Sunday 3 June 2018

Karanta Yanzu Kaji Dalili: Shekara uku na mulkin Buhari a Nigeria 'ba yabo ba fallasa'

Tura Wannan Zuwa


A ranar 29 ga watan Mayun 2018 ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya cika shekaru uku akan mulki bayan rantsar da shi a 2015.

Shin farin jininsa ya ragu ko ya karu? yayin da wasu 'yan kasar ke bayyana shekaru uku na mulkinsa da cewa 'ba yabo ba fallasa'.

A cikin jawabinsa a ranar dimokuradiya da gwamnatinsa ke cika shekaru uku,

shugaban ya ce duk da sun fuskanci kalubale, amma gwamnatinsa ta samu nasarori a fannoni uku da ta sa gaba - wato tsaro da yaki da rashawa da kuma tattalin arziki.

Sannan Shugaban ya ce an samu ci gaba ta fuskar samar da hasken wutar lantarki, yana mai cewa "an rage amfani da janareto saboda wadatuwar lantarkin."

Sai dai 'yan Najeriya sun ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da cikar gwamnatinsa shekaru uku.

Mutane da dama ne suka bayyana ra'ayoyinsu tare da tafka muhawara a shafin Facebook na BBC Hausa game da shekaru uku na mulkin Buhari.

Wasu sun yabi gwamnatin, yayin da wasu kuma ke cewa har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba, musamman ga gwamnatin da aka zaba domin kawo sauyi a Najeriya.

Gwamnatin Buhari dai ta samu nasarar karya lagon kungiyar Boko Haram da ta addabi yankin arewa maso yammaci.
Amma wasu 'yan kasar na ganin yawan kashe-kashe da sace-sacen mutane da ake samu musamman a Zamfara da wasu jihohi wani koma-baya ne ga gwamnatin Buhari.
Tun kafin a zabe shi, shugaban ke nanata cewa tabarbarewar tsaro ne babban mihimmin abun da zai magance.

Amma baya ga karya lagon Boko Haram da gwamnatindsa ta yi, har yanzu ana ci gaba da kisan mutane a Zamfara da Kaduna da kuma wasu jihohin da ke fama da rikicin makiyaya da manoma.

Ko da yake a cikin jawabinsa, shugaban ya bayyana damuwa da yawaitar kashe-kashen, tare da yi wa 'yan kasa alkawalin cewa gwamnatinsa za ta kawo karshen matsalar.

Wani batu kuma da ke ciwa 'yan kasar tuwo a kwarya shi ne yadda rayuwa ta kara yin tsada a zamanin mulkin na Buhari.
Ko da yake shugaban ya karbi mulki a lokacin da farashin danyen mai ya fadi a kasuwar duniya.

Amma wasu na ganin kudaden da gwamnatinsa ta kwato da kuma kudaden ajiyar da aka samu sun isa ace talakawan kasar sun ga sauyi a gwamnatin.

Gwamnatin Buhari wadda ta yi karin farashin litar fetir daga Naira 97 zuwa Naira 145, ta ce tana kokarin farfado da tabarbarewar tattalin arzikin da ta gada ne daga gwamnatin da ta gabata.

A cikin jawabinsa, Shugaba Buhari ya ce an samu bunkasar tattalin arziki karkashin wani shirin gwamnatinsa na farfado da tattalin arzikin daga shekarar 2017 zuwa 2020.

Ya ce wani binciken da gwamnati ta gudanar a kwanan nan a fannoni uku na tattalin arziki, da suka hada da noma da sufuri da lantarki da Gas, ya yi hasashen za a samu yawaitar masu zuba jari tare da samar da ayyukan yi sama da 500,000 zuwa 2020.

Ya kara da cewa an dauki matasa aiki 200,000 a shirin N-Power, kuma tuni aka zabi 300,000 da za a sake dauka aiki.

Shugaban ya kuma ce asusun ajiyar Najeriya ya karu zuwa dala biliyan 47.5 a watan Mayu daga dala biliyan 29.6 a 2015.
Ya ce asusun bai-daya na TSA ya taimaka wa gwamnatinsa wajen adana biliyoyin daloli inda ya ce an ajiye dala biliyan 200 na daga ma'aikatan bogi da aka gano a ma'aikatun gwamnati.

A kwanakin baya ne dai, Shugaban na Najeriya ya bayyana aniyarsa ta sake neman wa'adin shugabanci na biyu a zabe mai zuwa.

Sai dai wasu masana na ganin akwai babban kalubale a gabansa ganin yadda wasu da dama ciki har da 'yan jam'iyarsa suka dawo daga rakiyar gwamnatinsa.

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com munayin aiki Tukuru don jin dadin ku Isar
da bayanai akan lokaci ba tareda son zuciya ba shine muradinmu

Ku hanzarta sanar da 'Yan Uwa da abokanan Arziki sunan Website din Mu me Albarka, don
ganin sabbin posting din Mu sai ku duba cikin website din akwai "Home" sai ku shiga,

mungode

Muryarhausa24.com Zata Kasance Babbar Kafar Yada Labarai aduk fadin Duniya domin Bunkasa Harshen Hausa, domin Zafafan Labarai ziyarci www.muryarhausa24.com

Labari iri daban-daban, farin cikin Ku shine Farin Cikin Mu Always Visit==http://www.muryarhausa24.com

Ku Cigaba da Kasancewa da Shafin Muryarhausa24.com aduk inda kuke a fadin Duniya farin cikin ku shine Farin cikin Mu

Munayin iyakar bakin kokarin mu don baiwa me hakkin rubutu hakkinsa, ma'ana idan mun samu Rubutu daga Suleman Abubakar to zamusa daga Suleman Abubakar saboda awajensa musami Rubutun koda bashi yayi ba to mu bamu Sani ba, adinga yimana Uziri

Burin shafin Muryarhausa24.com shine ta fito da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan masu jin yaren Hausa waje daya a ko ina suke

KARIN BAYANI

Zaku iya aiko mana da labari,Nishadi,Fadakarwa,Hausa Novel,Ra'ayi,Labarin Soyayya, Sharhi ko nuna gamsuwar Ku akan yadda muke tafiyar da wannan shafi
me Albarka aika sakon ka anan muryarhausa24@
gmail.com mungode

Allah ka daukaka harshe Hausa dama Kasa baki daya Amin

Source by ©BBC HAUSA
TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user