Tuesday 5 December 2017

Bollywood: Fitaccen jarumin fina-finan India Shashi Kapoor ya mutu

Tura Wannan Zuwa

Daya Daga cikin fitattun jaruman fina-finan India na da Shashi Kapoor ya mutu yau litinin yana da shekaru 79 a duniya.

Rahotanni sun ce tsohon jarumin ya yi fama da rashin lafiya kafin rasuwar sa yau a asibitin Mumbai.

Shashi Kapoor da aka haifa a shekarar 1938 a Kolkata ya fito a shirin fina-finai sama da 150 kuma ya lashe kyaututuka da dama.

Cikin fina-finan da ya fito sun hada da Deewar da Kabhie Kabhie, kuma ya fito a fina-finai da dama tare da Amitabh Bachchan tsakanin shekarar 1970 zuwa 1990.

Shashi Kapoor ya yi kuma fina-finai da dama na turanci a Birtaniya da Amurka.

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: