Monday 2 October 2017

SHIN KO KASAN CIKAKKEN TARIHIN MARIGAYI RABILU MUSA DAN (IBRO)???

Tura Wannan Zuwa

An haifi marigayi Rabilu Musa
Ibro a shekarar 1971. Ya yi
karatun Firamare dinsa a
Danlasan da ke cikin karamar
hukumar Warawa. Sannan kuma
ya yi Sakandare a Kwalejin horon
malamai ta Wudil (Teachers
College). Daga nan ne ya shiga
aikin gidan Yari (Prison Service)
a shekarar 1991. Ya yi shekara
takwas Ya na aikin Gandiroba
inda ya kai matakin insfekto,
daga nan ne ya bari ya cigaba da
sana’ar wasan kwaikwayo.
Rabilu Musa Ibro ya fara sana’ar
Fim a tun ya na aji uku na
makarantar sakandare. Ya na da
Mata da Yara hudu ko uku
akwai : Jamila, Kubra, Auta.

Daga cikin yaransa akwai: Akwai
Faisal, Jawahid, Lawiza, Abdul-
Mummuni, Sannan akwai
Asma’u, Annabe, Sa’adiyya,
Akwai wani yaro kuma da ya
Haifa ya sa sunan mai gidansa
wato Baba Yaro.

Kafin Rasuwarsa Ya bayyana
Ciroki a matsayin dan wasan
hausa abokin sana’ar sa da ya fi
burgeshi.

Da aka tambayi Rabilu Musa ibro
dan wasan santimental da ya fi
burgeshi sai yace “ Adamu
Usher, ka ga wannan, yana bani
sha’awa. Saboda ba shi da
girman kai, ba zan manta ba
lokacin rasuwar kulu da Yautai,
tun daga farkon rasuwar mu na
tare da su.” In ji Ibro

Daga cikin dubunnan fina finansa
ibro ya bayyana cewa ya fi son
wadannan fina finai “Akwai
Kauran Mata, Kowa Ya Debo Da
Zafi, da kuma Mai Dawa.

Ibro ya bayyana ya fi son tuwon
dawa a bangaren abincinsa,
fannin sutura kuma sai yace “Na
fi son yadi wanda zan shekara da
shi ina gurzawa, ba in sa Shadda
ba kwana biyu in ga tana
kodewa.

Da aka tambayi Marigayi Ibro a
lokacin ya na raye me ya fi
bakanta masa rai a kan harkar
sana’arsa sai yace“ Ni abinda
yake bata mani rai kawai a
wannan sana’a bai wuce rashin
hadin kan ‘yan wasa ba.

Rabilu Musa Ibro Ya amsa kiran
mahallicinsa ya na da shekaru
43, a duniya. Allah ya kyautata
makwanci.
Ameeeeeeeeeeen

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Bashir M. Suleiman

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: