Saturday 12 May 2018

Takaitaccen Tarihin Maryam Babban Yaro: Abubuwan da Yakamata Ku Sani dangane da Rayuwar Jaruma Maryam Babban Yaro

Tura Wannan Zuwa
Maryam Gidado tana daya daga cikin manyan jarumai mata a masana’antar fina-finan Hausa. Aminiya ta tattauna da ita kan harkar, inda jarumar ta tabo batutuwan da suka shafi harkar fim da kuma rayuwarta.

Ga yadda hirar ta kasance:

A gabatarwa, wace ce Maryam Gidado?

Kamar yadda aka sani, sunana Maryam Jibril Gidado, wacce aka fi sani da ‘Maryam Babban Yaro.’
Na samu wannan suna ne tun daga lokacin da muka yi fim da Adam A. Zango mai suna ‘Babban Yaro.’ An haife ni a watan Disamba a 1988 a garin Jos. Na fara makaranta a Hassan Memorial, sai aka mayar da ni firamare ta LGA Gangare, sannan na yi makarantar Arabiyya ta Sakandire a Bauchi Road, duka a Jos.
Sannan na je na yi Diploma a bangaren kwamfuta a wata makaranta daban. Daga nan na koma Bauchi na nemi in yi HND, amma ban samu ba sai na yi diploma a bangaren kididdiga. Sai kuma na ci gaba har na yi HND a nan, sai na dawo Jos na yi digirina a Jami’ar Jos.

Ko Maryam ta taba yin aure?

To yanzu idan na ce ma ban taba yin aure ba sai a yi mini dariya a matsayina na Bafulatana, kasancewar kowa dai ya san ka’idar Fulanin daji yi wa ’ya’yansu aure da wuri. Bayan na gama jarrabawar WAEC da NECO aka yi mini aure.
Ina shekara sha hudu na haifi ’yata ta farko, bayan shekara daya da auren ke nan. Don haka shekara goma sha hudu na ba ’yata ta fari. Yanzu ka ga ta shiga shekara sha daya ke nan.

To yaya aka yi kika samu kanki a harkar fim?

Ni dai gaskiya da ina kallon fim ne kawai, amma ina tunanin shirme ne kawai, domin idan na ga ’yan fim har zaginsu nake yi don ban taba tunanin zan yi fim ba.
Daga baya sai na ga yadda abin yake fadakarwa. Na ga wasu ma sun Musulunta ta hanyar fim. Sai na ga abin wa’azi ne.

To, a baya kin fada mana yadda aka yi miki aure har kika haihu. Sai dai ba ki fada mana ko kun rabu da mijin ko mutuwa ya yi ko kuma da aurenki kike yin fim ba?

To, a gaskiya ba zan iya fada ba. Saboda a duniya babu abin da ya kai sirri dadi. Idan ka rufa wa wani asiri Allah Zai rufa naka. Kuma tsakanin mata da miji sai Allah. Don haka wannan mutane su yi hakuri.

Shin wannan dan naki na biyu babansu daya da ’yarki ta farko?

Ba daya ba ne. Bayan mun rabu da mijina na yi wani sabon aure. Lokacin da na auri mahaifin dana ma har na fara harkar fim. Ina da cikinsa ya gudu ya bar ni har na haife shi yanzu shekarun dana na biyu bakwai ke nan.

Abin nufi a nan shi ne, kun rabu da shi ne ko rasuwa ya yi?

To, in dai wannan ne ba rasuwa ya yi ba, yana nan da ransa, sannan ina da cikin dana na biyu wata daya ya tafi ya bar ni, har zuwa yanzu mahaifinsa bai zo wajen da yake ba. Sai dai ya turo a dauki hotonsa, kuma zai iya kira ta waya su yi magana, amma dai yana nan a Kaduna kawai dai tafiyar da ya yi ya bar ni don wani dalili ne na daban.

To daga nan sai me ya biyo baya?

Kai dai a bar maganar haka, don sirri yana da dadi.

Ki fada mana yadda aka yi kika samu kanki a harkar fim da kuma shekarar da kika fara?

A gaskiya na manta shekarar da na shigo, amma dai na fara ne da albam din Mahmud Nagudu mai wakar ‘Garin So Nisa’ amma fim din da aka fara yi mini shi ne wani fim mai suna ‘Ragowar Yaki,’ lokacin da muke yi a Jos da ni da Ali Nuhu.

Shi ne fim dina na farko da na fara yi a duniya, kuma da ma tun da na fara fim ban fara da mai tallafa wa jaruma ba, da jaruma na fara. Kodayake da farko mutane sun dauka albam nake yi ba fim ba, saboda shi ne na fara. Sai daga baya na zo na shiga fim din su Alma, inda na yi ‘Ragaya’ da ‘bingyal da ‘Mukaddari’ da sauransu.

Ko za ki iya bayyana yawan fina-finan da kika yi?

Gaskiya ba zan iya fadar adadinsu ba. Don ka ga a wata zan iya yin fim biyu ko uku, to yaya zan iya sanin fim din da na yi a tsawon lokacin da na yi a harkar fim? Sai dai zan iya fadar wasu kadan daga cikinsu, musamman wadanda ba su dade ba kamar ‘Babban Yaro’ da ‘Wata Hudu’ da ‘Munafikin Mata’ da ‘Al’ajabi’ da ‘Zawarawa’ da ‘Fulani’ da ‘Sultan’ da ‘Basaja.’ Ina ji da su a cikin fina-finaina.
Akwai lokacin da kika yi wani tashe sai kuma aka daina ganin ki a harkar fim.

Hakan ya sa ake cewa ko kin yi aure ne, ko kuma harkar kika bari…?

To gaskiya ba aure na yi ba, kuma ba barin harkar na yi ba, ina yi kadan-kadan ne, sai dai mutane ba za su gane ba, saboda ba sa gani na sosai, amma dai kafin na fara sai da na fada wa mahaifina, sai ya ce shi ma ga dokar da zai kafa mini, ya ce makaranta yake so in yi, kuma ya matsa sai da na yi, to da na ga na samu wannan sunan na daukaka, sai na koma makaranta. Hakan ya sa ake ganin kamar na bari ne, amma dai ina yin fim lokaci zuwa lokaci. Amma dai yanzu na gama na dawo.

A baya an fi ganin ki tare da Adam A. Zango, amma yanzu ba a ganin ku tare, me ya jawo hakan?

To ai da ma ba a kamfanin Adamu nake ba, kuma kamfanin Adamu fina-finan da suka yi mini ba su da yawa. Sai dai su ne suka yi mini fim din da ya fara daga ni. Don bayan albam din Mahmud Nagudu babu wani fim da ya daga ni sai na su Adamu. A gane furodusa ne yake hada ’yan wasa. Don haka idan suka ga dama su hada ni da Ali, in suka ga dama su hada ni da Adamu, ko Sani Danja da sauransu.

Yanzu a matsayinki na babbar jaruma, burinki ya cika a harkar fim?

Gaskiya burina ya cika sai godiya ga Allah. Yanzu burina daya ne kawai Allah Ya ba ni miji nagari.

Ku ’yan fim kullum ku ne fadar miji nagari kuke nema, amma ana yi muku kallon masu ruwan ido, ko me za ki ce kan hakan?

To, ai mu ba ruwan ido muke yi ba, muna tunanin maza suna ganin mu a fim ne, suna son su aure mu don wata manufa da suke da ita. Shi ya sa muke tsoron auren, ba wai muna tunanin wane mai kudi ba ne, ko marar kudi ba. Don idan ka auri mai kudi ma zai zaci don kudinsa ka aure shi. Gara ka auri talaka idan kudin ya zo kuna tare da shi. To yanzu abin ne sai ya zama muna tsoron mazan, su ma suna tsoron mu.

Ba kya ganin ana cewa idan kun yi auren ma ba kwa zama?

To ai wannan maganar da na yi ita ce ta ba da amsar wannan tambayarka. Nan za a gane Allah ne Ya san dalilin rabuwa tsakanin mata da miji, babu mamaki wancan dalilin zai sa a zo a yi auren wani bai yi tunanin wannan ba sai haka ta kasance.

Bayan harkar fim, ko akwai wata harka ta kasuwanci da kike yi?

E, ina yin kasuwanci. Don yanzu ina da wajen gyaran gashi a gidanmu. Sannan a makarantarmu ina yin aiki na wucin gadi, kuma ina saro kayan mata ina sayarwa.

Akwai wani lokaci da kika shirya na barin harkar fim?

Gaskiya ban shirya ba, sai lokacin da Allah Ya kawo mini miji to lokacin zan bar harkar fim.

Me kike alfahari da shi a game da harkar fim?

To abin da nake alfahari da shi na san ko ban yi komai ba akwai wadanda suka karu da ni a kan wani fim da na yi na gyara tarbiyya, sannan na san mutane masu yawa. Hakan abin alfahari ne, wanda ba kowa Allah Yake yi wa haka ba.
Sannan na samu abubuwa wadanda suke hakkokina ne nake ci ba na wasu ba. Sannan da fim na je Makka, na yi gida, na mallaki kadarori, na yi karatu, don haka dole na yi alfahari da harkar fim.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki 

Mungode

Source: Aminiya
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user