Saturday 1 December 2018

KARANTA KAJI: MU KOYI RUBUTUN HAUSA DA KA'IDOJINSA DARASI NA SHIDA

Tura Wannan Zuwa
Domin taimaka wa ɗalibai masu nazarin harshen hausa, da kuma masu so rubutunsu ya yi ma'ana da saukin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.


Darasi Na Shida


Mallaka

Mallaka, kalma ce ta wakilin suna da kan biyo bayan suna, wadda kuma ke nuna mallakar abin da ke da wannan suna. Mallaka iri biyu ce: Gajeriyar mallaka, da Doguwar mallaka.

Gajeriyar mallaka ita ce wadda yayin rubutu ake liƙa ta jikin kalmar abin da aka mallaka. Misali:

motarka ba motar ka ba

gonarsa ba gonar sa ba

aikinmu ba aikin mu ba

sana’arku ba sana’ar ku ba

matsalarsu ba matsalar su ba

Ita kuwa doguwar mallaka daban ake rubuta ta, ba a lika ta jikin kalmar abin da aka mallaka. Misali:

akuyar tawa

kayan nasu

lamarin naku, ds.

A lura:

Wakilan sunaye da ke nuna mallaka ne kaɗai ake liƙawa jikin kalmar abin da aka mallaka. Don haka ba za a liƙa su jikin sunan da ke nuna aiki ba. Misali:

ina jiran ka ba ina jiranka ba

ka tambaye ta ba ka tambayeta ba

yana ganin mu ba yana ganinmu ba

ta doke ni ba ta dokeni ba

an ɗaure su ba an ɗauresu ba

Za mu ci gaba  a sati mai zuwa Ranar Juma'a Insha Allah, Idan akwai mai tambaya a kan wannan darasi na yau sai a tura  tambaya zuwa
muryarhausa24@gmail.com mungode .

Wannan wani sabon darasi ne da
Waziri Aku tare da haɗin gwiwar Shafin Muryar Hausa24 su ka ɗauki nauyin kawowa 'yan uwa ɗalibai masu yin nazarin harshen Hausa da kuma masu son koyon ƙa'idojin rubutun harshen Hausa domin rubutunsu ya yi ma'ana da sauƙin karatu, ba tare da mai karatu ya canja wa rubutun nasu ma'ana ba.


KARANTA KAJI: MU KOYI RUBUTUN HAUSA DA KA'IDOJINSA DARASI NA BIYAR


A lura da haƙƙin mallaka wajen kwafin ɗin rubutu, darasin zai rika zuwa muku duk ranar Juma'a, daidai wannan lokaci, tare da taimakon Malam Nasir G. Ahmad.


Za mu ci gaba  a sati mai zuwa Ranar Juma'a Insha Allah, Idan akwai mai tambaya a kan wannan darasi na yau sai a tura  tambaya zuwa
muryarhausa24@gmail.com mungode .


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode


Source: www.MuryarHausa24.com.ng

TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user