Wednesday 3 January 2018

Karanta Wannan: An Bukaci Shugaba Buhari Ya Sauka Daga Mukamin Ministan Mai

Tura Wannan Zuwa

Wata kungiyar gamayya a jahar Kanon Najeriya ta bukaci Shugaban Najeriya kuma Ministan man kasar ya yadda kwallon magoron ya rabu da kuda.

Ma'ana, ya sauka daga mukamin Ministan mai don kar ya raba hankalinsa; ya nada sabon Ministan mai. Wannan ya biyo bayan abin da masu wannan ra'ayin ke kira yawaitar matsalar mai.

A yayin da ga dukkan alamu abubuwa ke dada yin yawa ma Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, kuma ‘yan Najeriya ke ci gaba da fuskantar karanci da kuma tsadar man fetur da kuma, uwa-uba, abubuwan da ke bin bayan tsada da kuma rashin man, gamayyar kungiyoyin sa kai a Kano sun bukaci Shugaba Muhammadu Buhari ya gaggauta sauka daga kujerar Ministan Albarkatun Mai na kasar kuma ya nada wanda ya kamata domin tunkarar wannan matsala.

Su ka ce idan aka nada Ministan mai, za a san wanda za a tambaya idan aka samu matsala a maimakon Shugaban kasa, wanda akwai abubuwa da yawa gabansa.

A wani taron gaggawa dangane da halin da kasa ke ciki, kungiyoyin sun tattauna sauran batutuwa da suka shafi rayuwar Jama’a, musamman hauhawar farashin kayayyakin masarufi da kuma yawaitar rashin ayyukan yi a tsakanin matasa, lamarin da sukace na kara zama barazana ga makomar Najeriya.

Dr Muhammad Mustafa Yahya, Daraktan Kungiyar Democratic Action Group shine yayi Magana da manema labarai a madadin sauran kungiyoyin, kuma ya yi wa wakilinmu na Kano Mahmud Ibrahim Kwari Karin haske game da abubuwan da taron ya cimma.

Shafin komai da ruwanka, Dadinkowa24 munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Kada Ku manta in zaku ziyarci website din mu
akan wayar/kwamfiyutar Ku zakusa address
kamar haka
dadinkowa24.blogspot.com banda sa www
kuma batareda bayarda sarari wajen sa
address din ba sannan da kananun Haruffa
kamar haka dadinkowa24.blogspot.com

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Dadin
Kowa24 don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://
dadinkowa24.blogspot.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Dadinkowa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Babban Shafi a Yanar Gizo da
ke gabatar da
shirye-shiryensa a cikin harshen Hausa Zalla
cikin 24 Hours ba tareda kakkautawa ba

Burin shafin DADINKOWA24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

ALLAH yabar Zumunci Amin

Source By ©Voa Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: