Saturday 11 August 2018

Hikayar Ali Baba Da Barayi Arba'in (4)

Tura Wannan Zuwa Ga
Bayan kwana biyu, barayi suka koma maboyarsu, ga tsananin mamakinsu sai suka tarar da an dauke gawar mutumin da suka kashe, bayan wannan kuma an sake dibar musu dukiya. Cikin fushi, bakinsa na kumfa, babban yan fashin ya ce, "Ina rantsuwa da abin da zai kashe ni, hankali na ba zai kwanta ba har sai na nemo wanda ya gane sirrinmu, yana zuwa yana dibar mana dukiya, ko wane ne shi, kuma ko a ina ya ke cikin duniyar nan. Idan kuwa na same shi zan gana masa azabar da ba a taba yi wa wani abu mai rai irinta ba, kafin na kashe shi!"


Ya ci gaba da cewa, "Ina so daya daga cikinku ya yi shiri irin na fatake, ya shiga cikin birni ya shako mana labari daga mutane, wata kila zai ji ana labarin wani mutum da aka kashe ta hanyar daddatsa jikinsa, ta haka za mu gane wanda ya zo nan ya dauke shi, kuma ya ke dibar mana dukiya."

Sai wani barawo daga cikinsu ya ce, "Ni zan tafi, kuma na yi alkawrin ba zan komo nan ba sai da cikakken labarin wannan mutum."

Babbansu ya ce, "Wannan aiki ne mai muhimmanci a wurinmu gaba daya, saboda haka idan har ka yi kuskuren da ka dawo nan ba tare da ka gano mana gidan wannan mutumin ba, to zan kashe ka."
Barawo ya ce ya yarda.
Ya yi shiri irin na matafiya, idan ka gan shi kamar wani mutumin kirki. Ya nufi birni. Ya iso cikin garin da sassafe. Da shigarsa cikin gari, sai ya hango wani mutum ya yi sammakon bude rumfarsa yana zaune a ciki. Da ya isa inda wannan mutumin ya ke, sai ya ga ashe dattijo ne, yana zaune yana dinkin takalmi. Ya yi mamakin wannan dattijo da yadda ya yi sammakon bude rumfarsa, bayan duk sauran rumfuna suna a rufe.

Barawo ya yi wa dattijo sallama. Bayan ya zauna sun gama gaisawa sai ya ce masa, "Baba, amma Allah ya hore maka kaifin ido, ta yaya kake iya gani cikin duhun safiyar nan har kake dinki, ga shi kuma ka tsufa?"
Dattijo ya ce, "Ga alama dai kai bako ne a wannan gari namu, idan ba haka ba waye bai sanni ba da kuma lakanin da ake yi mini na 'Baba Mustafa, dila mai idon zinari' ba. Tun ina dan shekara takwas na koyi wannan sana'a ta dinki daga mahaifina, kuma tun lokacin ita nake yi. Kai bari ma ka ji, saboda gwanancewata a dinki, har gawar mutum na taba hadawa na dinke ta wuri daya, bayan da barayi suka yi mata gunduwa-gunduwa, kuma a cikin daki mai duhu na yi wannan aiki."
Barawo ya bude baki cikin mamaki, ya ce a ransa, ga dukkan alamu na taki sa'a a kan wannan bincike da na fito yi, lalle ta hanyar dattijon nan zan sami abin da na fito nema. Ya dubi Baba Mustafa cikin mamaki ya ce, "Ka taba dinke gawar mutum fa ka ce? Kuma a cikin daki mai duhu? Wannan basira taka da yawa ta ke. Amma dai tun kana dan saurayinka ka yi wannan aiki ko?"
Baba Mustafa ya yi dariya ya ce, "Ba a yi kwana hudu da na yi wannan aiki ba. Wata rana ne, da sassafe kamar yanzu, wata yarinya.... Af! Na manta an rantsar da ni a kan cewa kada na yi wannan zance da kowa."
Da jin haka, sai barawo ya jawo jakarsa, ya bude ta sosai ta yadda Baba Mustafa zai iya ganin kudin da ke ciki. Ya lura da yadda Baba Mustafa ya yi ajiyar zuciya lokacin da ya ga kudin da ke makare a cikin jakar. Ya debo kudin ya ba shi, ya ce masa, "Karbi wannan ka fitar da kono a kan rantsuwar da ka yi, ina so ka fada mini wannan labari, kuma ka kai ni gidan da ka yi wannan aiki. Idan ka yi mini wannan, hakika zan biya ka da kudi mai yawan gaske."
Baba Mustafa ya ce, "Idan dai za ka biya ni ai sai na fada maka labarin duka." Barawo ya debo kudi mai yawa ya ba Baba Mustafa. Shi kuma ya fede masa biri har wutsiya.
Barawo ya ce, "Tashi mu je maza ka kai ni gidan, kafin mutane su fara fitowa zuwa wurin harkokinsu."

Baba Mustafa ya ce, "Ba ka ji labarin dai dai ba ne? Ai yarinyar rufe mini ido ta yi lokacin da za ta kai ni gidan, ba ta bude mini ido ba sai da muka shiga cikin dakin da gawar ta ke. Kuma ina gama aikin ta sake rufe mini ido, sai da muka zo nan sannan ta bude. Ba zan iya gane gidan ba, ko kalar fentinsa ban samu damar gani ba ballantana na ce zan iya shaida shi."
Barawo ya ce, "Ka yi amfani da hikimarka da basirarka mana, ni ma in rufe maka ido ka rika misalta hanyar da kuka bi a cikin zuciyarka har mu isa gidan. Ina tsammanin za ka iya yin wannan."
Baba Mustafa ya ce, "Kwarai kuwa zan iya, domin duk kwanar da muka bi zan iya kiyasta ta a cikin zuciyata. Kai bari ma ta wannan, har takun da muka yi kafin mu isa gidan da kuma bayan mun dawo na lissafe su kaf. Ba fa banza ake yi mini lakabi da dila ba yaro."

Suka tashi, barawo ya sami wani kyalle ya rufe idon Baba Mustafa. Suka shiga cikin gari. Bayan sun dan taba tafiya ta wani lokaci, sai suka iso gaban wani gida. Baba Mustafa ya tsaya, ya ce da barawon nan, "A dai dai nan ne na ji yarinyar nan ta bude kofar gida muka shiga daga ciki."
Barawo ya bude wa Baba Mustafa fuskarsa, ya ce, "Ka tabbata wannan gidan ne?" Baba Mustafa ya tabbatar masa da cewa ko shakka babu.

Barawo ya dubi gidan nan da kyau, da kalar fentinsa. Ga mamakinsa sai ya ga ai kusan duka gidajen unguwar kalar gininsu guda, kuma duk fentinsu kala guda ne. Sai lamarin ya daure masa kai, ya ga cewa idan ya koma ya fada wa 'yan uwansa ya gane gidan, idan suka zo cikin dare ba zai iya shaida gidan har ya nuna shi ba.

DUBA WANNAN: Hikayar Ali Baba Da Barayi Arba'in (5)

Don haka sai ya bude jakarsa ya dauko wani bakin fenti da yayi amfani da shi wajen canja kamannunsa, ya zana wata 'yar alama a jikin kofar gidan, yadda idan suka dawo cikin dare zai gane gidan. Ya sallami Baba Mustafa ya koma rumfarsa. Shi kuma ya juya zuwa cikin daji wurin 'yan uwansa domin ya shaida musu cewa bukata ta biya....


Za mu ci gaba....Ranar  Laraba Insha Allah

Ku ci gaba da Kasancewa da Mu domin samun ci gaban wannan ƙayataccen Labarin...

Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA ,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user