Wednesday 7 March 2018

KARANTA KAJI: Duk Hassadar Mai Hassada Sai dai Yaki Fadar Gaskiya Domin Mun Samar da Tsaro A Fadin Kasar Nigeria-Muhammadu Buhari

Tura Wannan Zuwa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ko 'yan hamayya da masu tsananin kushe za su yi amince cewa gwamnatinsa ta yi kokari wajen inganta harkar tsaro a kasar, tun daga hare-haren Boko Haram.

Shugaban ya fadi hakan ne a yayin da ya kai wata ziyarar jaje jihar Taraba da ke arewa maso gabashin kasar, a jerin ziyarar da ya fara ranar Litinin zuwa jihohi biyar da ke fama da rikice-rikice ko dai na manoma da makiyaya ko na masu tayar da kayar baya.

Ya kara da cewa tun bayan hawansa mulkin kasar nan gwamnatinsa ke mayar da hankali wajen magance matsalar tsaro.

Shugaba Buhari ya kuma jajantawa al'ummar jihar Taraba kan asarar rayuka da dukiyoyi da aka yi sakamakon rikicin baya-bayan nan da ya faru tsakanin manoma da makiyaya.

A yayin ziyarar tasa a Taraba, Shugaba Buhari ya yi ganawa ta musamman da sarakunan gargajiya na jihar da shugabannin al'umma da wakilan makiyaya da manoma da manyan jami'an tsaro da kuma manyan jami'an gwamnatin jihar, inda ya ji ta bakinsu kan abubuwan da ke faruwa.

Ya ce kokarin da ake na samar da zaman lafiya yana bukatar cikakken goyon bayan sarakunan gargajiya, musamman wajen ganin sun roki al'ummarsu da su dinga girmama rayukan juna.

'"Na zo nan ne musamman don na gana da sarakunan gargajiya da kuma gwamnatin jiha, don na mika musu sakon ta'aziyyata tare da jajantawa wadanda suka rasa 'yan uwansu suka kuma yi asarar dukiya.
"Ina so ku san cewa gwamnati na iya bakin kokarinta wajen ganin ta magance rikicin da ke tsakanin manoma da makiyaya, kuma za ta ci gaba da neman goyon bayan sarakunan gargajiya don sanin muhimmancinsu wajen kawo zaman lafiya a tsakanin al'umma, in ji shi.

Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku wanda ya tarbi shugaban ya ce ya karbi shugabanci ne daga jihar da dama can ke fama da rikicin kabilanci, amma gwamnatinsa tare da hadin gwiwar jami'an tsrao na iya kokarinsu don ganin sun sasanta kungiyoyin da ke fada da juna.

Su kuwa sarakunan gargajiya cewa suka yi, kamata ya yi a samar da wata tsattsaurar doka da za a dinga hukunta duk wanda aka kama da hannu a tayar da zaune tsaye, don hakan ne kawai zai rage rikice-rikicen.

Shugaban kasar dai ya yi alkawarin tabbatar da hakan ta hanyar gurfanar da duk mai hannu a janyo rikici a gaban shari'a da kuma daukar mataki a kansu.

Shugaban yana ziyartar jihohin Taraba da Zamfara da Benue da Yobe da kuma Rivers ne.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.

Source by ©Bbc Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: