Monday 2 October 2017

TSAYA KA DAURE KA KARANTA AKWAI FA'IDA A CIKIN SA

Tura Wannan Zuwa

Wata rana a makarantar manya malamin koyar
da sanin halayyar dan Adam (Psychology),​ ya
shiga aji yace "yau zamu yi wani wasa", "me?
wasa".
Malam yace a cikinku wa zai fito gaban allo a
fara da Shi?
Sai wata daliba Salma ta fito, Sai malam yace ta
dauki alli (chalk) ta rubuta sunan mutane 30
masu muhimmanci a rayuwarta, Salma ta rubuta
dangi, kawaye, abokan karatu da makwaftanta.
Sai malam yace ta goge 3 wadanda basu da
muhimmanci sosai a wajenta, Salma ta goge
suna 3 na abokan karatunta.
Sai malam yace ta kara goge 5 marasa
muhimmanci, Salma ta goge makwaftanta,
Malam yayi ta umartarta tana gogewa har sai da
ya rage sunaye 4 ka dai sune:-
1. Babarta
2. Babanta
3. Mijinta
4. Ɗanta 1 data haifa.
Gaba dayan dalibai sai suka natsu sun gane
cewa wannan ba wasa bane kamar yanda Malam
ya fada da farko, yazo musu ne da wani darasi
mai muhimmanci.
To! Sai malam ya kalli Salma yace ta kara goge
2 daga sunayen nan da suka rage, wannan zabin
fa yana da wuya, Salma tayi jimmm! Hannunta
yana rawa ba'a son ranta ba idonta ya cika da
kwalla ta goge sunan Babarta da Babanta.
Sai malam yace ta kara goge 1, Sai Salma ta
saka kuka ta goge sunan Ɗanta 1 Tilo Sai malam
yace ta koma wajenta ta zauna.
Bayan wani ɗan lokaci sai malam yayi tambaya,
yace:- " me yasa ta bar mijinta"?
Yace: Iyaye fa sune suka kawo ki duniya suka
raine ki har kika girma, Ɗanki kuma ke kika yi
cikinsa kika sha wahalar laulayin cikin kika haife
shi, kika raine shi, kuma da Iyaye da Da ba zaki
iya sake wadansu ba, amma miji ko yaushe zaki
iya chanja wani.
Aji akayi shiru ana jiran amsar Salma, Salma
cikin nutsuwa da sanyin murya tace:-
"Wata rana iyayena ina tare dasu suka dauke ni
suka kaini gidan miji, idan na kawo musu ziyara
sai su tambayeni, "lafiya"?
Idan yayi min laifi na taho gida sai su kira shi
suyi ta bashi hakuri, suce na tashi na koma
gidansa".

Ɗa na kuma wata rana zai barni idan ya girma zai
mai da hankali kan sana'arsa da hidimar iyalinsa,
Mutum 1 wanda zai kare rayuwarsa tare da ni
shine MIJINA,​ kuma...... Kafin ta kara magana
sai dalibai suka dauki tafi gaba daya saboda ta
fadin gaskiyar yanda rayuwa take.
Sai malam yace:- "Gaskiya ne, Allah ya sanya
aure a tsakanin Miji da mata ya zama
dangantaka ta tsowon rayuwarsu, Ko yaushe ka
girmama abokin rayuwarka (Miji ko Mata).
Allah ya sanya Miji da Mata su zama Abu 1
Kamar yanda yazo a cikin Al- qur'ani mai tsarki,
Allah yana cewa:- "yana daga cikin ayoyinsa ya
halitta muku matayenku daga jikinku, don ku rayu
dasu, ya sanya a tsakaninku soyayya da jin kai,
hakika a cikin wannan akwai aya ga ma'abota
tunani".
Don haka ku (Ma'aurata) ku zaku saka wannan
dangantaka ta zama sama da kowace
dangantaka a duniyar nan Kafin mutum yayi aure
Allah da Manzansa sune a farko sannan dangi,
bayan kayi aure Allah da Manzansa suna farko
Miji/ Mata sune na 2 Sannan dangi. Ma'aurata ya
zama wajibi ku baiwa Aurenku abinci ya girma
yayi karfi, abincin kuwa shi ne bin dokokin Allah,
Gaskiya, rikon amana, Hakuri, Zaman lafiya
Soyayya da Nishadi.

ALLAH KASA MUDACE
DUNIYA
DA
LAHIRA

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Fadila M. Idris

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: