Wednesday 13 December 2017

Shin Ko Kasan San Mece Ce Soyayya?

Tura Wannan Zuwa Ga
A wannan karon, na yi kicibis da sakon Yakubu Gwaram, wanda ya yi nazari game da ma’anar soyayya, domin kuwa a cewarsa, mutane da dama suna dai furta kalmar ce, amma ba su san ma’anarta ba.

Kuma ga alama da akwai kanshin gaskiya ga batunsa, amma dai ba zan ari bakinsa in ci masa albasa ba, bari mu saurare shi, mu ji abin da ya kawo a nazarin nasa:

Yakubu Sa’eed Yakubu Gwaram, 07066897465:

Assalamu Alaikum ya ’yan uwa ma’abota soyayya. Dukkan wani manazarci a kan wani abu zai so a ce ana aikata wannan abin da yake nazarta yadda ya dace. Na sani ku ma kun sani, a yanzu mafi akasarinmu muna ambatar soyayya a bakunanmu ne kawai, ba tare da mun san ita kanta soyayyar ba ballantana kuma ire-irenta.

Alhamdu lillahi, kwanakin baya na ga ’yan uwa sun kokarta wajen ba da ma’anar kalmar soyayya, ya dace a ce mu san ire-iren soyayya domin tantance a wane aji muke a soyayya.

Soyayya tana da azuzuwa guda uku ne, wato Soyayyar Ma’aurata da Soyayyar Saurayi da Budurwa da kuma Soyayya ta Gama-Gari, wacce take wanzuwa tsakanin sauran mutane. Duka wadannan sun kasu kasha-kashi, ga su kamar haka:

Soyayyar Ma’aurata: Ita ce soyayyar da ke sanya dukkan jiki ya amsa. Ta fi kowacce irin soyayya dadi, ita ce mai dauke da kauna, tausayi da jinkan juna.Ta kasu kashi biyu su ne kamar haka:

1-Cikakkiyar Soyayya: Irin wannan soyayyar ce dukkan wasu ma’aurata ke son tabbata a cikinta, domin takan mantar da su bakin ciki saboda tausayin juna, wato dai farin ciki da kulawa sun fi yawa a cikinta.

2-Sarkakkiyar Soyayya: Ita kuma wannan soyayyar tana kunshe ne da rashin jituwa sosai a tsakanin ma’aurata, duk da suna son junansu saboda wasu dalilai, sai ku ga ana ta samun matsaloli, dalilan kuwa sun hada da rashin tsaftar jiki ko rashin ilimi da sauransu.

Soyayyar Saurauyi da Budurwa: Ita ma wannan soyayya ce mai matukar mahimmanci, wacce a ita ce ake gina turakun zamantakewar aure domin a kayace take.Ta kasu kashi uku, su ne kamar haka:

1-Soyayya Mai Gudana (Ka So An So): A mafi akasarin lokuta irin wannan soyayyar ce ke kai wa ga aure. Soyayya ce wacce take babu tsunbure a cikinta, wato kowane sashe yana ba da hakkin da ya rataya a kansa (namiji da mace).

2-Soyayya Mai Gudana Tilo (Ka So An ki, Ka ki An So): Wannan kuma mutum daya ne ke kamuwa da ita, daya kuma bai ma san ana yi ba, sannan wannan soyayyar tana azabtar da zuciyar wanda ya kamu da irinta.

3-Soyayya Mai Gudana Kurma (Soyayyar Zurfin Ciki): Da jin kalmar zurfin ciki ko kurma lallai za a fahimci cewa wannan soyayyar ’yar shiru-shiru ce amma akan samu nishadi a cikinta, sannan kuma sashe biyu ne ke kamuwa da irinta amma a mafi yawan lokuta wanda suke zaune waje guda (namiji da mace) sun fi kamuwa da irin wannan soyayyar.

Soyayya Ta Gama Gari: Ita wannan soyayyar kusan kowa yana tsintar kansa a ciki, domin ta game dukkan abin da ake rayuwa da su, ta hade dukkan abin da z aka ji kana so, ban da wanda suke sama. Ta kasu kashi uku, su ne kamar haka:

1-Soyayyar Iyaye da ’Ya’yansu: Kamar yadda kowa ya sani, babu soyayyar da ta kai wannan soyayyar karko da karfi a zukatan mutane. Ita ce wacce ba ta gushewa.

2-Soyayya Tsakanin Al’umma: Ita ce mai cike da gaskiya da rikon amana, a wasu lokutan cike take da rudani da rashin tabbas da hayaniya.

3-Soyayyar Tilas: Ita ce soyayyar da dukkan wanda yake numfashi yake tsintar kansa a cikinta, domin son ita kanta rayuwar na cikin son da duk wani abu wanda ya zama dole mutum ya so a rayuwa.

Allah Ya ba mu damar zama da masoyanmu cikin lumana da jin dadi da rayuwar da ba nadama cikinta amin.

Madalla da wannan dogon nazari Malam Yakubu. Hakika mun karu da ilimi a wannan fanni, da fatan Allah Ya karo mana masu kaunarmu na gaskiya, amin! - FDk.

Hamidan Badamasi Kano, 07061855550:
Fatan alheri gare ka FDk, hakika sanin wace ce mace, wannan maganar ba duk kai ba ne kan iya bayyana yadda abin yake ba, amma mu ko in ce ni, a iya sanina da mace shi ne; tabbas mace wata halitta ce wadda Allah Ya halicce ta, aannan Ya sanya namiji ya zama jagora a gare ta. Mace ta kasance babu maganar tausayi a gare ta sai imani.
Tabbas mace ba ta da rikon amanar kanta balle amanar abokin zama.

Mace ba ta da rike sirri balle ka ba ta sirrin maganar da ba ka bukatar a san ta. In dai ka ga mace tana yin abin da aka umurce ta, to wannan sai a gidan daukar hoto ko tana da bukatar da take so ta cin ma wa, daga zarar ta samu abin da take so a gare ka, to ka gama yawo a wurinta.

Amma ba su taru sun zama daya ba.

Source By ©Aminiya
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user