Wednesday 4 October 2017

TUSHEN HAUSAWA: NAZARI KAN ASALIN HAUSA

Tura Wannan Zuwa

Kashi na biyu.

ASALIN JINSIN HAUSAWA

Tana iya yiwuwa, littattafan mu na addini sune
suka fara kawo mana tarihin asalin jinsi da
rarrabuwarsa. Saboda wannan wani tarihi ne
daya faru wanda indai ba baiwa mutum iliminsa
akayi ba, zaiyi wuya ya iya wassafa yadda
tarihin ya faru.

Ance Annabi Adamu da Matarsa Hauwa'u
sune mutane na farko a duniya. Sune suka rinka
haihuwar 'ya'yaye biyu-biyu daki-daki, tare da
haɗa aure tsakanin mace ɗaya da namiji ɗaya
daga tagwaye mabanbanta, watakila wannan
haihuwar tasu itace asalin kabilu, gamin
gambizar kuwa shine asalin dangantakar jinsi da
kuma rarrabuwar sa.

Idan ma ba haka ba, ko labarin Annabi Nuhu
A.S ya nuna cewar ya haifi 'ya'yaye uku ne.
ƊAkace Hamu shine ya haifi bakin mutum na
farko a duniya, daga jikinsa kuma zuriyar hindu
ta fito. Samu shine na biyu wanda akace daga
jikinsa turawa suka fito, sai kuma Yafisu wanda
akace daga tsatson sa kabilun birnin Sin suka
ɓulɓulo. Don haka, tanan kaɗai muna iya
hasashen cewa cakuɗuwa ta silar auratayya da
sauran kabilu ne silar haifar da wasu sabbin
kabilun.

Babban labarin dai shine, akwai ilimi na
zamani dake bada damar fahimtar kwayoyin
halitta tayadda har ake gane wane nada alaka ta
jini da wane, da haka kuma muke son fahimtar
hausawa da asalin waɗanda suke da alaka dasu,
in yaso daga bisani sai mu kwatanta kokarin bin
diddigin shekarun da rarrabuwa ta auku a
tsakanin su.

A bisa wancan ilimi na kwayoyin halittu
(Genetic), dukkan wani ɗan adam dake doron
kasa nada kwayoyin halitta waɗanda ana iya
cewa kashi 99.5 na zubin kamanceceniyarsu
ɗaya yake da juna. Wannan ke tabbatar mana
da wancan ilimin da aka saukar mana cewa
mutum ɗaya ne asalin ɗaukacin mutanen
duniya, daga gareshi dukkansu duka fito.

Abu na gaba shine, kusan muna iya cewa a
yanzu babu wata kabila da zaka samu 'yan
cikinta da kwayoyin halitta zubi ɗaya tsura, sai
dai zaka samu kaso sama da hamsin iri kaza ne,
sannan da wasu kashe-kashen na sauran kabilu
kaɗan-kaɗan aciki.

Wani masani Ronald Fisher yayi bayani
gwargwadon yadda zamu gane bisa tafarkin
masanin ilimin kwayoyin halitta Gregor Mendel a
littafinsa mai suna 'The Genetical theory of
Natural Selection' inda yake cewa dalilai biyu ne
kesa wannan cuɗanyar tsakanin kwayoyin
halittu. Dalili na farko shine, yanayin yadda ake
gadon su kansu kwayoyin halitta na sanyawa na
wancan yasha banban dana wancan koda kuwa
uwa ɗaya uba ɗaya suke, domin ko a siffance,
akan iya ganin uba da 'yayansa uku, yaro na
farko yayi kama da mahaifiyarsa, na biyu yayi
kama da ubansa, yayinda na uku ya ɗauko
kamannin kakansa.
Dalili na biyu kuwa shine cuɗanyuwar kwayoyin
haluttun ta hanyar auratayya.

Watau, ɗan
wannan kabila ya auri yar waccan kabila. Sai
kaga kwayoyin halittar waccan kabila dana
wancan sun haɗu a kabila ɗaya, amma sai akalli
inda sukafi rinjaya ayi hukunci dashi.

ASALIN JINSIN LARABAWA DA YARABAWA

Yana da kyau, kafin mu fahimci asalin jinsun
mu mufara fahimtar ilimin dake cikin asalin
kabilu makusantan mu.

Su dai larabawa, wani bincike mai taken
'National Geographic's Genographic' da aka
gudanar a shekarar 2005 ya bayya cewa akalla
duk wata kabila balarabiya ta fito daga cikin
yankuna huɗu ne.

Yanki na farko shine Arabia.

Yanki na biyu shine Arewacin Afirka.

Yanki na uku shine gabashin Afirka.

Sai yanki na huɗu watau Asia.

Sai wannan binciken ya ɗauki wasu kasashen
larabawa tare da bayyana yadda asalin su ya
kasance.

Misali, Daga ciki an ɗauki kasar Tunisia, wadda
akace kaso 88 na kwayoyin halittar mazauna
kasar ya nuna cewar suna da alaka ta jini da
sauran larabawan Arewacin Afirka.

Amma akwai
sirki na larabawan Arabia da kaso 5, da sirki na
turawa da kaso 4, da kuma sirkin bakaken fata
mazauna afirka ta yamma da kaso 3. Wannan
sirkin nuna cewar an samu auratayya da gamin
gambizar kwayoyin halittu shekaru da dama da
suka wuce a tsakanin jinsosin da aka zayyana a
sama.

Labarin kusan haka yake ga Yarabawa domin
kuwa wani bincike da wasu masana Adebuwale
Adeyemo na jamiar Ibadan, Chenchen Yianxiu na
Cibiyar bincike ta 'National Human Genome' da
kuma Charles Rotimi na jamiar Horward suka
gudanar, sun samu cewar kwayoyin halittun
Yarabawa, ɗaya ne dana kabilun Igbo, Akan, da
Gaa-Adangbe.

Hakan na iya nufin cewar Asalin kabilun
mutum ɗaya ne, daga 'ya'yansa ko jikokinsa aka
samu rarrabuwar waɗannan kabilu har ma dana
yare, tunda binciken yayi hasashen cewa duk
yarukan kabilun suna da alaka da juna, asalinsu
guda ne, daga bisani suka rarrabu, duk da dai
binciken bai nuna sauran kabilun da suka shigar
da kwayoyin haluttun su cikin na waɗannan
ɗinba.

JINSIN HAUSAWA

Abinda wani bincike dangane da bakaken fata
yayi hasahe shine shekaru masu yawa da suka
gabata, mafi yawan bakaken fata suna wuri
ɗaya ne a zaune, kuma tana iya gaskatuwa
Cewa mutum ɗaya ne uba wanda daga jikinsa
duk kabilun bakaken fata suka fito. Amma dai,
anyi hasashen cewa tun shekaru dubu sittin
zuwa dubu tamanin baya bakaken fata suka
soma baro wancan mazaunin nasu na asali tare
da fantsamuwa a sassan duniya musamman
afirka ta yamma. Daga waɗannan zuriyar ne
kuma akafi kyautata zaton bakaken fata
Hausawa sun fito.

Babu jimawa, farfesa Umar Elzakzaky Al-
Bahaushe yayi hasashen cewa kwayoyin halittun
hausawa dana tsoffin misirawa sunyi
kamanceceniya, har ma yace yana kallon kamar
firaunan dayayi zamani da Annabi Musa A.S
bahaushe ne.

Inaga zamu karu da ilimi idan muka kalli
zancen nasa da kuma martanin hujjoji da
masana suka bashi dangane da musanta
wannan magana tashi...

Za mu ci gaba Insha ALLAH

.
Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa kamar haka  dadinkowa24.blogspot.com mungode
.
Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa nayau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Idan kana/kina da Labarin daku keson asanarwa da Duniya, ko Tambaya,Shawarwari,Hausa Novels, Nishadantarwa,Ilimantarwa,Ko Neman Sani akan ranakun dazamu cigaba dakawo muku Posting na Hausa Novels da Sauran su, zaku iya tuntubar ma'aikatan mu kuturo da Sunan Ku tareda Addreshin Ku tawannan Email din Officialdadinkowa24@gmail.com kyautane zamuyi muku komai don cigaban Al'ummar Hausa bama bukatar kudinka sai dai idan kaikayi niyyar Turowa don siyan Data Saboda acigaba dayin Posting a Kodayaushe batareda dakatawa ba, Website din Mu bashi da Alaka ta kusa ko tanesa da Wani/Wata Dan Siyasa/'Yar Siyasa afadin Duniya Burin mu shine musamu amincewar Al'umma aika da Gudunmawarka,Labari,Shawara da sauran su a Addreshin mu na email ✉💌📩 officialdadinkowa24@gmail.com
.
Always Visit==http://dadinkowa24.blogspot.com
.
Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri
.
ALLAH yabar Zumunci Amin🙏
.
.
Source By ©Sadiq Tukur Gwarzo, RN.
08060869978

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: