Monday 9 April 2018

CIKAKKEN TARIHIN LIL AMEER: ABUBUWAN DA YAKAMATA KU SANI DANGANE DA RAYUWAR LIL AMEER

Tura Wannan Zuwa Ga
Hakika masana’antar nishadantarwa ta Arewa ta yi babban rashi da rasuwar daya daga cikin matasan mawakan Hausa Hiphop, amma indai ajalin mutum ya kai babu wanda zai iya kubutar da shi.


LIL AMEER


Ameer Isa Hassan (wanda a ka fi sani da Lil Ameer) ya rasu ranar 14 ga watan Satumba, 2017, a garin Kano sanadiyar hatsarin mota. An yi jana’izar shi ranar Juma’a a layin Massalacin Juma’a na Tarauni.

Haifafan dan jihar Kano, an haifi Marigayi Lil Ameer a cikin 2003 a birnin Kano. Har zuwa lokacin rasuwarsa, mawakin ya na koyan darasi a makaranta, duk da kasancewar shi wanda ya fara shahara a harkar wakoki marigayi bai bari harkar ta dauki hankalinshi wajen koyan darasi ba.
Ya kan tafi makarantar boko kuma idan ya tashi ya je ta islamiyya. Sai karshen mako ya ke samun damar yin aikin waka. Ameer ya canza makarantu da dama domin masoyansa su kan tunkare shi idan ya na koyon darasi. Babban burin marigayi shi ne in ya gama karatu ya zama matukin jirgin sama.

Lil Ameer Da Mahaifiyarsa

Hakika iyayensa ne su ka ba shi damar fara waka kuma mahaifiyarsa ta ke taimaka ma sa wajen rubuta wakokin, domin ya fara waka tun ya na aji daya a karamar sakandare (JJS 1).

Matashin ya tashi ne da muradin waka tun ya na dan kankani. Ya fara waka ne domin ya nuna wa duniya cewa matasa daga yankin arewacin kasar nan na iya rera waka kuma su yi nasara.

LIL AMEER

Ya samu damar yin wakoki da dama kuma ya yi wasa tare da sauran shaharrun mawaka kamar su Classik, Dj Abba, BOC da dai sauransu. Daga cikin garuruwan da marigayi ya samu damar halarta wasa akwai Kaduna, Kano da dai sauransu.

Cikin wakokin da marigayi ya yi akwai “Boss”, “Champion”, “Ilimin Boko Da Addinin Musulunci”, “Dance For Me”, “Baby Hello”, Hakan Ta Ke”, “Lifehood”, “Alhamdulillah”, “So Fly” da dai sauransu.

Tabbas abu ne mai wahala a sake samun karamin yaro kamar Lil Ameer, wanda ya yi shuhura haka bisa la’akari da karancin shekarunsa. A lokacin da a ke tsaka da ta’aziyyar marigayin, Farfesa Abdalla Uba Adamu ya taba shaida wa LEADERSHIP A RANAR LAHADI cewa, tun Marigayi Sanin Dankwairo ba a yi wani yaron mawaki mai shuhura ko basirar Lil Ameer a kasar Hausa ba.

Lil Ameer

Yau kimanin Shekara ɗaya da rasuwar Lil Ameer .

Ɗaukacin Ma'aikatan shafin Muryar Hausa24 muna Addu'ar Allah Ya ji kan sa, Amin!

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki tuƙuru don Ilimantarwa da Faɗakarwa.

Ku ci gaba da kasancewa da mu a www.muryarhausa24.com.ng   a duk inda ku kasance a faɗin Duniya.

MURYAR HAUSA24 FARIN CIKIN AL'UMMA.

Tushe/Asali: LEADERSHIP AYAU
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user