Friday 1 December 2017

KARANTA SAKONNIN SOYAYYA GUDA 7 DAKE SANYA MASOYA MURMUSHI

Tura Wannan Zuwa
TA ‘DAYA.

Ina son dukkan taurarin da suke bisan sama,
amma ba za’a hada son da na ke yi musu da
kuma na wadda ta ke a cikin idanuwan ki ba, ina
son ki.

Marubuci: Abba Muhd ‘Dan-Hausa


TA BIYU.

Lokaci yana nan zuwa da zaki mallakawa wani
zuciyar ki, ina mai yin kira a gare ki da ki
tabbatar da cewa kin mallakawa wanda ba zai
raunata zuciyar ki ta hanyar yaudara ko cin
amana ba, saboda ita zuciya d’ayace babu
wadda zaki dauko ki sauya a lokacin da bakin ciki
da damuwa suka mamaye zuciyar ta ki.

TA UKU.

Yanzu haka ina cikin farin ciki, shin kin kuwa san
mene ne dalili? Hmm saboda na kasance mai
sa’a, kin kuwa san tayaya? Saboda Allah ya na
so na, kin kuwa san me ya sanya na ce haka?
Saboda ya ba ni wata babbar kyauta, kin kuwa
san mene ne? Ba komai ba ne ba face KE
masoyiyata, ina son ki.

TA HU’DU.

A koda yaushe lokaci tashi yake yi tamkar
tsuntsu, amma ita soyayyar mu kullum ginuwa ta
ke tare da kara samun wajen zama a cikin
zuciyoyin mu karda ki manta da ni ki kasance
mai yin tinani na kamar yadda nima na kasance a
ko da yaushe.

TA BIYAR.

Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne
kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a
duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko
da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai
faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.

TA SHIDA.

SO tamkar wata sarkar zinari ce da ta d’aure
zuciyoyin mu a waje guda, a dukkan lokacin da
kika tsinka waccan sarka tofa ki tabbatar da
cewa tamkar kin kore farin ciki ne daga cikin
zuciya ta.

TA BAKWAI.

Salim ina son ka, me ya sanya ka ke yin
kokwanto a bisa kalmar so da na furta a gare ka?
Tabbas kaine mutum na farko da haduwa da shi
ya kore min bakin ciki, ya wanzar da farin ciki a
zuciya ta ya yalwata murmushi a saman fuska ta
hakane dalilin da ya sanya na ke kiran ka da
SADAUKI.

Salim, ka yi nasara ka yi nasarar jan
ra’ayin soyayya ta a kan ka kaine na mallakawa
linzamin zuciyata, kaine mutum na farko da na
taba furtawa kalmar SO kuma a yanzuma zan
kara mai-maitawa a gare ka ina son ka.

Kaa amincemu yi tsaftatacciyar soyayya.

Sai yanzu na gano cewa a duniya babu abun da ya kai
samun masoyi dad’i, a duk lokacin da na rasaka
ban san halin da zan shigaba, daga karshe ina
mai sanar da kai cewa buri na yanzu bai wuce na
ganin ranar da zaka zamo ango ni kuma na zamo
mata a gare ka ba, ina alfahari da kai a duk inda
na kasance, ka huta lafiya daga mai son ganin
farin cikin ka a koda yaushe. SALIMAT.

KARDA KU MANTA NI NE NA KU MASOYIN KU A
KULLUM, Dan-Hausa.
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user