Wednesday 9 May 2018

Takaitaccen Tarihin Sheikh Sheikh Khalifa Isyaka Rabi'u: Abubuwan da Yakamata Ku sani dangane da Rayuwar Marigayi Sheikh Khalifa Isyaka Rabi'u - Hotuna da Cikakken Tarihi

Tura Wannan Zuwa
Takaitaccen Tarihin Sheikh Sheikh Khalifa Isyaka Rabi'u Abubuwan da Yakamata Ku sani dangane da Rayuwar Marigayi Sheikh Khalifa Isyaka Rabi'u - Hotuna da Cikakken Tarihi

Biography of Sheikh Khalifa Isyaku Rabi'u

Marigayi Sheikh Khalifa Isyaka Rabi'u malamin addinin musulunci ne, kuma shahararren dan kasuwa ne wanda ya dade yana ayyukan taimakawa al'umma a lokacin rayuwarsa.

An haifi marigayi Isyaku Rabi'u a 1928 ga iyalan Muhammadu Rabi'u Dan Tinki, wanda mai wa'azin addinin musulunci ne daga Bichi cikin jihar Kano a Najeriya.

Daga 1936 zuwa 1942, marigayin ya halarci makarantar allo ta mahaifinsa, inda aka horar da shi kan Alkur'ani da Larabci.

Daga nan ya tafi Maiduguri domin karo ilimi, kuma bayan ya gama karatunsa a can ne ya dawo gida da niyyar yin aure.

Bayan ya yi auren kuma ya tafi Zaria gidan wani shahararran Malami, mai suna Malam Na'iya, inda ya samu shekaru biyu yana dalibta.

A shekarar 1949 ya kasance malamin addini mai zaman kansa, inda yake koyar da Larabci da Alkur'ani ga dalibansa. Kuma a cikin daliban akwai Ibrahim Musa Gashash.

A farko shekarun 1950 Mallam Isyaku Rabi'u ya fara kasuwanci, duk da cewa bai bar koyarwa ba. Ya kafa wani kamfani mai suna Isyaku Rabiu & Sons a 1952.

Da farko kamfanin ya fara da zama dilan kayan kamfanin UAC ne, wanda a wancan lokacin ke kasuwanci akan kekunan dinki, da litattafan addinin Musulunci da kuma kekuna.

A 1958, kamfanin ya sami bunkasa bayan da aka kafa masakar Kaduna Textile Limited kuma kamfanin na Isyaku Rabiu & Sons ya zama daya daga cikin dilolinsa na farko.

Marigayin ya zama babban dilan kamfanin a arewacin Najeriya, kuma a 1963 shi da wasu 'yan kasuwa daga Kano suka hadu don kafa Kano Merchants Trading Company.

Wannan kamfanin ya jure wa gasa daga kamfanonin da ke shigo da kayayyaki daga kasashen waje. Ya kuma kafa wani kamfani mai dinka kayan sawa a 1970.

A lokacin da aka fara siyasar janmuriya ta biyu, marigayi Sheikh Isyaku Rabi'u ya goyi bayan jam'iyyar NPN wadda ta mulki kasar.

Kasuwanci

Kamfanin da marigayin ya kafa na Isyaku Rabiu & Sons a matsayin kamfani mai kasuwancin gine-gine da harkar inshora da na banki da kuma saye da sayarwar filaye.

A shekarun 1970, kamfanin ya zuba jari cikin harkar hada akwatuna da jakukkuna, kuma wannan wani hadin gwuiwa ne da wasu masu zuba jari daga Lebanon.

A 1972 ya kafa masakar Bagauda Textile Mill, masu saka zannuwa da kayan inifom, inda daga nan ne ya kafa wasu kamfanonin da ke kasuwanci a bangarori daban-daban na tattalin arzikin kasar.

Wasu daga cikin sassan sun hada da kasuwanci kan kifi, da harkar gidaje da filaye, da siga, da kamfanin da ke samar da kayan motoci musamman na Daihatsu.

Amma saboda faduwar darajar Naira, kamfanin ya mayar da hankalinsa wajen kere-kere da kasuwanci kaya.

Marigayi Isyaku Rabi'u ya rasu ya bar mata da 'ya'ya har da jikoki masu yawa, kuma a cikin 'ya'yansa akwai Nafiu Rabiu, wanda shi ne babban dansa. Akwai kuma babban dan kasuwan nan, Abdulsamad Rabiu, wanda shi ne shugaban kamfanonin BUA.
Akwai kuma Rabi'u Rabi'u, mai kamfanin jirgin sama na IRS Airlines, da Naziru Rabi'u, da Quraish I Rabi'u, da Makiu Rabi'u, sai Abdullahi Rabi'u, da Muhammad Rabi'u, da Daha Rabi'u.

Kuma a fili yake cewa gidan marigayin na cikin gidaje mafi girma a duk fadin Kano.

Ayyukan taimako

Ban da fagen karatun addini da kaswanci, marigayi Sheikh Isyaku Rabi'u ya yi fice wajen ayyukan taimako, wanda ya sa mutane da dama ke kaunarsa.

Malam Isyaka Rabi'u sanannen dan darikar Tijjaniya ne, kuma yana daya daga cikin manyan almajiran shiek Ibrahim Nyass Kaulaha.

Tarihin Khalifa Isyaka Rabi'u a Takaice

Bayanai sun nuna cewa an haifi marigayin ne a 1928
Ya yi karatun AlKur'ani da na adidni a birnin Kano
Kafin daga bisani a tura shi birnin Maiduguri na jihar Borno domin kara karatu
Ya koma Kano inda ya ci gaba da koyar da karatun Kur'ani da na addini
Daga baya ne kuma ya fara harkokin kasuwanci inda ya kafa kamfanin Isyaka Rabiu & Sons
Ya yi fifce matuka a fagen kasuwanci da na karatun Alkur'ani
Daga bisa ni an nada shi Khalifan Darikar Tijjani a Najeriya
Harkokin kasuwancin da 'ya'yansa suka gada kuma suka ci gaba da samun daukaka a kai.

Bayani kan darikar Tijjaniya

An kafa darikar ne a kasar Aljeriya a shekarar 1784
Sheikh Ahmad ibn Muhammad al-Tijjani ne ya kafa ta
Ta yadu zuwa sassan duniya daban-daban, inda ta ke da mafi yawan mabiyanta a Arewaci da kuma Yammacin Afirka
Tana kuma da karin mabiya a Afirka Ta Kudu, da Indunisiya da kuma sauran sassan duniya
Akwai sauran dariku na Sufaye a addininin Musulunci amma Tijjaniya ta fi kowacce girma
Sun ce suna da muhimman ayyukan ibada guda uku a kowace rana:

Neman gafarar Allah; Yin salati ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma kadaita Allah
Sai dai ana zarginsu da wuce gona da iri wurin nuna soyayya ga Shehunnansu, lamarin da wasun su ke musanta wa
Ana alakanta Sheikh Ibrahim Nyass da farfado da darikar a karni na 20 bayan ta kwanta dama.

An haife shi a kasar Senegal kuma jama'a kan yi tattaki daga sassan nahiyar da dama domin ziyartar kabarinsa
Darikar Tijjaniya ta kasu kashi-kashi musamman a kasashe irin su Najeriya inda suke da mabiya sosai.

KARIN HASKE KAN NASARORIN SHI DAGA SHAFIN MURYARHAUSA24.COM.NG
KADAN DAGA CIKIN AYYUKAN ALHERIN DA MARIGAYI KHALIFA ISYAKA RABIU YAYI A RAYUWARSA

Ya Gina Babban Masallacin Juma,a a unguwar Gorandutse, wanda a zamanin da akayishi, shine giinin Masallaci mafi kayatarwa a Arewacin Nigeria.

Ya Gina Babban Masallacin juma,a tare da dakin taro na makaranta al,qur,ani a Kofar Mata kusa da kasuwar Kantin kwari.

Ya Gina Babban Masallacin juma,a a unguwar Gadonkaya hade da makarantar Haddar al,qurani a hade.

Ya Gina Babban Masallacin a unguwar Jakara kusa da tsohon Gidansa.

Ya samar da makarantar haddar al,qurani mai suna Al-Tanzeel wacce zata dinga bayar da shaidar karatu babba.

A iya sanin da nayi masa tun tasowa ta, Khalifa bashi da aikin daya wuce yiwa addini hidima.

Muna adduar Allah ya Gafartamasa Ameen.



Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku
Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, FADAKARWA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com 

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki Mungode

Source:Bbc Hausa and Muryar Hausa24

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user