Monday 19 March 2018

Karanta Kaji: 'Yan fina-finan Hausa sun nuna bacin ran su game da hoton diyar gwamnan kano da angon ta dan gwamnan jihar Oyo

Tura Wannan Zuwa

Wasu masu harka a masana'antar Kannywood sun nuna bacin ran su kan rashin tsawaitawa daga malamai kan hoton diyar gwamnan jihar kano da angon ta dan gwamnan jihar Oyo.

Hotunan shagalin bikin auren Fatima Ganduje da angon ta Idris Ajimobi wanda yayi  yawo a kafafen sada zumunta, an gan inda suka rungumi juna har hannun mijinta ya kai ga nononta cikin daya daga cikin hotunan.

Sunyi fashin bakin ne ta hanyar sako da suka wallafa a shafukar su na kafar sada zumunta ta instagram.

Jarumi Ty Shaban ya zartar da nashi bacin rai ga wani jigon masana'antar wanda ya taka rawar gani wajen ladabtar da jaruma Rahama Sadau bisa fitowar da tayi a wani bidiyo inda take rungumar mawaki

A cewar shi shi jigon mai suna mallam Nura Hussein wanda yake daya daga kungiyar masu shirya fim yayi shuru kan batun ganin cewa lamarin na yaran manya ne amma inda ga yan fim ne wanda suke yaran talatawa da an tsawatar dasu.

Yana tambaya kamar haka: "Mallam Nura Hussain Na daya daga cikin masu fada aji a masana'antar shirya Fina finai ta kannywood. Mallam Nura ya taka rawar gani lokacin da jaruma rahama sadau ta fito a wani video Waka Wanda takai har Saida hadaddiyar kungiyar masu shirya Fina finai (moppan)suka dauki matakin ladabtarwa a kanta.

TAMBAYA: shin Mallam Nura ba muji yayi wani sharhi akan pre wedding picture Na Fatima GANDUJE da Idris AJIMOBI ba Wanda duniya ta gani karara yana shamata Baki kuma hannuwansa akan nononta? Shin ko fadakarwar an kebe tane akan wasu gungun mutane ne?

Ya kara da cewa bawai ya hakan don ya alakanta jigon da hoton sai don ya tuna masa da irin rawar da ya taka wajen ladabtar da jaruma a matsayin shi na malam amma kuma yayi shuru da faruwar hakan wanda kuma hoton yayi yawo a duniyar gizo. " Ba Ina nufin alakanta Brother Mallam Nura Hussain bane da hoton bikin Fatima GANDUJE da Idris AJIMOBI, illa rawar da malamin ya taka a matsayinsa Na jarumi wurin tsawatarwa Rahama sadau akan fimdin da tayi...da kuma ladabtar da ita.

To, shine al'umma take kallo yana faruwa a yanzu kuma sunan malamin ya zama Matashiya abin kwatance a yanzu. kukan kurciya ne kawaii mukeyi."

Shima marubuci Zaharadeen Abdullahi ya koka kan batun inda yayi koke cewa wannan ba dabiar al'adar hausawa bane kuma yin haka yana bata tarbiyar yara.

Yace inda yan fim ne suka yi hakan wanda har yanzu ba'a kama su da yinta ba da malamai sun tsawaita amma daya ke diyan manya ne anyi kunnen kashi kan lamarin.

" Wannan ba dabi'armu baceba Hausa/Fulani anbata mana suna hakkin malamaine su tsawatar!! KALUBALE!! Diyan manya ke bata tarbiya sai an magana kuce yan film sabida su suka fito daga tsatson talakawa Gayaman sunan film din Hausa daya koyarda hakan??

Shima jarumi  Zaharadeen Sani ya goyi bayan marubuci inda ya gasgata sakon da rubutan ya kunsa a kafar sada zumunta na Instagram.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan
Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin
website din akwai "Home" sai ku shiga,
mungode

Ku cigaba da Kasancewa da Website din Muryarhausa24.com don samun abubuwan more rayuwa na
yau da Kullum

An kirkiri Wannan Shafi domin
bunkasa Harshen Hausa ako ina afadin Duniya
Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin
Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com
Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin
Muryarhausa24 aduk inda kuke a fadin Duniya
farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me
hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu
Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga
Suleman Abubakar saboda awajensa musami
Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani
ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki
daya Amin Summa Amin.

Source by ©Fim Hausa

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user

0 comments: