Tuesday 8 May 2018

Karanta Yanzu Kaji: Abubuwan da yakamata kusani dangane da Rigimar Adam A. Zango da Ali Nuhu ko me ye Dalili?

Tura Wannan Zuwa Ga


Za a iya cewa babu wasu jarumai fitattu da suka samu
daukaka a fagen fim din Hausa kamar Ali Nuhu da Adam A
Zango, sai dai rashin jituwar da mutanen biyu ke yi ta sa ana
nuna shakku kan wayewarsu da fargaba kan makomar
masana'antar, wacce ke fama da karancin shugabanci nagari.

Ba dai yanzu ne jaruman biyu suka fara samun sabani ba,
kuma duk da cewa an yi kokarin sulhun tasu a baya, amma
batun na ci gaba da ruruwa.

A 'yan kwanakin nan, kafafen sada zumunta musamman
Instagram sun cika da kalaman batanci da habaici, a wasu
lokutan ma har da zage-zage da ke kaiwa da komowa tsakanin
magoya bayan jaruman biyu.

Duk da cewa duka Ali Nuhu da Adam Zango ba su fito fili sun
tofa albarkacin bakinsu a kan lamarin ba, a zahiri ta ke cewa
sun san abubuwan da ke gudana, domin abin ya kai matakin da
ba zai yi wu na ce ba su sani ba.

Me ya hada fadan, kuma su waye ke ruruta shi?

Zai yi wuya ka fito ka ce ga abinda ya haddasa wannan rashin
jituwar ta baya-bayan nan, amma dai abin da ya fito fili shi ne,
akwai wasu da za a iya dora alhakin tabarbarewar lamarin a
kansu.

Ba wasu ba ne illa 'yan fada ko kuma masu dabi'ar fadanci.
Suna yawo nan da can suna fadar karya da gaskiya domin
neman gindin zama a wurin jaruman biyu.
A don haka ya kamata a fallasa masu ruru wutar rikin nan, a
kunyata su, sannan a hukunta su idan ba su daina ba. Wasunsu
fa ba za su taba son a zauna lafiya ba, ba za su taba son su ga
an yi sulhu ba, domin kuwa ba su da kwarewar da za su iya
fitowa a babban fim ba, in ba tare da fadanci da banbadanci
ba.
Dole ne a kauda dabi'ar nan ta fadanci ga wanda ya kawo
jarumi Kannywood, da kuma kokarin kushe abokin hamayyarsa.
Hakan na nuna irin raunin harkar fina-finan na Hausa, domin
kuwa tana nuna cewa gaba daya masu harkar tunani daya
kawai su ke yi, kuma manufarsu ma iri daya ce.

Abu ne mai kyau ka girmama duk wanda ya daura ka a wata
hanya, ko ya taimake ka, amma za ka iya hakan ba tare da ka
ci mutuncin wasu ba.

Tasirin Ali Nuhu da A Zango a Kannywood

Yanayin zamantakewa a rayuwa da kuma lura da abubuwan da
kan faru yau da kullum sun nuna cewa, kishi wata dabi'a ce ta
mutane da dabbobi. Zai yi wuya a ce wasu da suka yi tarayya a
wani abu guda ba sa kishi da juna.
Kishin ya kan yi tsanani idan wani ya yi wa sa'anninsa zarra,
hakan zai iya sa wasu su fara yi masa hassada da tunanin mai
ya sa wane zai fi ni.
A wasu lokutan ko da mutanen biyu suna zaune lafiya, na kusa
da su sai sun kunna wuta tsakaninsu.
A Kannywood, sama da shekara 10 ake dangantaka tsakanin
taurari biyu Ali Nuhu da takwaransa Adam A. Zango. Ali Nuhu
ya fi Adam Zango shekaru kuma ya riga shi fara fim.
Ko a kwanakin baya, Ali Nuhu ya shaida wa BBC cewa shi ne
ya fara saka Adam Zango a fim.
Duk da cewa akwai wasu kwararrun jaruman masu basira,
amma dai har yau ba bu kamar wadannan biyun wajen
daukaka. Haka rayuwa ta ke.
A yanzu duka jarumai masu tasowa na kokarin bin sawun Ali
da Adam, to sai dai abin takaici shi ne matasan biyu sun dau
dogon lokaci ba sa ga-maciji.
A duniya, ba ka raba taurari da janyowa kansu magana. Hakan
na taimaka musu wajen daukar hankulan kafofin watsa labarai.
Kuma yawan ambaton jarumi shi ya ke maida shi shahararre.
A bisa tsarin rayuwa, a kan samu sabani duk lokacin da
mutane suka yi mu'amala, ko aiki, ko zama tare. Don haka
taurari da dama suna hamayya da juna.

Rayuwar Ali Nuhu a takaice

An haife shi a watan Maris na 1974
Ya yi karatun firamare da sakandare a birnin Kano
Ya yi digiri a jami'ar Jos, kuma ya yi hidimar kasa a jihar Oyo
a 1999
Ya fito a fina-finai sama da 100 na Hausa da Turanci
Yana cikin Hausawa na farko-farko da suka fara fitowa a
fina-fina Nollywood
Ya shahara matuka a fagen fim a ciki da wajen Najeriya
Ya ci lambobin yabo da dama, abin da ya sa ake masa
lakabi da Sarki
Illar da fadan ka iya jawowa Kannywood
Matsalolin da Kannywood ta ke fama da su sun isa haka. Na
san cewa wasu za su ce ko a masana'antar fina-finan India ta
Bollywood da ta Amurka Hollywood ana samun irin wannan
matsala tsakanin manyan taurari.

Haka ne, domin misali kullum ana kasayya tsakanin Amir Khan,
Salamn Khan da Sharukh Khan tun shekarun 1990, haka kuma
taurari mata da dama suna rigima da dama kan samari, da
fitowa a fim, da kyautuka.
To sai dai karan masana'antarsu ta kai tsaiko don haka irin
wadannan matsalolin ba za su shafe ta ba.

Masana'antar Kannywood wata karamar masana'anta ce da
tun kafuwarta sama da shekara 20, take fama da suka daga
mutanen da ke ganin tana gurbata al'adun Hausa da addinin
Musulunci.
Bisa la'akari da wannan, a iya cewa duk wata badakala, da
gaba, da rashin hadin kai babu abin da za su haifarwa
Kannywood din sai koma-baya.
Sama da shekara 10, har yanzu ana sanya misali da ci gaba da
tattaunawa kan hoton bidiyon tsiraici na Maryam Hiyana. Ko
irin wannan kadai ya isa a ce ya janyo hadin kai da taka-
tsantsan a masana'antar.

A yanzu rashin-jituwa tsakanin Ali Nuhu da Adam Zango kadai
ta isa ta gasganta zargin masu cewa su kan masu harkar fina-
finan ba su da tarbiyyar da sanin ya kamata da har za su iya
koyar da wata kyakkyawar tarbiyya ko fadakar da masu
kallonsu, kamar yadda kullum suke ikirari.
Ta fuskar zamantakewa da sanin ya kamata, abin kunya ne
yadda mabiyan taurarin biyu suke musayar mugayen kalamai,
da habaici, wasu lokutan ma har da zage-zage.
Ba makawa, wannan na nuni da irin dabi'a da tarbiyyar masu
fina-finan na Hausa tun daga kan mutanen biyu.
Saboda dimbin magoya bayan da suke da shi, rikicin ya kusa
raba kan masana'antar ta Kannywood gida biyu. Hakan ta sa
har a kan samu wasu taurari suna sauya sheka daga wannan
bangare zuwa wanda suka ga za su fi samun biyan bukata.
Kazalika hakan ya sa a wasu lokutan a ke kin saka wasu taurari
a fim saboda ana ganinsu a matsayin 'yan gidan abokan gaba.
Kuma shi ya sa a wasu lokutan a kan sa wadanda ba su dace
ba su taka wata rawa a wasu fina-finan, wanda kuma hakan
koma-baya ne.

Rayuwar Adam A Zano a takaice

An haife shi a garin Zangon Kataf a jihar Kaduna
Ya bar garin a 1992 bayan rikicin kabilancin da aka yi
Ya koma arayuwa a jihar Plateau inda ya yi karatun Firamare
Talauci ya hana shi cigaba da karatu a wancan lokacin
Tun yana yaro ake masa lakabi da Usher - mawakin nan dan
Amurka saboda yadda yake rawa
Ya koma Kano inda ya fara aiki a wani kamfanin kade-kade
da raye-raye
Fim dinsa na farko shi ne Sirfani, wanda ya ce shi ya shirya
shi da kansa
Ya fito a fim sama da 100 a tsawon shekara 16
'Ko a gidan giya akwai babba'
Yawan magoya baya da makiya da suke da shi ya kuma sa duk
abinda suka yi yana jawowa Kannywood din bakin jini ko
akasin haka.
Akwai ma wasu karin wasu illolin da rikicin ya ke yi wa
Kannywood. Ba manufatace in ce wane ne da laifi ko wane ne
da gaskiya ba.

Amma dai ana cewa ko a ginda giya akwai babba. Don haka ya
kamata Adam Zango ya ja kunnen magoya bayansa da suke
ganin dai-dai ne cin mutuncin Ali Nuhu.
Shi ma a nasa bangaren, ya kamata Ali Nuhu ya gane cewa
sun jima tare da Adam Zango suna abota da ya kamata ma a
ce sun zama 'yan uwa. Don haka shi ma ya kamata ya
magantu ya gargadi magoya bayansa.
Dole ne duka su biyun su gargadi magoya bayansu cewa duk
wanda ya kara zagin wani to sun raba-gari.
'Babu shugabanci nagari'
Kungiyar masu fina-finai da manyan cikinsu ya kamata su ma
su tsara kansu, su zama suna damuwa da abinda ke faruwa a
Kannywood, su samarwa kansu kima da za su iya jan kunnen
duk wanda yake kokarin raba kan 'ya'yan masana'antar.
Abin takaici ne ganin yadda ba a je ko ina ba, aka koma ruwa
bayan sulhun da darakta Falalu Dorayi ya shirya, kuma
shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano Isma'ila Na'abba
Afakallah ya jagoranta.

Mai yuwa hakan ba zai rasa nasaba da rashin fayyace hukunci
kan duk wanda aka samu da laifin saba ka'idojin sulhun ba.
Don haka dole ne kowa ya shigo a samu domin daidata
manyan taurarin. Domin kuwa masana'antar ta fi kowa daga
cikin su biyun muhimmanci, don haka ya kamata a tsawatar
musu.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©BBC HAUSA
TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user