Monday 2 October 2017

WAJIBI NE GA DUKKAN MUSULMI SU YI WA MUSULMIN KASAR BURMA ADDU'A

Tura Wannan Zuwa

1. Mafi karancin abin da daidaikun Musulmi za su
yi wa Musulmin Kasar Burma (Myanmar) shi ne
addu'ar Allah Madaukakin Sarki ya kubutar da su
daga hannun azzaluman mahukuntan Kasar
Burma, da kuma hannayen azzaluman talakawan
Kasar Burma.

2. Kasar Burma (Myanmar) wacce take Kudu
Maso Gabacin Asia (Southesat Asia), wacce take
iyaka da India da Bangladesh ta yammacinta,
take kuma iyaka da Thailand da Laos ta
gabacinta, take kuma iyaka da China ta
arewacinta da kuma arewa maso gabacinta, take
kuma iyaka da hannun tukun Bengal ta
kudancinta; kasa ce da masu rinjaye a cikinta
wadanda suke masu bin addinin Buda ne suke ta
gallazawa tsirarun Musulmi da ke cikinta!

3. Kasar Burma (Myanmar) tana da yawan
mutane sama da miliyon 55 kuma yawan
Musulmai a cikinsu ya kai kashi goma sha biyar
a cikin dari (15%).

4. Mafiyawan Musulmim Kasar da ake kira
Rohingya suna zama ne a Jihar Arakan (Rakhine)
.
5. Lalle muna kira ga shugabannin kasashen
Musulmi, da sauran shugabannin Duniya da su
gaggauta tsaida kisan kiyashin da mahukuntan
Burma suke yi wa al'ummar Musulmin Rohingya.

6. A nan muna jinjina ga Shugaban Kasar
Turkiyya (Turkey) Rajab Tayyib Erdogan (Recep
Tayyip Erdogan) saboda irin yadda yake nuna
damuwarsa a fili kuma a aikace game al'ummar
Musulmin Rohingya, kuma ko da a ranar
28/8/2017 sai da ya yi kira da babbar murya ga
shugabannin Duniya da su gaggauta kubutar da
al'ummar Rohingya daga wannan azaba da suke
ciki. Sannan ina ma jin a yau Laraban nan ne zai
tura Ministan harkokin wajensa watau Maulud
Chaawish Aglu (Mevlut Cavusoglu) zuwa Kasar
Bangladesh saboda da ya gane wa idanunsa irin
halin da 'Yan gudun hijirar Musulmim Rohingya
wadanda suka kai dubu 123 ke cikin.

Ina ma iya tunawa shi Shugaba Rajib Dayyib
Ordogan tun yana matsayin Prime Minister ma
ne ya kai ziyara ta musamman a Kasar Burma
saboda duba irin halin da Musulmin Kasar ke
cikin ya kuma kai wannan ziyarar ne a ranar
8/8/2012 tare da matarsa A'aminah Gulbaram
(Emine Erdogan) da kuma ministan harkokin waje
na Kasar tasa na wancan lokacin Ahmad Dawud
Uglu (Ahmet Davutoglu).
Muna fatan sauran shugabannin kasashen
Musulmin Duniya su ma za su yi koyi da wannan
bawan Allah wajen nuna damuwa da irin halin da
wadannan bayin Allah Musulmin Burma suke ciki.

Allah muke roko da ya gaggauta kubutar da
Musulimn Rohingya daga hannayen wadannan
azzalumai. Ameen.

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By  ©Dr Ibrahim Jalo Jalingo

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: