Saturday 13 January 2018

Karanta Kaji Dalili: Kasashen Afirka wulakantattu ne —Trump

Tura Wannan Zuwa Ga

Wasu rahotanni sun ambato shugaban Amurka Donald Trump yana yin maganganun wulakanci kan 'yan ci-ranin da suka fito daga kasashen Haiti, El Salvador da Afirka ba.

"Me ya sa wadannan mutane da suka fito daga wulakantattun kasashe suka shigo nan?" tambayar kenan da Mr Trump ya yi wa 'yan majalisar dokoki ranar Alhamis, kamar yadda kafafen watsa labaran Amurka suka ruwaito.

Wadannan kalamai, wadanda ya yi a lokacin da suke tattaunawa kan shige-da-fice, ya yi su ne kan 'yan kasashen Afirka da Haiti da kuma El Salvador.

Fadar White House ba ta musanta kalaman wulakancin da Donald Trump a kan 'yan ci-ranin ba.

A makonnin baya bayan nan, gwamnatin Mr Trump tana ta kokarin ganin ta takaita iyalan 'yan ci-ranin da ke zaune a kasar da za a iya barin su su shiga Amurka, kuma ta dauki matakin ganin ta soke izinin zaman mutane da dama a kasar.

Mene ne takamaiman abin da ya fada?

Kalaman wulakancin da Mr Trump ya yi sun faru ne a lokacin da 'yan majalisar daga jam'iyyun kasar suka kai masa ziyara ranar Alhamis domin gabatar masa da kudirin dokar shige-da-fice wanda suka amince da shi.

Dan majalisar dattawa na jam'iyyar Democrat Richard Durbin ya yi jawabi kan izinin zama dan kasa na wucin gadi da aka bai wa 'yan kasashen da suka hadu da mummunan bali'i.

Jaridar Washington Post ta ambato Mr Trump na shaida wa 'yan majalisar cewa a maimakon karbar 'yan ci-rani daga wadancan kasshe, ya kamata Amurka ta rika amincewa da 'yan ci-rani daga kasashe irinsu Norway, kasar da Firai ministanta y ziyarci Trump a ranar.

Jaridar ta ambato shi yana cewa : "Me ya sa za mu kyale 'yan kasar Haiti a wannan kasar? Ya kamata mu kore su."

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba

Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user

0 comments: