musuluntar Sayyadina Hamza da Sayyadina Umar, dawowar musulman da sukayi hijira daga Habasha, shekarar bakin ciki, hijira izuwa Madina, ginin Masallacin Annabi, yakin badar da yakin uhudu, yakin khandaq da Banu kuraiza.

Fim din yaci gaba har izuwa wafatin Manzon Allah (S.A.W) da kuma abinda ya biyo baya wanda yayi sanadiyar zaman Sayyadina Abubakar R.A khalifa na farko, daga nan har izuwa wafatinsa shima da kuma zaman Sayyadina Umar R.A khalifa na biyu, da yakukuwan da suka faru a zamaninsu wanda suka hada da yakin ridda, yakin Musailama, yakin Farisa (wanda akayi a giwaye), yakin Damashka (wanda akayi da igwar yaki) da makamantansu.

<font color="black">BAJINTA A CIKIN FIM DIN</font>

Baya ga tarihin musulunci da tarihin Sayyadina Umar R.A, fim din a 6angare guda kuma ya nuna tarihin mutane kamar:

-Sayyadina Abubakar R.A
-Sayyadina Usman R.A
-Sayyadina Aliyu R.A
-Abu-Ubaida Bin Jarrah R.A
-Sa'ad Bin Abi-Wakkas R.A
-Zaidu Bin Khattab R.A
-Abdullahi Bin Suhail R.A
-Abu-Jandal Bin Suhail R.A
-Suhail Bin Amr R.A
-Salamatu Bin Hisham R.A
-Ayyash Bin Rabi'ah R.A
-Bilal Bin Rabah R.A
-Ammar Bin Yaasir R.A
-Wahshi R.A
-Hamza Bin Abdulmuttallib R.A
-Abbas Bin Abdulmutallib R.A
-Sa'ad Bin Mu'az R.A
-Abu-Huzaifa Bin Utbah R.A
-Salim Maula Abu-Huzaifa R.A
-Ikramata Bin Abu-Jahal R.A
-Safwan Bin Umayya R.A
-Khalid Bin Walid R.A
-Walid Bin Walid R.A
-Abdullahi Bin Umar R.A
-Qaqa'u Bin Amr R.A
-Abu-Sufyan Bin Harb R.A da matarsa Hindu
-Amru Bin Al-as R.A
-Umair Bin Wahab R.A
-Abu-jahl L.A
-Utbatu Bin Rabi'ah L.A
-Abu-Lahab L.A
-Walidu Bin Mughira L.A
-Umayyatu Bin Khalaf L.A
-Da sauransu masu yawa.

Babban abinda ya kara birgeni da fim din shine, duk da cewa an yishi ne cikin harshen larabci, amma anyi masa fassarar wasu yarukan kamar turanci, urdu da sauransu, sannan kuma yana nan a "you tube" har yanzu.

MATSALOLIN DA FIM DIN YACI KARO DASU.

-Fim din ya fuskanci kalubale ta fuskar nuna wasu mutane guda hudu da yayi a matsayin "Khulafa'ur Rashiduna".

-Matsala ta biyu ita ce yanda aka nuna alaka tsakanin mutumin da ya fito a matsayin Abu-Sufyan da matarsa, da kuma mutumin da ya fito a matsayin Sayyadina Umar da kanwarsa Fatima Bintu Khattab.

-Matsala ta uku ita ce ba'a nuna karshe wasu mutane ba a fim din, duk da cewa fim din ba wai ya ginu bane akan tarihinsu.

-Abu na hudu kuwa shine yadda aka ringa ambatar sunayen wasu mutane a fim din, amma ba'a nunasu ba.

RA'AYINA AKAN FIM DIN

A zahirin gaskiya fim din ya kayatar dani matuka, kuma na tabbatar da cewa zai kayatar da dukkanin wanda ya kallashi, domin kuwa ya tattara takaitattun bayanai masu matukar muhimmanci wanda ya kamata ace kowanne musulmi ya sani.

Allah ya tarfa mana albarkacin Sahabban Manzon Allah (S.A.W)

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don ganin sabbin posting din Mu se ku duba saman website din akwai "Home" sai ku shiga, mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com

Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin🙏

Source By  ©Abba Ahmad Gwammaja

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: