Monday 11 March 2019

Karanta Sabuwar Hanyar Samun Garaɓasar Shiga ko Ina a Yanar Gizo na Tsawon Wata 6 a Kyauta A Layin Airtel

Tura Wannan Zuwa Ga
Kamar Yadda Shafin Muryarhausa24.com.ng ya shahara wajen kawo muku hanyoyin samun kyaututtukan kira ko hawa yanar gizo cikin tsari mafi rahusa .


A yau wannan shafi na Muryar Hausa24 ta sake kawo muku sabon tsari na yadda zaku more kyautar shiga yanar gizo cikin sauki.

Idan masu karatu bazaku manta ba a kwanakin baya wannan shafi na Muryar Hausa24 ta kawo muku yadda zaku more garaɓasar 4GB a ₦1000 duk da cewa a wancan tsarin ba kowa bane yake shiga cikin jerin waɗanda kamfanin sadarwa na MTN suka zaɓa (A matsayin waɗanda su cancanci samun wannan garaɓasar) .

Kamfanin sadarwa a Nijeriya Airtel sun fitar da sabon tsarin more garaɓasar watanni shida cikin sauki.

Nasan wasu zasu tambayi Muryar Hausa24 ta ya ya zamu samu wannan garaɓasar?

Ga yadda zaku samu kyautar:

Na Ɗaya: Dafarko waɗanda suke da sabuwar wayar Android ƙirar kamfanin Infinix ko Tecno ko kuma wata sabuwar wayar Android , amma sunfi ba masu amfani da Infinix ko Techno.

Na Biyu: idan ku sayi Datar  ₦1,000 maimakon ku samu 1.5GB zasu baku 3GB kaga kenan kasamu kyautar 1.5GB.

Na Uku: ba Ina nufin idan ka sayi 1.5GB zaka samu 3GB  A'a idan ka sayi 10GB zaka samu 20GB (Iyakar kuɗin ka iyakar Shagalin ka) wannan shine a takaice.

Na Huɗu: kada ku manta zaku iya shiga ko ina da wannan datar kamar Facebook, Twitter, Whatsapp , Instagram, Youtube da sauran su kuma zaku iya sauke Audio/Video a duk shafin yanar gizo wanda kuke so.

Na Biyar: Zaku more wannan garaɓasar na tsawon watanni shida.

Nasan wasu zasu kuma tambayar Muryar Hausa24 , shin ta ya ya zan san ina cikin waɗanda zasu more wannan garaɓasar?

Hanya mafi sauƙi da zaku gane ko kuna cikin waɗanda zasu more wannan garaɓasa Shine :

Kawai ku shiga wajen aika saƙo (SMS) ku rubuta GET zuwa 141.

Ku jira na ɗan sakwanni zaku samu saƙo daga kamfanin sadarwa na Airtel wanda hakan shi zai baku damar more garaɓasar tsawon watanni shida.


Ku ci gaba da Kasancewa da Shafin MuryarHausa24.com.ng domin samun rahusa ta hawa yanar gizo ko kira a koda Yaushe.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com

Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.muryarhausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA GA

Mawallafi: verified_user