Saturday 29 December 2018

KARANTA KAJI: TA RASU AWANNI KADAN SUKA RAGE MATA TA ZAMA AMARYA ALLAHU AKBAR!

Tura Wannan Zuwa
Sunanta Fauziyya Abdulkadir Tataru, ta kammala karatunta a Makarantar ATBU Bauchi, ta gamu da Ajalinta a yayinda da ake Shagulgulan daurin aurenta a jiya Juma'a da misalin karfe 9:30pm, yayinda kuma daurin auren nata ya kasance yau Asabar ne da misalin karfe 11:00am.
Tana farin cikin za ta dakin miji ashe kabari za ta. Hausawa sun ce ana bikin duniya ake kiyama, da yammacin Jiya juma'a ne aka yi walimar auren ta, kwatsam sai ga shi cikin daren jiyan Allah ya dauki ran ta.


Fauziyya Abdulkadir Tataru, yarinya ce wanda za'a daura Aurenta a yau 29/12/2018 da misalin karfe 11:00am na safe a masallacin Gwallaga dake Bauchi Da Angonta Abduljalil Salisu Boyi.


Yau da safe ne ranar daurin auren ta a masallacin Gwallaga dake jahar Bauchi, sai ga shi yau din ne za ayi jana'izar ta. Allahu akbar!

Awanni kadan suka rage ta zama Amarya, Allah ya karbi rayuwarta.


Wannan shine abinda Muhammad Kabeer Bauchi Ya wallafa a shafin sa"Sunanta Fauziyya Abdulkadir Tataru, ta kammala karatunta a Makarantar ATBU Bauchi, ta gamu da Ajalinta a yayinda da ake Shagulgulan daurin aurenta a jiya Juma'a da misalin karfe 9:30pm, yayinda kuma daurin aurennata ya kasance yau Asabar ne da misalin karfe 11:00am."

Ayayinda nayi kokarin jin ta bakin wassu daga Makusantar Marigayiya Fauziyyan cewa ko tayi fama da rashin lafiya ne? Sun tabbatar mun da cewa, lallai tana cikin koshin lafiyarta a yayin shirin Biki, sai dai sun tabbatar mun da cewa, tun kafin daurin auren akwai wani tsohon Samarinta dan Maiduguri Wanda ya ce mata 'Ayi auren mana ya gani' tabbas wannan kalma nasa ta tayar wa al'umma da hankali.


Wannan shine abinda Muhammad Kabeer Bauchi ya shaidawa wakilin mu.

Allah buwayi gagara misali, mahaliccin da ya fi Angonta kaunarta ya dauke abinsa.

Allahu akbar! Ita da kanta ta rubuta sanarwar daurin auren ta a shafinta.


Allah ya jikan wannan baiwar Allah ya gafarta mata, da rahama, ya mata makoma da madaukakiyar aljanna firdausi Amin Summa Amin.


Shafin komai da ruwanka, Muryarhausa24.com.ng munayin
aiki Tukuru don jin dadin ku

Isar da bayanai akan lokaci ba tareda son
zuciya ba shine muradin Mu

Burin shafin Muryarhausa24 shine ta fito
da kyawawan manufofi, tsari, Nagartar masu jin
yaren Hausa a dukkan fadin Nigeria da kasashen
da suke makwabtaka da ita kuma ta hada kan
masu jin yaren Hausa waje ɗaya a ko ina suke

Domin samun Labarai,Nishaɗi, Kalaman Soyayyar Hausawa,Bincike mai zurfi,,Tarihi,Fadakarawa,Tunatarwa, Addu'o"in littafin Hisnul Muslim (Garkuwar Musulmi) cikin harshen Hausa, Kimiya da Fasaha,Hotuna,Hausa Comedy, Sharhi mai gamsarwa, tsage gaskiya dalla-dalla da dai sauran su Ku ci gaba da kasancewa da Mu a www.muryarhausa24.com.ng a duk inda Ku Kasance a fadin Duniya

Mun kudiri aniyar tsage gaskiya
na bada labarai da suka hada da
harkokin yau da kullum Da zummar
samar da zaman lafiya da kuma
daukaka kima da martabar
al’adun Hausa.

DOMIN SAMUN LABARAI, RAHOTANNI, LABARIN BOLLYWOOD, LABARIN FINA-FINAN HAUSA NA KANNYWOOD, LABARIN WASANNI, HAUSA NOVELS, SABABBIN WAKOKIN SIYASA, TSOFAFFIN WAKOKIN HAUSA, ZAFAFAN KALAMAN SOYAYYAR ZAMANI, TSOFAFFIN WAKOKIN SIYASA, SABABBIN WAKOKIN HAUSA, FADAKARWA, TUNATARWA ADDU'O"IN LITTAFIN HISNUL MUSLIM (GARKUWAR MUSULMI) CIKIN HARSHEN HAUSA,NISHAƊANTARWA, LABARIN WASANNI, GARAƁASAR KIRA DA HAWA YANAR GIZO, ILIMANTARWA DA SAURAN SU AKAN LOKACI KU CI GABA DA KASANCEWA DA MU A www.muryarhausa24.com.ng

Zaku iya aiko mana da Labari ko shawarwari, Ra'ayoyin ku ko kuma nuna gamsuwar Ku akan yadda Mu ke tafiyar da wannan Shafi mai ALBARKA aika saƙon ka/ki akan addreshin Mu Na yanar gizo muryarhausa24@gmail.com  Za muyi farin ciki da samun saƙon ka/ki

Mungode

Source: www.MuryarHausa24.com.ng


TURA WANNAN ZUWA

Mawallafi: verified_user